Complete Hausa Novels

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 19 of 104

2 days later

Su Dad sun kai kuɗin Auren Ameen gidansu Hafsat, inda a ka tsaida ranar biki wata huɗu masu zuwa. Maganganu sun yi ta yawo a cikin Family'n su Dad sosai, wasu na faɗin Ameen ya yaudari Hameedah, wasu kuma na faɗin Ameen kuɗin mahaifin Hafsat ya bi zai aure ta, wasu kuma suna faɗin ai gwara ma da ba Hameedah zai aura ba, dan sam ba su dace ba. Mommy'n Hameedah kuwa kamar za ta yi hauka, duk da an kai kuɗin amma ƙara kwantarwa da Hameedah hankali take da faɗin indai ta na raye Ameen ba shi da mata sai ita. Su Neehal da Haneefah da sauran cousins d'in Neehal murna suke sosai da baikon Yayan nasu. Next week su Neehal za su yi resuming school, ta na cikin d'akinta ta na guge hijabs ɗinta Mama ta shigo d'akin. "Neehal yau fa Muna da baƙi a gidan nan." Neehal ta ce "Suwa kenan Mama?" Mama ta ce "Ameen ya ce Hafsat za ta zo ta gaishe ni, ki bar gugar nan ki taso mu ki musu ɗan abun taɓawa." Neehal cikin murna ta ce "Yanzu kuwa Mama, ashe yau mu na da manyan baƙi." Mama ta ce "Ki dai yi sauri kar time ya k'ure." Sosai Neehal ta zage jikinta ta shiryawa su Hafsat kayan ciye_ciye kala_kala ita da su Dije da suka taya ta. Bayan sun gama aikin ta na nunawa Mama abubuwan da suka yi Mama ta ce. "Um lallai Neehal, da ni na saki wannan aikin na san har kuka sai kin mun, amma da yake budurwa Ameen ce za ta zo ko nuna alamun gajiya ba ki yi ba." Neehal ta yi murmushi kawai. Mama ta ce "Ki je ki yi wanka kafin su ƙaraso, su Dije za su jera musu abincin a dinning." Neehal ta ce "Toh."

Hafsat 'Ya mace ɗaya tilo a gurin mahaifinta wanda ya kasance hamshaqin mai kuɗi, Hafsat ta so Ameen kamar ba gobe, amma Ameen ya nuna sam ba ya ra'ayinta. A wancan lokacin haka za ta yi ta zarya gidan Mama tun suna Abuja ta na gaishe ta, daga baya ne da ta ga Ameen ɗin dai ba ya k'aunar ta sai ta hak'ura ta k'yale shi amma ba don ta dena k'aunar shi ba. Cikin wata rantsatstsiyar Mota suka ƙaraso gidan, driver'nta a gaba ya na driving ɗinsu sai ita da k'awarta mai suna Fadeela a bayan Motar. Bayan ya yi parking Motar ya fito da sauri ya buɗe mata mota, cikin izzarta ta fito ta na kallon harabar gurin. Duk da kasancewar mahaifinta ya fi Dad kuɗi amma babu abun da gidansu zai nunawa gidansu Ameen a kyau da tsaruwa, sai dai ya fishi girma. Cikin takunta ɗai_ɗai ta fara tafiya k'awarta na bin bayanta. D'aya daga cikin ma'aikatan gidan ne ya musu jagora zuwa part ɗin Mama. Hafsat sosai take farin ciki da zuwanta gidansu Ameen ɗin, domin wannan zuwan ta zo ne a matsayin suruka ba kamar baya ba da take zuwa dan neman samun guri ba. Fadeelah ta dube ta tace "Hafsy na lura yau wani farin ciki ki ke na musamman kamar yau ne ranar auran naku." Hafsat ta faɗaɗa fara'ar fuskarta ta ce "Hmmm Fadeelah kenan, wannan zuwan fa da na yi gidansu Ameen a matsayin suruka na zo, saɓanin da da nake zuwa da k'ok'on bara ta." Fadeelah ta ce "Gaskiya ki na son Ameen da yawa."Hafsat ta ce "Faɗar irin son da na kewa Ameen ma ɓata baki ne saboda tarin yawansa a cikin zuciyata." Fadeelah ta ce "Amma me yasa be bari sai ya dawo daga Lagos ki zo yana nan ba?" Hafsat ta ce "Ni na matsu sai na zo na gaida Mum ɗinsa, shi ma da yaso na bari sai ya dawo na ce ni dai sai na zo......." Buɗe k'ofar da Zulai ta yi ya katse mata maganar da take. Zulai ta ce "Sannunku da zuwa, ku shigo." Fadeelah ce kawai ta amsa da "Yawwa" amma ita Hafsah ɗan yatsina fuska ta yi ta wuce ciki. Gurin zama Zulai ta nuna musu sannan ta haura sama domin ta sanarwa da Mama zuwansu. Hafsat ta dinga satar kallon falon dan ba ƙaramin kyau da burge ta ya yi ba, ga wani sassanyan k'amshi da yake tashi a cikin sa. Neehal Mama ta turo ta hawo da su sama. Neehal da murnarta ta taho dan tarar Aunty'n tata. Tun da ta fara sakkowa Hafsat ta ƙura mata ido cikin fad'uwar gaba, domin ta gane ita ce Neehal ɗin da kullum sai Ameen ya yi zancen ta, dama ta santa a ASTV amma sai ta ga kamar a TV'n ma rage mata kyau a ke a fili ta fi kyau. Haɗe rai ta yi sosai tare da ɗauke kanta daga kallon Neehal  ganin ta ƙaraso cikin falon. Da fara'a sosai Neehal ta ce "You are highly Welcome Dear, sai dai ban san wacce ce Aunty'n tawa ba da nake ta ɗokin zuwan ta ba" Fadeelah ta yi murmushi dan ita kam yanda Neehal ta musu ta burget a, nuna Hafsat ta yi ta ce "Gata nan, tunda kin kasa hak'uri na gabatar miki da ita." Neehal ta yi murmushi ta na kallon Hafsat ta ce "Masha Allah, gaskiya Yayanah ya iya zaɓe." Ta ƙarashe zancen tare da ƙoƙarin rungume Hafsat ba tare da ta damu da ɗauke kan da ta mata ba. Wani kallon wulak'anci Hafsat ta jefa mata tana yatsina fuska kamar ta ga kashi..............✍️
[7/21, 9:00 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*

_By_
_Zeey Kumurya_

*1️⃣4️⃣*

Duk da Neehal ta ga irin kallon da Hafsat ta mata amma ta danne zuciyarta ta rungume ta, sai dai jikinta ya yi sanyi ba kaɗan ba. Kamar yadda ta rungume Hafsat haka ta rungume Fadeelah. Fadeelah da ba ta ji daɗin abun da Hafsat ta yi ba ta yi murmushin ƙarfin hali ta ce "Ai na yi fushi, tunda Aunty'nki kawai ki ka sani ita ki ka fara tarb'a." Neehal ta yi murmushin yaƙe ta ce "Sorry ai kema Auntyna ce." Fadeelah ta yi murmushi dan sosai ta ji ta na son Neehal, yarinyar ta burgeta daga gani ba ta da d'abi'ar wulak'anta mutane duk da kasancewar ta celebrity. Neehal ta ce "Mama ta na sama mu ƙarasa." Fadeelah ce kawai ta amsa mata suka mik'e suka bi bayanta, Hafsat sai hararar bayan Neehal take. Neehal ta shiga d'akin Mama ta sanar mata da isowarsu sannan ta fito ta wuce ɗakinta. Kafin Mama ta fito Fadeelah ta ce wa Hafsat "Haba Hafsah, gaskiya ban ji daɗin abun da ki ka yi wa yarinyar nan ba ko kaɗan wlh." Hafsat ta mata wani kallo ta ce "Yarinyar ba ta mun ba ne shi ya sa." Fadeelah ta ce "Hmmmmm, me yarinyar nan ta yi da za ki ce ba ta miki ba? Yarinya ta taho da murnarta da ɗokin ganin ki ka amma ki mata wannan wulak'ancin, gaskiya ban ji dad'i ba." Hafsat ta tab'e baki ba ta ce komai ba, domin ita kaɗai ta san baƙin cikin dake cin ranta na ganin Neehal, ashe duk kyawunta da mutane suke faɗa na ganin da suke mata a TV a fili tafi haka, yarinya ga dirin jiki kamar ita ta yi kanta, tafiyar ta ma kaɗai abun kallo ce ga zazzak'ar murya.... Fitowar Mama ya katse mata tunanin da take. Cikin girmamawa suka ɗan zamo daga kan kujerar da suke suna amsa sallamar da Mama ta musu. Mama ta zauna ta na faɗin "Sannun ku da zuwa." Suka amsa da yawwa tare da gaisheta, Mama ta amsa musu cikin fara'a ta ƙara da faɗin. Ya mutanen gida.?" "Suna lafiya, suna gaishe ku." Cewar Fadeelah. Mama ta ce "Masha Allah, muna amsawa." Hafsat dai kanta na ƙasa ta na satar kallon Mama, domin Maman kamar ba ta tsufa, a 'yan shekarun da ta yi ba ta ganta ba sai ta ga ta ƙara kyau da gayu, ba za ka taɓa cewa ta haifi Ameen ba. Mama ta mik'e ta na faɗin "Bismillah ku ƙarasa dinning ku ci abinci, bari na kira Neehal ta yi serving ɗinku."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.