Neehal Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 6 of 104
Kafin la'asar Neehal ta dawo gida, tare suka taho gidan yau da Haneefah, a falo suka tarar da su Mama da kannenta guda biyu mata masu kama da ita, sun zo yiwa Hajiya sallama, Aunty A'isha da Aunty Sadiya, Neehal ta tafi da sauri ta rungume Aunty Sadiya dan tafi kusa da kofa, Haneefah kuma ta rungume Aunty A'isha, Neehal ta ce "Aunty Sadiyata welcome" Aunty Sadiya na murmushi ta ce "Yawwa my daughter, ya aiki?" Neehal ta ɓata fuska cike da shagwab'a ta ce "Alhamdulillah, sai gajiya" Aunty Sadiya ta ce "Sorry dear, za ta tafi ne itama" sakin Aunty Safiya ta yi ta koma ta yi hugging Aunty A'isha tare da gaisheta" Aunty A'isha na murmushi ta ce "Lafiya k'alau, Neehal yanzu an gujeni ko, yaushe rabonku da gidana" Neehal ta ce "Kai Aunty ko wata fa ban yi da zuwa ba" Aunty Aisha' ta ce "To ai da ko sati ba kya yi ba ki zo ba, ko Anwar d'inne ya hana ki fita?" Haneefah tay karaf ta ce "Baruwan Angonmu, Mama ce ke hanamu fita" Mama ta harare ta ta ce "Ta yaya zan bar ku ku fita ba'amun aiki ba, duk randa fa ba su je aiki ba ko school, wuni suke a d'aki su na shiririta, sai na je na fatattako suke saukowa su yi abun da ya dace, can gidan Barrister ma ta ce in sun je haka suke, kamar wasu yara" Neehal ta turo baki gaba ba ta ce komai ba, ta zauna kusa da Hajiya, wadda ta ƙurawa TV ido ta na kallo. Aunty A'isha ta yi murmushi kawai, Haneefah ta dubi Aunty Sadiya ta ce "Aunty Sadiya dama ina shirin kiranki, wasu freinds ɗinmu sun turo mun kuɗin ankon Neehal bari na yi miki transfer yanzu" Aunty Sadiya ta ce "Toh, na atamfa ne ko na lece?" Haneefah ta ce "Duka" Neehal ta lumshe idonta gabanta na faɗuwa, tunawa da ta yi nan da 2 months fa inda rai da lafiya an yi aurenta, shikenan za ta bar Mamanta da Yayanta da Dad ɗinta mutane mafi soyuwa a gareta, ƙoƙarin mai da kwallar da ta ciko idanta ta yi ta mik'e ta wuce sama. Da yamma bayan su Neehal sun ci abinci sun yi wanka suka tafi gidansu Haneefah, Mommy ta na zaune a falo suka shigo gabad'aya suka yi kanta suka ruk'unk'ume ta, Mommy ta ce "Uhm, Allah ya kawo ku, Kwana biyu bakina shiru amma yau za ku zo ku samun ciwon kai" Neehal ta ɓata fuska ta ce "Kai Mommy ko irin yar tarb'ar nan ma babu" Mommy ta ce "Ban san ta ba, ba kuma zan yi ba, a ɗaga mun jiki Ni, ba daɗi nake ji ba" Haneefah ta tashi daga jikin Mama tana faɗin "Shiyasa wlh gwara gidan Mama sau dubu da nan" ta ƙarashe zancen ta na shigewa kitchen. Mommy ta ce "Ni da za ki tattara kayanki, ki koma gidan Maman da kin taimaka mun" Neehal ta yi dariya ta ce "Ai ba za ki iya kwana 2 ba ki ga Besty ba, abun da ko kwana ɗaya ta yi kinta kiranta a waya kina ta dawo" Mama ta ce ''Ai dan ba Ni da mai mun aiki ne, amma ba wai kewarta nake ba" Haneefah ta dawo falon ta na duban Mama ta ce "Mama cake za mu yi wa ya Anwar, na gidan Mama kwananne ne, kuma na duba kitchen kamar ba ki da butter" Mama ta ce "Babu kam, amma bari na ba wa idi ya karb'o, tun da ɗana za'aiwa" Neehal ta ce "Au da mu za mu ci, ba za ki bayar a siyo ba?" Mommy ta ce "Sai dai ku siyo da kanku ko kuma ku haƙura da cin" Haneefah ta ce "Mommy nan da wasu watanni fa kin dena ganinmu a kai a kai, ki dinga lallaɓamu fa" Mommy ba ta kula ta ba ta shige ɗakinta dan ɗakko kuɗi. Neehal ta dubi Haneefah da damuwa a fuskarta ta ce "Besty Yau gabad'aya ban ga Yayana ba, ba na jin daɗi" Haneefah ta ce "Why?" Neehal ta ce "Da safe da zan fita, na san ya na bacci, da muka dawo kuma ban ga car ɗinshi ba, na tambayi Mama shi, ta ce sun fita tare da Dad" Haneefah ta ce "ki kirashi mana" Neehal ta ce "Good idea" ta ƙarashe zancen tare da zaro wayarta daga cikin small handbag ɗinta mai kyau, kiran duka numbobin sa ta yi amma bai ɗauka ba.
Bayan Magriba Neehal na zaune a gaban madubin ɗakinta ta na d'aura ɗankwalin atamfar da ke jikinta, dawowarta kenan daga gidansu Haneefah ta sauya kaya ta fara shiryawa kafin Anwar ya ƙaraso. Wayarta dake kan mudubinne ta fara ringing cikin amon sautin wak'a mai daɗi irin ta masoya, murmusawa ta yi ta kai hannu ta ɗauki wayar dan tasan Anwar ne ya ƙaraso tun da shi kaɗai ta sawa wannan ringing ɗin, ta ɗaga kiran tare yin sallama cikin siririyar muryarta, Anwar ya amsa tare da faɗin "Gimbiyata na ƙaraso" ta yi murmushin jin daɗi mai sauti ta ce "Welcome Sir" shima murmushin ya yi tare da katse wayar, Neehal ta ƙarasa daurinta ta feshe jikinta da da daɗaɗan turarukanta masu sanyin ƙamshi, wanda idan mutum ba matsowa kusa da ita ya yi ba, ba zai ji k'amshin ba. Ɗakin Mama ta lek'a ta sanar mata Anwar ya zo ta fita, Mama ta ce sai ta dawo, ta kuma gaishe da Anwar ɗin, a falon ƙasa ta tarar da su Dije su na kallo, ta dube su ta ce "Aunty Dije dan Allah idan babu damuwa ki ɗan biyo ni da cake ɗin can, zan ɗau drinks ne" Dije ta je "Haba uwar ɗakina babu damuwar komai" Neehal ta yi murmushi ta ce "Toh Nagode" Zulai ta ce "Kawai ki wuce zamu kawo miki har ruwanma, kar yay ta jiranki" Neehal ta ce "Toh Nagode sosai"
Ya na zaune a kan fararen kujerun da suke zama koyaushe dan yin zancen, ya na latsa wayarsa, ya na sanye cikin wata shadda light blue, da ta haska choculate colour É—in fatarsa wadda ta nuna zallar jin daÉ—in da yake ciki, Anwar Kyakkyawane a jin farko a sahun kyawawa, dogo ne amma bashi da jiki sosai. Neehal ta Æ™araso gurin tare da yin sallama, Anwar ya d'ago ya na bin ta da wani kallo k'auna, wadda ya sata saurin sunkuyar da kanta Æ™asa cikin jin kunya, ya amsa mata sallamar ya na Æ™ara k'ura mata ido, Neehal ta turo baki gaba cikin shagwab'arta ta ce "Ina yini" ya yi murmushi ganin yanda ta yi, kasancewar gidansu Neehal akwai wadatuwar haske sosai ko mun dare, shiyasa ya ke kallonta tar" ya ce "Lafiya k'alau, ya Mama" ta ce "Tananan k'alau ta na gaisheka" ya ce "Ina amsawa tare da ajiye wayarsa a kan É—an table É—in robar da ke gabansu, cike da soyayya da kulawa ya ce "Me ya faru ne, na ga kamar Queen na fushi da Ni" Neehal ta Æ™ara shagwab'e fuska ta ce "Nothing, kawai kai ne na ga ka na ta kallo na" murmushi Anwar ya yi me sauti ya ce "Dan mutum ya kalli matarsa laifine, ni fa gaskiya kunyar nan ta ki ta na cutata, dan ma kwanaki kaÉ—an suka rage ki zama mallakina na cire miki ita gabad'aya" Neehal ta Æ™ara sunkuyar da kanta Æ™asa ba ta ce komai ba, saboda fad'uwar da gabanta ya yi, a dalilin zancen auransu da Anwar ya yi, ta rasa me ya sa tun da auransu ya matso take jin hakan a tattare da ita, a da kuma farkon soyayyarsu ba ta jin komai, burinta kawai a lokacin a ce sun mallaki juna, saboda tarin k'aunar da take masa, amma yanzu duk sai ta ji jikinta ya yi sanyi da auran. Anwar bai yi tunanin wani abu a shirun da Neehal ta yi masa ba, dan ya riga ya saba da halinta na jin kunya idan suna tare, saÉ“anin idan suna waya ko chat da take zagewa ta na rattabo masa kalaman soyayya, amma idan ya zo gurinta sai dai ya yi ta hirarsa shi kaÉ—ai, ita daga um sai um'um, in kuma ta so wani lokacin ta zage su sha hirarsu. Anwar ya Æ™ara cewa "Yau ko um É—inma ba zan samu ba Queen, sai dai shiru?" Neehal ta yi murmushi a Æ™oÆ™arin ta na ganin Anwar din kar ya yi tunanin wani abu ta d'ago kanta tana kallonshi amma ba ido cikin ido ba ta ce "Za ka samu mana, harma fiye da haka" Æ™arasowar su Dije gurin ya hana Anwar maganar da yake son yi, su ka yi sallama Neehal da Anwar suka amsa musu a tare, gaishesa suka yi tare da ajiye kayan hannunsu a gaban Anwar din, Anwar ya amsa musu tare musu godiya suka juya suka tafi. Neehal ta mik'e ta tsiyaya masa ruwa da lemo a glass cup, sannan ta koma ta zauna suka cigaba da hirarsu ya na shan drink d'in kaÉ—an_kaÉ—an. Can Anwar ya dubeta ya ce "Queen ni fa yau na zo miki da babbar tsaraba" Neehal ta ce "Ta me kenan?" Bai ba ta amsa ba sai hannunsa da ya zira a aljihun rigarsa ya É—akko wani abu da Neehal ba ta gane mene ba, buÉ—e É—an Æ™aramin case É—in ya yi wani zobe mai kyau ya bayyana, Neehal ta waro manyan idanunta ta ce "Wow ya Anwar ring É—in nan ya yi kyau sosai fa" ya ce "Sai ma kin san a wannan kyakkyawan finger É—in naki, na san sai ya Æ™arawa zoben kyau" Neehal ta yi murmushi, Anwar ya É—akko zoben dake ta k'yalk'yali ya ce "Kawo Hannunki in saka miki, na ki ne na kawo miki" Neehal ta ce "Nagode sosai Ya Anwar, amma Ni dai ka ba ni in saka da kaina" Anwar ya ce "A'a my Queen ni dai ki barni na sa miki" Neehal ta yi shiru ba ta ce komai ba, domin ba za ta iya musu da Anwar É—in ba, hannun damanta ta kalla, a hankali ta sa hannun hagunta ta cire zoben dake babban É—anyatsanta ta ajiye, sannan ta miÆ™a masa É—anyatsan, murmushi Anwar ya yi ya matso ya zira mata zoben, hakan ya yi dai_dai da fitowar Ameen daga part É—insa domin tafiya Masallaci dan anfara kiran sallar isha'i, karaf a idanunsa Anwar ya zira wa Neehal zobe...........âœï¸
[7/21, 9:00 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.