Complete Hausa Novels

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 64 of 104

_By_
_Zeey Kumurya_

*4️⃣1️⃣*

Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*

A hankali ya fara takawa ya ƙarasa inda take, tsugunnawa ya yi a daf da ita cikin sanyin murya tare da marairaicewa ya ce "please Aunty ki daina kuka" Neehal ta d'ago kanta da sauri tare juyowa a tsorace dan ba ta ji shigowar shi ba, sai maganarsa kawai ta ji. Ta ɗan ja baya tare da kallonsa cikin mamakin ƙarfin hankalinsa na shigo mata har cikin daki. Ya marairaice fuska kamar ƙaramin yaro tare yi mata alamar rok'o da hannunsa. Ta tsaida kukan da take cikin jan numfashi tare da ƙoƙarin miƙewa tsaye, hannu ya zira a aljihun wandonsa ya ɗauko handkerchief ɗinsa ya miƙa mata, ta karb'a ba tare da ta ce komai ba, ta shiga share hawayen fuskarta. Wani sassayan k'amshi ya daki hancinta wanda yasa ta sakin ajiyar zuciya ba tare da ta shirya ba tare da lumshe idanunta. "Princesss!" Ya faɗa murya ƙasa_ƙasa tare da jan sunan, buɗe idonta ta yi da sauri ta sauke su akan fuskarsa cikin nazartar wani abu. 'Princess?' ta maimaita sunan a ranta kamar mai son tuno wani abu, kusancin da suka samu a yanzu yasa ta samu damar ƙarewa fuskarsa kallo sosai, sai ta ga kamar ta san fuskar, amma ta rasa a ina ta santa, ko kuma dan yana kama da su Afrah ne shi yasa. Ta kawar da kanta da sauri ganin yanda yake sakar mata wani murmushi wanda yake ƙoƙarin zautar da zuciyarta. 'Yana da kyau sosai.' ta faɗa a ranta tare da miƙewa tsaye da sauri kamar wadda aka tsikara, shima miƙewar ya yi still idanunsa na kanta. Ba tare da ta kalle shi ba ta miƙa masa hancky ɗinsa tare da faɗin "Thank you." Ya karɓa tare da faɗin "You are welcome, and I want to talk to you please." Da sauri ta kalle shi ta ce "Ni kuma?" Ya gyaɗa mata kai, ta ce "Okay ina jinka." Ya ɗan ja numfashi sannan ya fara magan "Tun d'azu nake son na miki godiya akan tsintar yarana da kikai a titi kika ɗauke su ba tare da ƙyama ko tsoron wani abu ba, and....." "Kar ka damu ai yiwa kai ne." Ta katse shi da faɗin haka. Ya yi murmushi ya ce "Duk da haka ba kowa ne zai iya abun da kika kai ba, hakan ya nuna kina da kyakkyawar zuciya mai cike da tausayi da jin ƙai. Allah ya biya ki ya albarkaci rayuwarki, ya yaye miki duk wani abu da yake damunki a cikin rayuwarki, ya yi miki tukuci da gidan Aljanna." Cikin jin daɗin addu'arsa ta ce "Ameen ya Allah na gode sosai, Allah ya raya mana twins." Ya ce "Amin, and secondly I......" Turo ƙofar ɗakin da akai ya katse masa maganar da yake yi. Zahra ce ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da Sallama. Da mamaki ta ce "Yaya dama kana nan, muna ta nemanka zamu tafi, Ummi ta kira wayarka baka d'aga ba." Ya juya ya nufi ƙofa yan faɗin "Ina nan ina yiwa Aunty godiya." Zahra ta yi murmushi ta ce "Gaskiya ne." Neehal ta ƙirƙiro murmushi tana kallon Zahra bayan ya fice ta ce "Har kun fito?" Zahra ta ce "Ehh, sai tafiya." Neehal bata kuma cewa komai ba ta ɗauki wata leda dake cike da kayan wasan su Afrah suka fice daga ɗakin zuwa downstairs.

Babu kowa a falon duk sun fice. a parking space suka tarar da su tsaitsaye suna sallama. Su Afrah suna hango Neehal suka rugo gurinta suna faɗin "Aunty Daddy ya ce dake zamu tafi, zaki je gidanmu ko?" Neehal ta shafi kuncinsu tare da gyaɗa musu kai. Zahra ta karb'i ledar hannunta ta zira a Mota sannan ta dawo ta karb'i phone Numbern'ta. Cikin matuƙar dauriya Neehal ta ƙarasa bakin Motar da za su tafi a cikinta ta cewa Ummi. "Ku gaida gida, Allah ya tsare." Ummi ta ce "Ameen d'iyata, sai mun kuma dawowa ko kuma in kin zo ganin ƴaƴanki." Neehal ta murmusa bata kuma cewa komai ba, dan tana buɗe baki ta san kuka ne zai kufce mata. Ta buɗe murfin Motar ta zira su Afrah wanda suka mak'ale mata su sai da ita zasu tafi. Ganin bata shigo motar ba tana ƙoƙarin rufewa suka fasa kuka tare da ƙoƙarin fitowa. Ummi ta ce "Ah ah, me ya faru?" Afrah ta ce "Aunty, ni gurin Aunty zani." Cikin rarrashi Ummi ta ce "Ba ga Auntin nan ba ai tare zamu tafi da ita." Amrah ta ce "Ai bata shigo cikin Mota ba." Neehal da k'walla ta tarar mata a ido ta yi murmushi tare da shafa fuskar Afrah ta ce "Kayana zan ɗauko yanzu zan dawo sai mu tafi." Yarinyar ta ce "To zan biki." Ummi ta ce "A'a Afrah ku jira ta, ta dawo." Yaran suka saka kuka dan sun gane wayo ake musu, Neehal ta juya da sauri ta bar wajen hawaye na zuba daga idonta. Ahmad dake tsaye yana kallonsu ya bita da kallo, da sauri kuma ya bi bayanta ya sha gabanta. Ta tsaya ba tare data d'ago kanta ba. Fuskarsa cike da damuwa ganin tana kuka ya ce "I'm sorry na raba ki da yaranki ko?" Ta d'ago ta kalle shi cikin mamakinsa, shi da yaransa amma yana bata haquri. Ya yi mata murmushin nan nasa mai kyau, tare da girgiza mata kai alamun ta daina kukan. Jin kukan su Afrah a kusa da ita yasa ta juya da sauri, ashe fitowa sukai daga cikin motar suka taho gurinta. Ta tsugunna ta rungume su a jikinta, sannan ta d'ago su ta musu kiss a goshinsu tana murmushi. Afrah ta ce "Aunty ki zo mu tafi Please, mu dake zamu tafi." Kafin Neehal ta ce wani abu Ahmad dake tsaye yana kallonsu cikin burgewa ya kama hannun yaran ya ce "Aunty zata ɗauko kayanta ne, mu je Mota mu jira ta." Neehal ta miƙe tare da juyawa da sauri ta d'agawa Zahra hannu sannan ta nufi cikin gidan zuciyarta cike da kewar yaran, bayan tafiyarta ba jimawa su Ahmad suka fice daga gidan suna d'agawa su Mama hannu, sai da suka fice sannan su Mama suka koma cikin gidan.

Neehal ba ta yi kuka sosai ba kamar yadda Mama ta zata, tana komawa ɗakinta ta shiga toilet ta wanke fuskarta, sannan ta sakko ƙasa gurin Aunty A'isha suka sha hira, bayan Sallar Magriba Aunty A'isha ta tafi, tana tafiya ba jimawa Sadik ya zo. Shima ya yi tunanin zai zo ya same ta cikin damuwar rashin su Afrah, amma sai ya tarar da akasin haka, suka sha hirarsu kamar kodayaushe. Washegari da hantsi ta shirya ta je saloon aka yi mata wankin kai, daga nan ta wuce gidan Haneefah kamar yadda ta yi mata alƙawari. Sai Bayan Magriba ta dawo gida, a hakan ma dak'yar Haneefah ta barta ta taho suna ta shan hira. Bayan Sallar isha'i Zahrah ta kira ta a waya, bayan sun gaisa ta musu ya suka je gida ta haɗa ta da su Afrah. Sun daɗe suna wayar suna ta bata labarai, bayan ta sha complain ɗin rashin bin su da bata yi ba..... Ranar Monday ta fara zuwa siwes ɗinta na school, a gidan TV'nsu take yi, hakan yasa abun ya zo mata da sauk'i. Bayan tafiyar su Afrah kullum sai sun yi waya a wayar Zahra, dan yanzu duk abun Ahmad ya haqura ya bar su a gidan Ummi su cigaba da zama anan saboda abun da ya faru. Neehal ta rasa meyasa fuskar Ahmad ta ƙi bacewa daga idanunta, musamman murmushinsa da yay ta kashe ta da su a ranar, kullum sai ta yi imagining ɗinsa a cikin ranta, a gefe guda kuma tana son tuno inda ta san fuskarsa, dan tabbas ta taɓa ganinta a rayuwarta ko da a hoto ne kuwa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.