Neehal Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 84 of 104
Sai wajen Azhar Mama ta dawo gidan, ita kaɗai ta dawo Daddy ya wuce gurin sabgoginsa. Kitchen ta faɗa ta ɗora girki, sannan ta barwa su Dije su ƙarasa dan ita Hospital zata tafi aiki, ta bar musu sallanun idan Neehal ta tashi su ce mata ta wuce office, a bakinsu take jin labarin zuwan su Afrah da mahaifinsu, ta ji daɗi itama sosai ta ce Insha Allahu zata dawo da wuri kafin su dawo daga gidan Mamy......
A gidan su Sadik kuwa yau tun safe Kawunsu ya zo gidan shi da Hajiyarsu (Kakar su Sadik) wadda kawun ya biya ya taho da ita. Maamah ta tarb'e su cikin mutuntawa da girmamawa. Umma kuwa yau ita ce da girki tana ɗakin Abba tana zuba masa kissa da kisisina, zuwan su Hajiyan yasa suka fito tare da Abban. Bayan an gama gaggaisa sun taɓa abun da Maamah ta kawo musu Kawu ya gyara zama ya dubi Abba ya ce. "Surajo Rukayya ta kira ni ta sanar da ni wani zance mara daɗin ji da ma'ana." Abba ya kalli Umma ya ce "Wanne zance kenan Yaya?" Kawu ya ce "Zancen yarinyar da Abubakar yake neman Aurenta mana." Hajiya ta tari numfashin Abba da faɗin "Au Sadik ɗin har ya fara neman Aure ba mu da labari?" Abba ya ce "A'a, soyayya dai kawai suke, tunda shi batun Aure dole sai an fahimci juna kafin akai ga maganar yin shi." Hajiya ta ce "Gaskiya ne, To Allah ya taimaka. Amma me ya faru da ita yarinyar?" Kawu ya kwashe duk abun da Umma ta sanar masa ya faɗa musu. Hajiya ta zaro ido tana jinjina kai ta ce "Kai! Gaskiya kuwa matuƙar haka ne da matsala, to ya rabu da ita mana ya nemi wata, ga ƴan mata nan burjik da yawa a gari sai ya zab'a ya darje." Maamah ta sunkuyar da kanta ƙasa cikin rashin jin daɗi, Umma kuwa murmushin farinciki ta saki a ɓoye." Abba ya ce "Ni fa Hajiya a gani na wannan duk ba matsala ba ce, yarinyar nan na yi binkice a kanta da iyayenta sosai mutanen kirki ne, mahaifinta ba b'oyayyen mutum ba ne, dan ya taɓa tsayawa takarar shugaban ƙasa, daga baya kuma ya daina siyasar kwata_kwata. Duk da dai ba shi ya haife ta ba, amma a matsayin mahaifi yake a gurinta tunda shi yake riqon ta." Maamah tay saurin d'ago kanta a karon farko ta ce "Au ba shi ɗin ne ya haife ta ba dagaske?" Abba ya ce "Ehh, amma itama yarinyar an tabbatar mun mahaifinta kafin ya rasu mutumin kirki ne, kuma ɗan asalin jihar nan ne a ƙaramar hukumar Gabasawa." Kawu ya ce "Wane ne marik'in nata?" Abba ya ce "General Alhaji Muhammad Tafida." Kawu ya jinjina kai ya ce "Tabbas na san sunan mutumin sananne ne, to amma mu yanzu ba nasabarta ce abun damuwar mu ba, damuwar mu batun kashe duk wanda ya ce zai aure ta da ake yi." Hajiya ta ce "Gaskiya fa, abun nan abun dubawa ne, dan watakila aljanu ne da ita suka aure ta." Umma ta ce "Nima abun da na gani kenan Hajiya, hankalina gaba-d'aya ya tashi har na kasa haquri na kira Yaya na sanar masa dan a yiwa tufkar hanci, tunda shi Abban nasu ya ƙi saurara ta." Abba ya ce "To, gaskiya ni dai duk a iya binciken da na yi ban ci karo da wannan labarin ba, kuma itama Rukayyan ban san a ina ta samo shi ba." Umma tay karaf ta ce "Ai ita marik'iyar yarinyar akwai ƙanwarta a nan unguwar, nan gaba kaɗan ne da mu babu nisa, to a gurin wata mak'ociyarta na ji wannan labarin, kuma babbar mace ce baza tay mun ƙarya ba." Abba ya ce "Ka ji fa, watak'ila ma ba gaskiya ba ne zuzutun abu ne irin naku na mata." Hajiya ta katse shi da faɗin, "Ba wani zuzutun mu na mata, maganar nan fa ya kamata a duba ta, kar mu zo mu yi abun da za'ai dana sani daga baya." Kawu ya ce "Ato, faɗa masa dai Hajiya." Abba ya ce "Shikenan, zan yi sabon bincike akan hakan Insha Allahu, idan ya tabbata haka ne sai ya haqura da ita ya nemi wata kawai." Daga haka suka rufe wannan chapter suka kama wata......
Sai da ƙarfe biyu na rana ta wuce sannan Neehal ta tashi daga baccin da take, shima ƙarar wayar Ahmad da ake ta kira ne ya farkar da ita. Tashi zaune ta yi tana kallon agogon bangon dake ɗakin, mamaki ne ya cika ta ganin ta yi fiye da awa uku tana baccin. Ta sauke numfashi a ranta tana tunanin may be a cikin magungunan data ke sha akwai na bacci, dan wannan baccin nata daga jiya zuwa yau ya yi yawa. Ta sauko daga kan gadon domin yin Sallah, wayar Ahmad ce ta ƙara yin ringing alamun shigowar kira. Kamar ta share sai kuma ta ɗauki wayar ta duba mai kiran, *Jamila* sunan da ta gani kenan akan ɗan screen ɗin wayar. Ta mayar ta ajiye sannan ta nufi toilet dan yin alwala. Bayan ta fito ta ji still ana kuma kiran wayar, bata bi takan ta ba dan dama dalilin da yasa ta kira shi ya dawo ya ɗauka kenan kar ayi ta kiransa a wayar ba'a same shi ba. Har ta yi Sallarta cikin nutsuwa ta idar ba'a daina kiran wayar ba. Ta yi ɗan tsaki ta tashi ta je ta ɗauki wayar, 17 missed calls ta gani kuma duk mutum ɗaya ce wato Jamila. Ta tab'e baki ta ajiye ta sauka ƙasa. Ƙwaƙwa da dabinon da Daddy ya siyo mata ta ɗauko a cikin fridge ta zauna ta fara ci bayan ta ɗibarwa su Dije. Bayan ta gama ci ta ɗebo abinci kaɗan ta ci. Koda ta koma ɗakinta dan yin sallar la'asar sai tarar wayar tana ringing, still a fili ta ce "Kai wannan mai kiran akwai naci, tunda ta kikkira ta ga ba'a ɗauka ba ai sai ta haqura." Ta d'aga wayar a kufelen da ita kanta bata san ko ta mecece ba ta ce "Mai wayar ba ya kusa." Bata jira amsa ba ta katse wayar. 5 missed calls ta gani bayan na d'azu, kuma duk dai mutum ɗaya ce, sai kuma 4 unreaad message data gani. Har zata ajiye wayar sai kuma ta shiga message ɗin ta gani, ɗaya na kamfani ne sauran ukun kuma duk na Hajiya Jamila ne. Ta shiga na farko ta ga abun da ta turo, _*Please Dear pick my call.*_ ta fita ta shiga na biyu ta ga shi kuma haka ta rubutu, _*Dama kiran ka nay in ji lafiyar ka, dafatan kana lafiya Habibi?*_ bata karanta na ukun ba ta ajiye wayar saboda takaici. Haka kawai ta ji ranta ya ɓaci ba tare data san dalili ba. Ta nufi kan darduma ta tada ik'amar Sallah dan tana da alwalarta.
Ƙarfe biyar da Æ´an mintuna Mama ta dawo, É—akin Neehal ta leqa ta tarar da ita zaune a kan gado tana latsa waya. Ta d'ago ta dubi Maman ta ce "Sannu da zuwa." Mama ta ce "Yawwa ya jikin?" A hankali ta ce "Da sauqi." Mama ta ce "Ashe su Afrah sun zo, har yanzu ba su dawo ba ne?" Ta gyaÉ—a mata kai kawai. Mama ta juya ta fice ganin kamar bata son magana, ita kuwa ranta ne a É“ace har lokacin, sai taune lip É—inta take. Kafin Magriba Ahmad ya dawo da su Afrah, da gudu suka je suka rungume Mama dake zaune a falon Æ™asa. Mama ta shafa kanwunansu tana murmushi ta ce "Welcome yarana." Ahmad ya zauna a kan carpet ya gaishe da Mama cikin girmamawa. Ta amsa masa tare da tambayarsa yanda ya baro Mamy da su Ummi. Su Amrah suka bar jikin Mama suka nufi upstairs dan sun san Auntin nasu tana can. Tana nan yanda Mama ta bar ta suka shigo É—akin suna kiran sunanta. Ta d'ago ta kalle su bata ce komai ba, suka hawo kan gadon da murnar su, Afrah ta ce "Aunty mun dawo, Mamy ta ce mu gaishe ki." Ta yi É—an murmushi ta ce "Sannun ku da dawowa, to ina amsawa." Amrah ta ce "Daddy yana Æ™asa shi da Mama." Ta yi shiru bata ce komai ba, yaran suka cigaba da yi mata hira. Kiran Ahmad ne ya shigo wayarta, ta É“ata rai kamar yana gabanta ta Æ™i d'agawa, haka kawai ta ji tana jin haushin shi ba tare da ta san dalili ba. Bayan kiran ya katse wani ya Æ™ara shigowa, still Æ™in É—agawa ta yi. After three minutes Mama ta turo Æ™ofar É—akin ta ce mata ta je Ahmad yana jiran ta. Fuska a cukule ta É—auki wayarsa dake kan bedside locker ta fice daga É—akin, su Afrah suka mara mata baya........âœï¸
[7/21, 9:32 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.