Complete Hausa Novels

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 62 of 104

Mama sai kallon su take cike da tausayawa, haka ma Musbahu da bakinsa ya kasa rufuwa dan murna. Ahmad ya manta da kowa da yake gurin yaransa kawai yake biyewa suna hirarsu, wani irin wasai yake jin zuciyarsa ta masa, gaba-ɗaya damuwar dake cikinta ta gushe sai wani sanyi ne yake ratsata. Su Afrah sai labarin new Aunty'nsu (Neehal)  suke bashi da kuma school ɗin da suke zuwa. Tun kafin ya ga Antin tasu ya ji yana k'aunarta saboda kulawar da ta yi da sanyin idaniyarsa, ya fara tunanin mai zai mata a duniyar nan wanda zai faranta mata a matsayin tukuici. Lokaci ɗaya ya koma ainihin Ahmad ɗinsa mai yawan fara'a da saurin sabo da mutane. Kasa daurewa ya yi ya kira Mahaifiyarsa ya sanar mata wannan abun farinciki. Farincikin data tsinci kanta a ciki ba zai misaltu ba, ta cewa Ahmad kar ya taho Abuja ya jira komai dare za su zo Kano su yiwa gidan da suka riƙi su Afrah godiya. Suna gama wayar kuma ta shiga kiran ƴan'uwa da abokan arziki tana sanar musu anga su Afrah.

Neehal tana kwance tana chatting da Habibinta bata san mai yake faruwa a gidan nasu ba. Shigowar Mama yasa ta tashi zaune. Mama ta ce "Har yanzu bacci kike ne?" Ta ce "A'a idona biyu, yanzu ma so nake na tashi na je saloon a wanke mun kai na." Mama ta ce "Jiya da kika je ɗauko su Afrah ashe kin gamu da wani yace miki ya san su?" Gabanta ya faɗi ta dubi Mama da sauri ta ce "Eh, amma wa ya faɗa miki?" Mama ta ce "Da kansa ya zo ya faɗa mun, yanzu haka ma suna part ɗin baƙi shi da Mahaifin su Afran." Neehal ta waro Idanunta sosai ta ce "Ta yaya suka san suna gidan nan to? Mama anya kuwa dagaske mahaifin nasu ne? Kar fa wasu su zo su yi miki ƙarya." Mama ba ta ce komai ba ta girgiza kai kawai ta juya ta fice. Neehal ta sauko daga kan gadon da sauri ta biyo bayan Mama ƙirjinta na dokawa. A falo ta ci karo da Amrah sanye cikin uniform, cikin murna Amrah ta kama hannunta ta ce "Aunty Daddy ya zo, ki zo mu je ki gan shi ya ce mu kirawo ki, ashe dama ya san gidan nan?" Neehal ta shafa fuskar yarinyar ta ce "Dagaske Daddy'nku ya zo? Yana ina?" Amrah ta ce "Yana wani falo, mu je ki gan sa." Neehal ta tsaya cak cikin tsananin shock, zuciyarta cike da murnar bayyanar iyayensu. Ta kama hannun Amrah tana murmushi suka koma ɗakinta ta ɗauko Hijab ta zira, sannan ta ƙara kamo hannunta suka fito. A kitchen ta tarar da Mama da su Dije suna ƙoƙarin haɗa girki dan tarb'ar baƙi, dan Ahmad ya sanar mata su Umminsu suna nan tafe. Haka Kawai Neehal ta tsinci kanta cikin farinciki, duk da ta san lokacin rabuwa da twins ɗinta ya yi za su koma gurin iyayensu, tunda Allah ya bayyana su. Sai dai kuma suna zuwa part ɗin baƙin ta ji gabanta ya faɗi, ta ɗan tsaya a bakin ƙofar falon tana jin jikinta wani iri. Amrah ta ce "Aunty Daddy'n yana cikin falon nan mu je ki gan shi." Neehal ta ce "Toh." Cikin sauke numfashi, sannan ta ƙarasa ta tura ƙofar falon a hankali ta shiga bakinta ɗauke da sallama cikin zazzak'ar muryarta. Ahmad wanda yake ta murmushi yana sauraren hirar da Afrah take masa ya d'ago ya dubi ƙofar falon, karaf idanunsa suka sauka akan Neehal wadda kanta ke ƙasa, hannunta riƙe da na Amrah........✍️
[7/21, 9:31 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*

_By_
_Zeey Kumurya_

*4️⃣0️⃣*

Samun kansa ya yi da kafe ta da ido kamar mai san gano wani abu a tattare da ita. Afrah ta sauka daga jikinsa ta tafi gurin Neehal da gudu cikin murna tana faɗin "Aunty! Daddy'nmu ya zo, kin gan shi." Ta ƙarashe maganar tare da kamo hannunta tana nuna mata Ahmad. Neehal ta d'ago kanta tana murmushi ta shafa kan Afrah ta ce "Thank God." Ai Ahmad ji ya yi gaba-ɗaya yawun bakinsa ya ƙafe ƙaf tare da wani irin bugawa da zuciyarsa ta yi. Ƙara ware idanunsa ya yi a kanta dan tabbatar da abun da yake gani kar ya je ko idon ne yake masa gizo, har abada ba zai taɓa manta wannan kyakkyawar fuskar ba. Neehal ta ɗan saci kallonsa a hankali cikin sanyin muryarta ta ce "Ina yini." Ahmad ya sauke wani dogon numfashi yana murmushi ya ce "Lafiya k'alau Aunty." Neehal bata kuma ce masa komai ba saboda tsintar kanta da ta yi uncomfortable tun shigowar ta falon, ta mayar da kallonta ga Musbahu wanda yake ta aikin latsa waya, posting ɗin hotunan su Afrah yake a social media tare da yin note ɗin bayyanarsu. Gaishe sa ta yi, ya d'ago ya dube ta tare amsa mata cikin fara'a, ita kuwa duk sai ta ji kunya ta kama ta saboda abun da ta yi masa jiya dan ta shaida sa. A hankali ta ƙarasa kan kujera ta zauna, su Afrah na jikinta suna mata hirar Daddy'nsu, duk da gashi nan a zaune a gabanta ya zuba mata na mujiya, ko kifta idanunsa ba ya yi. Amrah ta koma jikinsa tana masa surutu, amma ba ya ma saurarar abun take cewa, zuciyarsa gaba_ɗaya tana gurin Neehal. Ita kuwa Neehal tun tana daurewa tana biyewa Afrah har ta yi mata shiru tare da turo bakinta gaba, duk d'agowar da zata yi sai sun haɗa ido da shi, gashi idanun nasa sun sa ta fara jin wani iri ajikinta, gaba-ɗaya  ya dabaibaye ta da kallonsa. Gajiya ta yi da kallon nasa ta miƙe ta fice daga falon a ranta tana faɗin "Wannan kuwa lafiyarsa k'alau? Ko dai ganin yaransa ne ya zautar da shi?" Ahmad ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da lumshe idonsa bayan ta fice. *Fateemah,Neehal,Princess.* Ita ce ko mai kama da ita? Dagaske ita ya gani ko kuma dai mafarki yake? Idan ita ce wacce irin *Ranar sa'a* ce wannan a rayuwarsa? "Oh my God!" Ya faɗa cikin siririyar murya, at first da ya ganta ji ya yi kamar ya je ya rungume ta, ba ƙaramin control ɗin zuciyarsa ya yi ba wajen ganin bai aikata hakan ba, sai dai duk yadda ya so ɗauke idonsa daga kanta kasawa ya yi, wani maganaɗisun abu ya ji yana fizgar zuciyarsa a game ita, wadda bai taɓa jin irinsa akan wani mahaluƙi ba.

Neehal ta koma part ɗin Mama tana ɓaɓɓata fuska, a ranta tana ta gulmar Ahmad. Sosai ta ga kamminsa da yaransa kamar ma ya fi su kyau. Kitchen ta shiga suka cigaba da aiki tare da su Mama. Sai da su Ahmad suka tafi masallaci sannan su Afrah suka dawo part ɗin Mama, a lokacin ne kuma Daddy ya ƙaraso gidan. Bayan sun dawo daga masallaci Mama ta aika musu da drinks da ɗan abun tab'awa. Neehal tana cikin Sallah Afrah ta shigo ɗakinta tana faɗin "Aunty ki zo in ji Daddy'nmu." Ganin tana Sallah sai yarinyar ta fita. Ko da ta idar ƙin fita ta yi, ta ɗauko wayarta dan kiran Haneefah da Sadik ta sanar musu bayyanar iyayensu Amrah.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.