Neehal Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 65 of 104
Ranar Asabar da yamma ta dawo daga gurin aiki ta tarar Hameedah da Mommy'nta sun zo gidan. A gajiye take amma duk da haka ta zauna a falon Æ™asa inda ta tarar da su da fara'arta ta ce "Sannunku da zuwa." Hameedah ta mata wani shegen kallo ta É—auke kanta. Haj. Saratu ba yabo ba fallasa ta ce "Yawwa." Neehal ta ce "Ina yini Mommy." Hajiya Saratu ta ce "Lafiya, ashe an yi bikin Æ™awar nan taki mara kunya?" Neehal ta ce "Eh." Cikin rashin jin daÉ—in mara kunyar data kira Haneefah da shi. Hajiya Saratu ta tab'e baki ta ce "Ke kuma yaushe ne naki bikin?" Neehal ta ce "Mommy idan an saka bikina ai zaku ji." Hajiya Saratu cikin baÆ™in ciki ta ce "Au da akwai wanda kike kulawa yanzu kenan?" Neehal ta ce "Eh." Cikin takaici Haj.Saratu ta ce "Wanne me rabon É—orawa iyayensa asararsa ne? Ko kuma munafuntarsa akai ba a gaya masa matsalar da kike da ita ba?" Neehal ta yi shiru dan ta gane inda maganar Haj Saratu ta dosa. Hameedah ta ce "Kema dai Mommy ban da abinki ai kin san baza a faÉ—a masa ba tunda ana neman a shiga daga ciki kar a tsufe a gida." Haj. Saratu ta ce "Hakane fa daughter, shi dai Yaya Muhammad Allah ya haÉ—a shi da masifa, yana zaman zamansa za'a É“ata masa suna a idon duniya, daga ya fito a dinga nuna shi ana yarinya ce a gidansa ta zama annoba duk wanda zata aura sai ya mutu." Mama dake sakkowa daga sama karaf maganganun Mommy a kunnenta, ta yi wani murmushi ta ce. "Saratu kenan." Haj Saratu ta ce "To Æ™arya na faÉ—a ne, ai gaskiya ce, wa ya sani ma ko dama can dangin nata sun san annoba ce ita shi yasa suka Æ™i riÆ™e ta karta zame musu masifa." Har Mama zata kuma magana sai kuma ta fasa, ta san dama haka Haj. Saratu take so ta tanka mata su yi ta yi, ita kuma bata da wannan lokacin. Ta dubi Neehal da take kuka sosai na kiranta annoba da Hajiya Saratu ta yi ta ce "Tashi ki wuce sama." Ta miÆ™e ta zari jakarta tana share hawaye ta yi sama, Mama ta bi bayan ta, ta bar Haj. Saratu tana cigaba da faÉ—ar bak'ak'en maganganu marasa daÉ—i akan Neehal. A kan kujera ta tarar da Neehal ta kifa kanta tana kuka. Mama ta janyo ta jikinta ta shiga lallashinta tana faÉ—in "Ki yi shiru haka kukan ya isa, kar ki É—auki maganganunta na banza ki saka a ranki har su zo suna damunki, na san halinki da saka abu a rai." Ta d'ago ta, ta shiga share mata hawayen fuskarta. Sosai maganganun Haj.Saratu suka daki zuciyar Neehal, musamman idan ta tuna kalmar annoba da Hajiya Saratu ta kirawo ta da ita, hakan yasa hawayenta suka Æ™i tsayawa. Mama ta tashi ta shiga dakinta ta barta a falon. Haj. Saratu tana cikin mitar ta Ameen ya shigo falon, tana ganinsa ta yi shiru. Hameedah ta faÉ—aÉ—a fara'a cikin iyayi ta ce "Yaya Ameen sannu da zuwa." Kallo É—aya yay mata ya É—auke kansa tare da amsa mata ciki_ciki. Ba yabo ba fallasa ya gaishe da Haj. Saratu sannan ya haye upstairs abinsa. A falo ya tarar da Neehal durk'ushe inda Mama ta barta tana kuka, ya bita da kallo tare da faÉ—in "Me aka yi miki kike kuka?" Neehal ta d'ago kanta jin muryarsa amma ba ta ce komai ba, ya Æ™araso ya tsugunna a gabanta a É—an ruÉ—e ya ce "FaÉ—a mini me ya faru?" Neehal ta share hawayenta ta ce "Mommy ce, ta kira ni da annoba." Sai ta kuma fashewa da kuka. Shiru ya yi cikin É“acin rai, ya rasa uwar me Neehal ta tsarewa Haj. Saratu a rayuwa ta tsane ta. A hankali ya matso daf da ita ya janyo ta jikinsa ya rungume ta tsam a Æ™irjinsa ya shiga rarrashinta..........âœï¸
[7/21, 9:31 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*4ï¸âƒ£2ï¸âƒ£*
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*
Lamo ta yi a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya tare da barin kukan da take. A hankali ya d'ago ta daga jikinsa yana dubanta da murmushi akan fuskarsa ya ce "Je ki wanke fuskarki ki zo ki raka ni unguwa." Ta gyaɗa masa kai tare da miƙewa ta shige ɗakinta. Ya bita da kallo cikin sauke numfashi. Miƙewa ya yi shima ya shiga ɗakin Mama. Bayan ya yi sallama ta amsa sun gaisa ya zauna a gefenta tare da faɗin "Mum ki taya ni murna, next month zan dawo Kano da aiki Insha Allah." Mama ta ce "Masha Allah, na ji daɗin hakan sosai, ka ga an huta da fargabar barin Hafsah ita kaɗai a gida." Ya ce "Hakane, bari in je masallaci na ga lokacin Sallah ya gabato, idan na dawo zamu fita da Mimerh." Mama ta ce "Fita kuma? Zuwa ina?" Ya ce "Unguwa." Ta ce "Ita unguwar bata da suna?" Yana miƙewa ya ce "Sirri ne tsakanin Yaya da ƙanwarsa." Mama ta tab'e baki ta ce "Kamar gaske." Ya yi murmushi kawai tare da ficewa daga ɗakin. Itama Neehal data shiga toilet bayan ta wanke fuskarta ganin Magriba ta gabato sai ta ɗauro alwala ta fito. A gaban mudubi ta tsaya ta ɗan gyara fuskarta ta saka kwalli a idanunta saboda kukan da ta yi. Bata canza kaya ba, mayafi kawai ta ɗauko ta yafa ta ajiye hijabin da yake jikinta. Ɗakin Mama ta shiga dan sanar mata Ameen ya ce za su fita, zuciyarta cike da mamakinsa dan ta manta rabon da su je unguwa ko wani gurin tare da shi, dan tun da ko Mama ta ce ya kaita School ko gurin aiki sai ya haɗa ta driver, ya ce shi ba direbanta ba ne. Ta tarar Mama tana toilet tana alwala, ganin ƙofar toilet ɗin a buɗe ta ƙarasa bakin ƙofar ta ce "Mama Yaya ya ce zamu fita yanzu." Mama ta ce "Ya faɗa mun, amma ai kya ci abinci kafin ku tafi." Ta ce "Bana jin yunwa." Mama ta ce "Shikenan ai, ki je ki yi sallah kafin ya dawo, shima ya je masallaci." Neehal ta ce "Toh." Ta dawo cikin ɗakin ta ɗauki darduma ta shimfid'a ta zira hijabin Mama ta tayar da Sallah. After some minutes Ameen ya shigo ɗakin, yana duban Neehal ya ce "Tashi mu je kar dare ya yi." Mama ta ce "Allah ya tsare, saura kuma kafin ku dawo ka samun ita kuka, dan na san hali." Ya yi ɗan yi murmushi bai ce komai ba. Neehal ta yiwa Mama Sallama suka fice a tare. Yanda ta bar Haj.saratu da Hameedah haka suka sauko suka same su, da alama ko tashi sun je sun yi sallah ba su yi ba. Ba suce musu ƙala ba suka fice, su kuma su Hameedan suka raka su dana mujiya. Bayan fitarsu Hameedah ta dubi Mahaifiyarta ta ce "Sabon salo b'arawo da sallama, ko ina kuma za su a daren nan?" Haj Saratu ta ce "Oho musu, amma ni fa na fuskanci take_taken Haj. Fatima so take ta aurawa Ameen shegiyar yarinyar can." Hameedah ta lailayo ashariya ta ce "Tab'dijan, da kuwa an yi ƙaramin yaƙi a family wallahi, ta hana shi aure na sannan kuma ta aura masa wata can bare." Haj Saratu ta ce "Hmmmm, ba dai tak'amarta ita ta haife shi ba, to ai ba ɗanta ba ne ita kaɗai, wallahi matuƙar ta ce zata aurawa Ameen yarinyar nan da taƙi auruwa sai na yi sanadin barinta gidan nan, mu zuba mu gani ni da ita." Cikin damuwa Hameedah ta ce "Mommy ni duk ba wannan ba ma, wai ya batun aure na da Ya Ameen ne? kin ce mun wannan zuwan da mukai akan maganar auren ne, kuma ban ga wata alama da ta nuna hakan ba, ni fa gaskiya na gaji da gafara sa ban ga k'aho ba." Ta ƙarashe maganar cikin botsarewa. Mommy ta ce "Me kike ci na baka na zuba ne? Ki bari ki ga me zan yi mana, akwai shirin da nake yi, da zarar ya kammala zaki sha mamaki, ke dai ki kwantar da hankalinki bana son kina damuwar nan." Hameedah ta sauke numfashi cikin damuwa, ita yanda Ameen yake nuna halin ko in kula da ita yafi komai d'aga mata hankali, gashi ita babu wani wanda yake zuwa gurinta a yanzu da sunan saurayi. K'awayenta duk sun yi aure, ita ga kuɗin ga aiki tana yi amma babu mashinshini duk da uwar maganin farin jinin da uwarta take dirka mata.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.