Neehal Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 51 of 104
A lokacin da aka yi engaged ɗin Neehal aka buɗe gidan Television na ASTV. Wani abokin Daddy ne ya buɗe, hamshaqin mai kuɗi ne kuma sananne ne a ƙasar nan. Da kwalin Deplomer aka ɗauki Neehal aiki a gidan TV'n, Haneefah kuma da S.S.C.E Daddy ya sa aka mata alfarma ita ma aka ɗauke ta. Neehal abun nema ya samu ta zama Jonorlist sai murna. Kafin Neehal ta fara aiki sai da aka kai ruwa rana da Ameen, dan da farko cewa ya yi baza ta yi ba. Mama ta ce, A nan bai isa ba kuwa, wanda zai aure ta ma bai hana ta ba sai shi ɗan karere. Har wannan lokacin dukiyar Neehal tana hannun Uncle Umar yana juya ta, babu wanda ya ce masa k'ala a kanta, su Fauziyya da aka ga Neehal a gidan TV baƙin ciki kamar ya kashe ta, musamman da ta ga yanda ta ƙara kyau ta zama ƴar gayu wanke hannu ka taɓa, gashi ko ta ina samun masoya take rututu a faɗin ƙasar nan.
*CIGABAN LABARI.............âœï¸*
[7/21, 9:03 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*
_By_
_Zeey Kumurya_
*3ï¸âƒ£4ï¸âƒ£*
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*
Washegari bayan an yi sallar asuba, Daddy ya dawo daga masallaci Mama ta sanar masa abun da Aunty Sadiya ta faɗa mata, dan jiya bai dawo da wuri ba shi ya sa bata faɗa masa ba. Zarya yake ta yi a ɗakin baccinsa, Mama kuma tana zaune a gefen gado ta yi tagumi cikin tunanin mafita. A hankali ta ɗago da idanunta da ba su samu isasshen bacci ba a daren jiya saboda fargaba ta dubi Daddy ta ce "Daddy ka zauna mana, ka bar wannan safa da marwar ka zo mu nemi mafita akan wannan al'amarin." Daddy ya sauke numfashi tare da goge gumin da ya kwanta a kan goshinsa ya ce "Al'amarin ne ya girgiza ni ba kaɗan ba Doctor." Mama ta sauke tagumin data rafka bata ce komai ba. Daddy ya zauna a kan bedside locker yana fuskantar Mama ya ce "Zuciyata ta kasa yarda da wannan abun Doctor, ba zan taɓa yarda saboda Daughter ake wannan kisan ba gaskiya." Cikin karaya Mama ta ce "Saboda me zaka ce haka? Kar fa ka manta mahaifan Neehal ma fa kashe su a kai, kuma har yau an kasa gano waɗanda suka yi kisan da kuma dalilin da yasa aka kashe sun. Haka su Jameel suma har yau an kasa gano waɗanda suka kashe su, ai ko aljanu ke kisan nan ya ci ace zuwa yanzu asirinsu ya tonu." Daddy ya ce "Ka da ki yi la'akari da haka, zata iya yiyuwa mahaifan Neehal b'arayi ne suka kashe su ko kuma wani mak'iyin Abbanta, kin san idan mutum ba ya k'aunar ka a shirye yake da ya aikata komai a kanka. Sannan na biyu kuma Jameel, mahaifinsa ɗan siyasa ne abokan hamayya babu abun da baza su iya ba suma a kan mutum, tun lokacin da aka kashe Jameel tunanin da kowa ya yi kenan ciki har da mahaifinsa. Sai kuma Anwar, wanda shi kaɗai ne ma babu wani dalili a rayuwarsa da a yi tunanin zai sa a kashe shi." Mama ta sauke numfashi ta ce "Yanzu dai a takaice kana son ka ƙaryata abun da Sadiya ta faɗa kenan? Ko kuma kana son ka kwantar mun da hankali ne kamar yadda ka saba a kodayaushe idan ka ganni a cikin damuwa? Daddy! Wannan maganar ba fa ƙaramar magana ba ce, ina tsoron abun da Sadiya ta faɗa ya tabbata." Daddy ya ce "Ko kaɗan ba ina nufin na ƙaryata Sadiya ba ne domin akan aikinta take, kuma ban san hujjar data gani ta faɗi haka ba, kawai dai ina son nusar dake wani abu ne." Mama ta ce "Wanne abu zaka nusar da ni? Hmm Daddy kenan, ni fa na riga na gano ka, kawai kana san kwantar mun da hankali akan wannan al'amarin ne." Daddy ya yi shiru domin tabbas abun da Mama ta faɗa haka ne, yana son ya kwantar mata da hankali ne kawai amma tabbas shi ma maganar ta girgiza zuciyarsa ba kaɗan ba, ya manta rabon da ya ji abun da ya firgita zuciyarsa irin wannan. Mama ta ce "Ya Allah ka bayyana mana gaskiyar wannan abun, ka tona asirin duk wanda yake da hannu a cikin wannan al'amari da gaggawa." Daddy ya ce "Ameen ya Allah, abun da ya dace dama mu dage da yi kenan addu'a, Insha Allahu gaskiya zata bayyana." Kusa da Mama Daddy ya dawo ya kama hannunta ganin damuwa ƙarara a fuskarta ya ce "Please Doctor ki rage damuwar nan da kike, kin san Neehal ɗin ma idan ta ganki a haka itama zata shiga damuwar ne, ina jarumtar dana san ki da ita ne? Haba matar soja uwar soja." Mama ta sauke numfashi ta ce "Idan ka ga na daina damuwa to naga na aurar da Neehal, shine kawai hankalina zai kwanta." Daddy ya miƙe ya ce "Insha Allahu zaki gani, ai shi aure hab'o ne idan lokacinta ya yi dole sai ta yi, fata kawai Allah ya kawo mata miji na gari, wanda zai riqe mana ita da amana ko bayan ranmu." Mama ta ce "Ameen ya Allah." Daddy yana buɗe wardrobe ɗinsa ya ce "Yanzu ita Neehal ɗin akwai wanda take kulawa ne?" Mama ta ce "Gaskiya a sani na babu kowa." Daddy ya ce "Wannan yaron da yake zuwa fa wani ɗan fari dogo haka?" Mama ta ce "Sadik kake nufi wai?" Daddy ya ce "Ehh, Barrister ne shi ko?" Mama ta ce "Ehh, a unguwar su A'isha gidansu yake." Daddy ya ce "Allah ya tabbatar mana da Alkhairi." Mama ta ce "Ameen." Car key Daddy ya miƙawa Mama ya ce "Gashi ki ba wa Daughter." Mama ta karb'a cikin mamaki ta ce "Mota ka sai mata?" Daddy ya ce "Ehh mana, alƙawarin dana mata ne tun sanda ta gama Polytechnic kika hana a bata a time ɗin." Mama tana murmushi ta ce "Masha Allah, Allah ya sanya Alkhairi ya tsare, ai yanzu ta ƙara hankali zan bar ta ta yi driving ɗinta. Mun gode sosai fa Allah ya ƙara buɗi mai albarka" Daddy ya ce "Ameen ya Allah. Mama ta miƙe ta ce "Bari in je inwa Daughter albishir, na san zata yi farin ciki sosai." Daddy ya yi murmushi cikin jin daɗin ganin Mama na murmushi, saɓanin d'azu da damuwa ke kwance a kan fuskarta. A duk duniya abun da ke d'aga masa hankali kenan ya ga iyalinsa a cikin damuwa, da yana yanda zai yi da sai ya magance wa Neehal wannan K'ADDARAR data shigo cikin rayuwarta, amma babu yanda zai yi komai rubutacce ne tun fil'azil daga Ubangiji Mai girma da ɗaukaka, amma ya ɗaukar wa kansa alk'awari sai inda ƙarfinsa ya ƙare a game da binkicen wannan al'amari, a matsayinsa na k'wararren soja.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.