Neehal Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 39 of 104
Cikin tsananin takaici ya d'ago yana jifan ta da wani irin kallo, ita ma kallon nashi take da kyawawan idanunta cikin shock ta turo small pink lips ɗinta gaba. Tsaki ya ja tare da ɗauke idonsa daga kanta, ajiye abincin hannunta ta yi a ƙasa ta kai hannunta jikinsa inda abincin ya zuba tana faɗin "Sorry Yayanah bari na goge maka." Shi dai be ce mata komai ba sai harara da yake ta banka mata, maimakon ta goge masa kamar yadda ta ce sai ma ƙara damula masa miyar take a inda babu, cikin k'ufula ya buge hannun nata tare da jan wani wawan tsaki ya tashi fuuu ya nufi ɗakin da Aunty A'isha ta sauke shi, shi fa shiyasa tun farko bai so Mama ta yo wannan tafiyar da shi ba, sai da ya ce mata ba zai biyo ta ba amma ta takura masa sai ya zo, gashi nan daga zuwan shi wata tsaregar yarinya ta fara ɓata masa rai. K'wafa ya yi lokacin da yake cire rigar jikinsa, ba dan ya kai zuciyarsa nesa ba da sai ya gaggaura wa yarinyar maruka, dan ta gane shi ba sa'an wasanta ba ne. Neehal kuwa ɗakin Aunty ta yi da gudu tana kuka, Mama kuwa tana ganin Neehal ta shigo da kuka ko da ba a faɗa mata ba tasan ita da Ameen ne, dan tasan halin kayanta sarai. Tashi ta yi ta fito falo, Aunty A'isha kuwa rarrashin Neehal ta shiga yi. Ba ta ganshi a falon ba hakan yasa ta bi shi har ɗakin da yake, ta tura ƙofar ta shiga da Sallama, trolley ɗinsa da ya ɗauko riga a ciki ya saka yake zipping, ya amsa mata sallamar cikin muskilar muryarsa. Mama fuska ɗaure ta ce "Ameen! Me yarinyar mutane ta maka kake dukanta? dan na saka ka zo sai ka huce a kanta?" Kamar ba zai yi magana ba sai kuma dai ya ce "Mum ni ban dake ta ba, kawai ta zo tana samun ciwon kai ne shine na ɗan maketa." Mama ta ce "Uhm lallai, ai gwara daka ɗan maketan, to tunda ka make ta kuwa kai zaka zo rarrashe ta." Tana gama faɗin haka ta juya ta fice, cize lips d'insa na ƙasa ya yi, ya tashi ya fito falo. Da Mama ta koma ɗaki ta tarar Neehal ta yi shiru tana bawa Aunty A'isha labarin dalilin kukanta. Aunty A'isha ta ce "To ki yi haquri kin ji, kuma ai ke kika ɓata masa kaya dole ya dake ki, ki je ki bashi haquri ki ce masa ba za ki kuma ba kin yi yarinyar kirki tah." Neehal ta gyaɗa mata kai ta fice daga ɗakin da saurinta. Aunty A'isha ta yi murmushi ta ce "Neehal rashin ji Ameen kuma babu haquri." Mama ta ce "Dama da abunsa, har yanzu fushi yake na taho da shi, na rasa irin wannan muskilanci na Ameen da baya son shiga cikin mutane, ya fi son in barshi a gida yay ta fama da system da takarda, kamar a kansa aka fara study." Aunty A'isha ta ce "Ameen halinsa sai shi kam." Neehal tana fita ta ɗan nutsu saboda tsoron Ameen da ya dirar mata a zuciya. A hankali ta ƙaraso kusa da shi cikin sanyi ta ce "Yayanah ka yi haquri ba zan kuma ba." Ameen ya sauke numfashi ya kamo hannunta ya ce "Shikenan na haqura, amma ki daina rashin ji da yiwa mutane ihu kin ji." Neehal ta gyaɗa masa kai, cikin murnar ya ce ya haqura ta ce "Yayanah za ka kai ni islamiyya gobe? Nima ince wa su Noor ga Yayanah." Ameen ya ɗan murmusa tare da gyaɗa mata kai. Ganin fa ya sake mata sai ta shiga yi masa hira tana bashi labarai kala_kala, shi dai kallon ɗan ƙaramin lips ɗinta da kyawawan idanunta kawai yake, a zuciyarsa yana mamakin surutu irin na Neehal sai ka ce Radio, ko ya ta motsa bakinta sai dimples ɗinta sun lotsa abun sha'awa. Kiran Sallar Magriba ne ya tada shi, tare suka fita da ita bayan ya yi alwala ita kuma ta yi part ɗin Ummanta. Washegari da safe Mama ta je part ɗin Umma suna hira, kamar ko wacce Sunday Aunty A'isha ta kamo Neehal ta fara yi mata kitso duk da zillewar da tai ta yi, saboda a rayuwarta ba ta k'aunar a taɓa mata kai ko kaɗan, kitso kuka, tsifa kuka, wankin kai kuka, haka Allah ya yi ta. Yauma gaba-d'aya ta cika part ɗin Aunty A'isha da ihun kukan kitson, Ameen yana daga ɗaki a kwance amma yana jiyo ihun nata, dan ware murya ta yi iya ƙarfinta, kamar wadda ake yankar naman jikinta. Da abun da ya ishe sa ne ya fito a fusace ya daka mata tsawa, ba shiri ta yi tsit sai tsiyayar hawaye kawai take, daga baya kuma sai bacci ma ya ɗauke ta. Haka rayuwa tay ta tafiya, Neehal tana girma kyawunta na ƙara fitowa, gata ƴar gatan Abbanta babu abunda ya rage ta da shi, Haka ma mahaifiyarta da Aunty'nta. Tana zuwa Gabasawa sosai musamman lokacin hutu, haka ma tana zuwa Abuja gidan Mama, amma tun daga time ɗin da Ameen suka zo gidansu ba ta ƙara ganin shi ba, saboda ya tafi Turkey karatu. Tun tana tambayar Mama shi har ta manta da shi ma. Neehal yarinya ce mai ƙoƙari ga iyayi da son gayu, hakan yasa take da farin jini a ko'ina, duk inda ta shiga sai an k'aunace ta.
Tana da shekara takwas kakarta Inna mahaifiyar Umma ta rasu, mutuwar Inna ta girgiza mutane da yawa, Umma ta yi kuka ita da su Uncle Umar, Neehal ma duk yarinya ce a time ɗin Amma ta ci kuka ta gode Allah. Shekarta goma sha biyu ta zana commen entrance, a lokacin ne ta samu hutun makaranta mai tsayi kusan na 3 months, Gabasawa ta fara zuwa ta yi 1 week daga nan ta dawo gida ta je gidan Baffa ƙofar Nasarawa ta musu kwana uku, daga nan ta je gidan Uncle Umar ta yi kwana biyu, dan duk da Uncle Umar yana da ƴaƴa guda biyu amma Neehal ba ta jin daɗin zaman gidan saboda matarsa ba ta da kirki, shi ma Uncle Umar ɗin kuma dama ba ya wani sakar mata fuska, hakan yasa babu wata shak'uwa mai ƙarfi a tsakaninsu, sai masifar tsoransa ma da take ji. Daga nan Gombe ta wuce gidan Hajiya (Mahaifiyar su Aunty A'isha), time ɗin ba'ayi auren Aunty Sadiya ba, kuma ga Ameerah ƴar gidan Uncle Mahmud suna wasa tare, shi ya sa take jin daɗin zaman Gombe. Satinta ɗaya a can ta wuce inda tafi jin daɗin zamansa akan ko'ina wato Abuja gidan Mama. Daga cewa za ta yi 2 weeks sai gashi tar tafi wata ba ta dawo ba, su Abba da Umma da Aunty sun yi kewarta, kullum suna waya a wayar Mama, idan suka tambaye ta yaushe zata dawo sai ta ce musu ta kusa amma kuma ta ƙi dawowar. Ameen ya dawo Naija time ɗin, amma ba ya Abuja yana Lagos acan ya fara aiki, zuwa time ɗin ya zama cikakken saurayi mai cikar zati da kwarjini, miskilanci kuwa da tsare gida sai abun da ya yi gaba. Neehal tana jin daɗin zama a Abuja sosai, saboda yanda Mama da Daddy suke tarairayarta tare da nuna mata tsantsar k'auna tamkar su suka haife ta. Ita kam babu abun da za ta ce da dangin Aunty A'isha sai godiya da sam barka, ƴan'uwan kishiyar babarta ne amma har sun fi wasu ƴan'uwan Abbanta kula da ita, dan idan ta je Gabasawa a yanzu da babu ran Kakarta Yayar mahaifinta wadda take kira da Ummi ita kaɗai take kula da ita, sauran cousins ɗin Abbanta kuwa tsakaninta da su gaisuwa ce kawai, amma idan zata shekara a garin babu mai aiko mata da abun biyar, amma su komai na su sa kwashi jiki su tafi gurin Abbanta ya biya musu buƙatar su. Gwara ƴan'uwan Umma su ko ba su bata komai ba, amma akwai sakin fuska kuma suna janta a jiki. Ƴaƴan Baffa kuma wanda ya rik'i Ummanta da Abbanta suma dai ba wani jin daɗin su take ba, Ƴaƴansa duka maza ne guda huɗu, duk sun yi aure sun hayayyafa, wasu ma sun haifi wanda suka girme ta, Baffan ne dai ya nuna mata k'auna da ya raye, ba ya banbanta ta da sauran jikokinsa. (Da yake tun Neehal tana shekara goma Allah ya yi masa rasuwa.) Akwai wani cousin ɗin Abba da yake nan Kano Yaya ne a gurin Abban, mutumin yana da kirki ga ilimin Addini, kaf cousin ɗin Abba ya fi zumunci da Abba sosai, dan tamkar uwa ɗaya uba ɗaya haka suka ɗauki junansu. Mutumin yana son Neehal sosai, dan Abba yana yawan kai masa ita, to shi kuma matsalar matarsa ce makira kuma muguwa, zata nuna babu ya kai a zahiri, amma a cikin zuciyarta ba haka ba ne, da wani abu na sharri zai same ka sai ta fi kowa murna. Duk da haka dai suna Zumunci sosai da Umma da Aunty A'isha. Dangin Abba haushin yanda Neehal take da ƴan'uwan Aunty A'isha suke ji, a cewar su wai itama Umman kwad'ayi ne yasa ta bar Neehal take shige musu, dan ta ga suna da kuɗi. Ita kuwa Umma daɗin yanda Aunty A'isha da danginta suke son Neehal take ji, ga kuma tausayin Aunty A'ishan na rashin haihuwa da Allah bai ba ta ba, shi yasa ta bar mata Neehal ɗin, dan komai na Neehal yana hannun Aunty A'isha, dan in ba faɗa maka aka yi ba za ka ce ba Aunty A'isha ce ta haife ta ba, dan Umma tana mata kawaici sosai akan Neehal, dan ko abu ne za ta cewa Neehal je ki gurin Mamanki ta miki kaza, Mamanki kaza, Aunty'n Neehal ma take cewa Aunty A'isha. Abba kam sosai yake jin daɗin yanda Umman take wa Aunty A'isha, hankalinsa a kwance yake tun da kan matansa a haɗe yake. Ita kuwa Aunty A'isha sosai take girmama Umma, haka ma ƴan'uwanta, babu ruwansu da wai su masu kuɗi ne ƴan'boko, ita kuma Umma ƴar talakawa ce talakawan ma na ƙauye balle su wulak'anta ko suna mata gani_gani.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.