Complete Hausa Novels

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 63 of 104

 Kafin la'asar Su ummi sun ƙaraso Kano zuciyoyinsu cike fal da farinciki, Ahmad da kansa ya je ya ɗauko su a Airport. Su uku suka zo, da Ummi da wata ƙanwarta Aunty Mardiyya sai Zahra ƙanwar Ahmad. Cikin fara'a da mutuntawa Mama ta karɓe su hannu bibbiyu. Aunty A'isha ma ta zo a lokacin, Aunty Sadiya ce dai ba ta zo ba tana gurin aiki. A part ɗin Mama aka sauke su, hakan yasa su Ahmad su ma suka dawo nan. Ummi ta rungume su Afrah a jikinta tana hawaye tare da godiya ga Ubangiji, murnarta guda biyu ce a wannan rana, ta farko bayyanar jikokin nata, na biyu kuma ta san yanzu farinciki da walwalar ɗanta za su dawo, kuma lafiyarsa zata samu Insha Allah. Su Afrah kam yau take Sallah a gurinsu, kowa sai rungumar su yake da murnar ganin su, suma daɗi suke ji ba kaɗan ba na ganin su cikin ahalinsu. Bayan an gama murnar, su Ummi sun yi sallar la'asar Mama ta gabatar musu da abinci. Ahmad kuwa duk wannan abun da ake rabin hankalinsa ne a gurin, rabi yana gurin Neehal, ga shi ko wulgawarta bai ƙara gani ba, ya tura su Afrah ya kai sau biyar su kira ta amma Neehal ta ƙi fitowa, sai dai su dawo su ce masa bacci take. Bai taɓa tunanin akwai abun da zai iya ɗauke masa hankalin murnar ganin Ƴaƴansa ba, sai gashi tozalin da ya yi da Neehal ya raba masa hankali, wani irin farinciki yake ji a cikin ransa, burinsa kawai yanzu ya samu ya tattauna da ita dan ya tabbatar ita ɗin ce.

 Bayan su ummi sun gama cin abincin aka zauna zaman mai da zance. Ummi ta dubi Mama ta ce "Yanzu duk tsawon watannin nan yaran nan suna tare da ku a gidan nan? Tsintar su kuka yi ko yaya?" Mama ta bawa Ummi labarin yanda Neehal ta tsinci su Afrah, da yanda akai ta cikiyar neman iyayensu . Cikin al'ajabi Ummi ta ce "Ikon Allah, Ubangiji ne ya kub'utar da yaran nan daga hannun azzaluman da suka ɗauke su, domin kuwa duk wanda ya ɗauki yaran nan da wani mugun nufin ya ɗauke su sai kuma Allah bai bashi nasarar cimma abun da ya yi niyya ba akansu." Aunty A'isha ta ce "Fita suka yi waje aka ɗauke su ko kuma a makaranta ne?" Ummi ta ce "Ba ɗaya, har cikin gida har falonsu aka shigo aka ɗauke su. Ita mai kula da su ta shiga wanka a ɗaki, su kuma suna falo suna kallo, sai fitowa ta yi ta ga babu su a falon, ta shiga ƙwala musu kira tana zaga ko ina na gidan amma bata gan su  ba, ta fito ta tambayi mai gadi a ruɗe ko ya ga fitarsu ko kuma shigowar wani ya fita da su, amma ya ce babu wanda ya shigo kuma babu wanda ya fita. Hankali a tashe ta kira ni ta sanar mun, na kira mahaifinsu na tambaye shi ko shi ya dawo ya ɗauke su, ya ce shi bai ma koma gida ba yana office, na kira gidan kakaninsu nan ma suka ce ba su zo ba. Wasa_wasa ƙaramin abu ya zama babba, muka fahimci yara fa sace su akai, tunda har dare babu su babu labarinsu. Tashin hankalin da muka shiga ba zai misaltu ba, mahaifinsu kuwa yanke jiki ya yi ya faɗi a sume ciwonsa ya tashi. In tak'aice miki zance ya sha jinya kamar ba zai rayu ba, har waje sai da aka fita da shi, daga baya kuma Ubangiji ya kawo masa sauƙi, har ya warware. Ba mu fi wata da dawowa daga India ba, satinsa biyu ma da komawa gurin aiki." Mama ta ce "Allah sarki, yaran mahaifiyarsu ta rasu ko?" Ummi ta ce "Ehh, a gurin haihuwar su Allah ya mata rasuwa." Mama ta ce "Allah ya ji k'anta ya gafarta mata." Nan dai sukai ta tattaunawa akan batun, Ummi ta kira Ammi kakar su Afrah ta haɗa ta da Mama, ta yi mata godiya sosai, sannan ta bawa su Afrah wayar ta ji muryar ƴan jikokin nata kafin ta gan su. Ummi ta kalli su Afrah ta ce "Ni fa tun d'azu ana ta bani labarin Aunty amma har yanzu ban gan ta ba." Mama ta ce "Au bata sakko ba, ban ma lura ba muna ta hira bari na kira ta." Mama ta miƙe ta hau sama su Afrah na biye da ita a baya. Fitowarta kenan daga wanka Mama ta shigo ɗakin, Mama tana kallonta ta ce "Kakannin su Afrah sun zo amma shine baki sauko kun gaisa ba dan iskanci." Neehal ta ce "Mama bacci ne fa ya ɗauke ni, yanzu na tashi." Mama bata ce komai ba ta juya ta fita. Afrah ta ce "Aunty, Ummi da Aunty Zahra sun zo suna falon ƙasa." Neehal ta ce "To bari na shirya mu je na gan su."

Tare suka sauko da su Afrah, tunda ta fara sakkowa ya zira mata na mujiya yana sakin ajiyar zuciya, sai ya ga kamar ta ƙara yi masa kyau fiye da d'azu. Neehal bata lura da shi ba ma a falon, ta gaishe da Ummi cikin girmamawa, Ummi ta rungume ta tana sanya mata albarka tare da yi mata godiya cikin k'aunarta. Tana dariya ta ce "Zauna anan kusa da ni kin ji d'iyata ƴar albarka." Neehal ta yi ƙasa da kanta cikin jin kunya. Zahra ta waro Ido ta ce "Laaa kamar Neehal ɗin ASTV." Aunty A'isha ta yi murmushi ta ce "Ita ce." Zahra ta dawo kusa da Neehal tana murmushi ta ce "Nice to meet you Aunty Neehal and I love You." Ta yi murmushi itama ta ce "Thank you, ya kike?" Zahra ta ce "Lafiya k'alau." Hira Zahra ta shiga yiwa Neehal, dan ba laifi akwaita da surutu. Neehal kuwa gaba_ɗaya jinta take a takure, ta rasa dalili kuma, nan kuwa kaifin idanun Ahmad ne yake yawo a jikinta. Ta ɗan juyo dan ta gaishe da Aunty Mardiyya karaf suka haɗa ido da shi ya mata ƙuri, ta ɗauke idanunta da sauri a ranta tana mitar yau ta gamu da gamon ta, mutum daga zuwa ya mayar da ita TV'nsa. Bayan sun gaisa da Aunty Mardiyya ta janyo Afrah ta mata raɗa a kunnenta da faɗin "Je ki cewa Daddy ya daina kallo na." Yarinyar ta kalle ta zata yi magana Neehal ta ce "Shiiii, go and tell him I will give you chocolate." Afrah ta tafi da sauri ta haye jikinsa, cikin raɗa kamar yadda Neehal ta ce mata ta ce "Daddy, Aunty ta ce ka daina kallon ta." Ahmad ya ja hancin yarinyar ya ce "Go and tell her, ciwo idona yake mun idan ban kalle ta ba." Afrah ta ce "Daddy kasa glass ɗinka zai daina ciwon." Ya girgiza mata kai ya ce "No, idan ina kallon Aunty ne kawai zai daina." Afrah ta tashi daga jikinsa ta koma gurin Neehal ta faɗa mata abun ya ce. Neehal ta kalle shi tana turo baki gaba, shi kuma ya wani marairaice fuska yana ƙara tsare ta ido tare da sakar mata murmushinsa wanda yasa ta ji gabanta ya faɗi, da sauri ta ɗauke kanta daga kallon sa tana ɓata fuska. Wajen ƙarfe biyar suka fara shirin tafiya, Mama ta ce Su bari sai gobe mana, amma Ummi ta ce "Ba zai yiyu ba, dan Family suna can suna jiran dawowar su, kowa yana d'okin ganin su Afrah, tun yanzu an fara addabarta da kira inaga sun kwana." Mama ta dubi Neehal ta ce "Je ki haɗowa su Afrah kayansu." Ta miƙe da sauri dama duk a takure take da kallon da Ahmad ya addabe ta da shi, Zahra ta bi bayanta dan taya ta haɗa kayan. Jiki a matuƙar sanyaye ta shiga haɗa musu kayan, tare da ƙoƙarin danne kukan da yake ƙoƙarin k'wace mata. Bata taɓa tunanin zata rabu da twins ɗinta nan kusa ba, tana son yaran sosai ta shak'u da su over, suna matuƙar ɗebe mata kewa, yanzu gashi rana ratsa Allah zai raba su kamar yadda ya haɗa su. Ta haɗa musu kayan sawarsu a wata ƙatuwar jaka, suka kama ita da Zahra suka sauka da ita ƙasa. Ahmad ya taso da sauri ya karɓe su yana faɗin "Sannu Aunty, thank you so much." Ta yi masa shiru ba ta ce komai ba sai ma juyawa da ta yi ta koma sama. Ummi ta dubi Zahrah ta ce "Ta tattara kayan da suka ci abinci ta kai kitchen." Ahmad ya faki idon mutanen falon ya bi bayan Neehal da sauri. Yana shiga falon sama ita kuma tana rufo ƙofar ɗakinta, hakan yasa ya gane nan ta shiga ya nufi ɗakin cikin murna ya tura ƙofar ya shiga. Tana shiga ita kuma kukan da take ta dannewa ya kufce mata, ta kwantar da kanta a jikin gado ta shiga rera shi. Ya tsaya a bakin ƙofa tare da hard'e hannuwansa a ƙirjinsa yana sauraren sautin kukan da take, wanda ko ba'a faɗa masa ba ya san na rabuwa da twins ne........✍️
[7/21, 9:31 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.