Neehal Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 31 of 104
Hameedah ce zaune ta ɗora kanta akan cinyar mahaifiyarta tana kuka ƙasa_ƙasa, ganin tabbas ta rasa Ameen tunda gobe zai angonce da wata. Mumy wadda ta gaji da rarrashi tun a gurin bikin ta ce "Wai Hameedah meke damunki ne? so kike har sai mutane sun fuskanci halin da kike ciki, masu dariya su yi miki suna Allah ya ƙara, na ce miki daure zuciyarki za ki yi ki nuna kamar baki damu ba, a yi bikin nan a gama." Hameedah ta d'ago kanta cikin sheshshek'a ta ce "Mumy na yi iya yina nayi ƙoƙarin hakan amma na kasa, wallahi Mumy ba ki ji yanda nake ji a cikin zuciyata ba kamar ana rura mun garwashin wuta." Mumy ta ce "Na san abun da ciwo, kuma nima ina jin yanda kike ji, amma ki daure dai, na faɗa miki ko mai daren daɗe wa sai kin auri Ameen in dai da bokaye a cikin duniyar nan, yanzu dai ki share hawayenki in faɗa miki wani abu kin ji My daughter." Hameedah ta gayd'a mata kai ta fara share hawayen nata.
Misalin ƙarfe 12:30 na dare Ameen ne zaune a falon Daddy shi da Mama da ta kira shi, ya tattara duka hankalinsa yana sauraren abun da zata faɗa masa. Mama ta ce "Dama d'azu kai ka tsayar da Neehal?" Ya ce "Eh." Mama ta ce "Akan wanne dalili?" Ya yi shiru, Mama ta ce "Ka yi shiru ina maka mgn." Ya ce "Babu komai Mama." Mama ta girgiza kai ta ce "To me ne dalilin da yasa ka bata kayan data saka? bayan ga wanda suka ɗinka za su saka ita ƴan'uwanta." Ameen ya ce "Mama wai dama wannan shine kiran da kika mun? wallahi na ɗauka wani babban abunne ya faru." Mama ta harare shi ta ce "Ban sani ba." Shigowar Neehal falon ya hana Ameen faɗar abun da zai faɗa. "Ke kuma daga ina?" Mama ta tambayi Neehal tana kallonta, Neehal ta turo baki gaba ta ce "Bacci zan yi a nan saboda ina son na kwana tare da yaran." Mama ta nuna mata dakin da suke da hannu tana faɗin "Suna nan, zaki wani kwaso jiki a daren nan ki taho kamar da tare da su kike kwana." Neehal ba ta ce komai ba ta shige, Ameen da ya bita da kallo har ta shige dakin sannan ya dubi Mama ya ce "Wanne Yara ne kuke magana akansu." Mama kamar ta share ta ƙi faɗa masa sai kuma dai ta sanar masa, don abokin kuka shi ake fadawa mutuwa. Shima ya girgiza da lamarin, amma dai ya ce wa Mama da safe sai akai yaran gidan Radios da Televisions a bada cikiyarsu ko za a dace a samu iyayensu. Mama ta yi na'am da shawarar shi. Neehal ta daɗe kafin bacci ya ɗauke ta, tana ta aikin kallon yaran, tana jin ƙaunar su na mamaye mata zuciya.
Washegari da safe Neehal tana tattare É—aki Yarinya É—aya ta tashi tana kiran sunan Daddy, Neehal ta ajiye tsintsiyar hannunta ta Æ™arasa gadon ta d'ago ta tana faÉ—in "Kin tashi, mu je ki yi fitsari to." Yarinyar dake bin ta da kallo ta gyaÉ—a mata kai. Bayan ta yi fitsarin Neehal ta wanke mata baki da fuska suka fito, suna fitowa ta ga itama É—ayar ta tashi zaune tana ta mutsitsika ido, Neehal ta kama ta itama ta kaita toilet, Bayan sun fito ta kalle su ta ce "What is your name?" Wadda tafi surutu ta ce "Afrah, amma Daddy yana ce mun Princess, a lesson da islamiyya kuma *FATIMA AHMAD*." Neehal ta jinjina kai ta ce "Nice name Darling." Sannan ta juya ta kalli ÆŠayar ta ce "Ke fa." Yarinyar ta ce "Amrah, amma Daddy yana ce mun Jewel a lesson da islamiyya kuma *AISHA AHMAD*." Neehal ta Jinjina kai tana murmushi ta ce "Nice name sweetheart." Afrah ta ce "Aunty safiyar ta yi zaki kai mu gurin Daddy ko?" Neehal ta gyaÉ—a mata kai zuciyarta cike da k'aunar yaran. Mama ce ta shigo É—akin hannunta É—auke da tea flaks da Æ™ananun cups, yaran suka bita da kallo kafin su haÉ—a baki a tare su ce "Ina kwana." Mama ta ajiye kayan hannunta tare da amsa musu, ta Æ™araso ta shafa kansu da cike da kaunarsu, dan yaran sun matuÆ™ar burge ta ba kaÉ—an ba, musamman da suka gaishe ta, ga dukkan alamu daga gidan tarbiyya suke. Mama ta dubi Neehal ta ce "ÆŠauko musu kayansu a saka musu, bari na haÉ—a musu breakfast su yi." Neehal ta amsa mata tare da ficewa daga É—akin, yaran suka bita da kallo kamar za su bita. Bayan sun yi breakfast Neehal ta musu wanka ta shirya su cikin rigunansu na jiya. Kasancewar yau ne d'aurin Aure yasa gidan ya Æ™ara cika da baÆ™i mata da maza, duk inda Neehal ta É—ora k'afarta su Afrah na biye da ita a baya, duk wanda ya tambaye ta yaran waye sai ta ce na wata Friend É—inta ne. ÆŠaya daga cikin sojojin gidan ta bawa kuÉ—i ya siyo wa musu kayan sakawa da takalma da panties, kafin Azhar ya kawo mata ta shirya su tsaf suka yi kyau sosai. kowa so yake ya É—auke su ko ya musu hoto, amma yaran sun Æ™i yarda da kowa sai Neehal, saboda ganin taron jama'a, ita kuwa ta cika su da kayan zaÆ™i dangin su chocolate da sweet suna ta sha. Mama kanta ya É—au caji tana da hidima da mutane, hakan ya sa ba ta bi takan zancen yaran ba, dama kuma da taywa Daddy maganar su ya ce a bari bayan biki sai a san abun yi. Ƙarfe biyu na rana aka É—aura Auren AL'AMIN MUHAMMAD TAFIDA da amaryarsa HAFSAT AHMAD ÆŠAN GASKE. Anan babban masallacin Juma'a dake cikin Narasawa G.R.A. Yau ma Neehal ta yi kyau sosai, shadda ta saka da safe Wadda aka mata akai mai kyawun gaske, ta kafa É—aurinta. Su Afrah sai faÉ—in "Kin yi kyau Aunty." suke, Murmushi Neehal take idan suka faÉ—i haka. Ta ce musu "Thank you Dear." Wajen Æ™arfe uku Sadik ya Æ™araso gidan. Neehal ta fito tare da twins É—inta, tunda ta fito ya Æ™ura mata ganin irin kyawun da ta yi. Neehal ta gaishe shi ya amsa yana kallon yaran, Neehal ta ce "Ya su Maamah da Abba?" Sadik ya ce "Suna Lafiya, Ya taro?" Neehal ta ce "Alhamdulillah." Ya ce "Allah ya sanya Alkhairi ya ba su zaman lafiya, saura naki kuma." Neehal ta yi murmushi ta ce "Yau har na gaji da jin wannan furucin, kowa muka haÉ—u sai ya ce sai mun zo naki kuma." Sadik ya ce "To ai gaskiya ne, gwara Mama ta aurar dake ta huta da rigimarki." Neehal ta ce "hmmm." Kawai, Sadik yace "Wannan cute babies É—in fa?" Neehal ta ce "Yaran wata Friend É—ina ne." Sadik ya ce "Masha Allah, Allah ya raya su." Neehal ta ce "Ameen." Tare da dubansu ta ce "Ba ku gaida Uncle ba." Amrah ce ta fara gaishe shi da faÉ—in "Ina kwana." Sannan itama Afrah ta gaishe shi, ya kama hannunsu tare da amsa musu. Bai wani jima ba ya tafi saboda Ameerah data zo kiran Neehal. Suna tafiya Ameerah ta ce "Amma Yaa Neehal wannan saurayinki ne?" Neehal ta girgiza kai tare da faÉ—in "Ko É—aya, he is just my Friend." Ameerah ta yi shiru amma ba dan ta yarda ba. Ƙarfe huÉ—u aka tafi gurin da za ai Mother's Day, sai bayan magriba aka tashi. Yau kam amarya ba ta zo ba, tana gida suna nasu suma, shima Ameen É—in bai je ba, hakan yasa yau kwata_kwata ba su haÉ—u da Neehal ba. Twins kam ganin hada_hadar mutane yasa ba su Æ™ara takurawa Neehal akan ta kai su gurin Daddy'nsu ba, sai da suka zo bacci nema suka so yi mata rigima ta lallaÉ“awa su da faÉ—in sai an gama biki zata kai su. Washegari ma anyi taro a gida inda akai kidan Æ™warya manyan mata suka cashe, tun kafin Azhar aka fara har bayan la'asar ana yi. Yau za a miÆ™a Amarya gidan angonta, misalin Æ™arfe biyar na yamma Neehal dake jin duk jikinta a sanyaye ba tare da tasan dalili ba ta bar wa Haneefah twins ta nufi part É—in Ameen............âœï¸
[7/21, 9:01 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.