Neehal Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 41 of 104
Aunty A'isha tana part ɗinta tana bacci ƙarar harbin ne ya tashe ta, amma ko kaɗan ba ta yi tunanin a cikin gidan ba ne, ta yi tunanin wani gidan custom ne da suke mak'ota b'arayi suka shigar masa. Amma duk da haka sai da ta ji gabanta ya faɗi a lokacin da akai harbin ƙarshe, wayarta ta ɗauka ta kira Numbern Abba amma bai ɗauka ba, jin shiru kusan minti talatin da yin harbin Ba'a kuma ba ta sauke ajiyar zuciya ta koma ta kwanta, amma sai ta nemi bacci a idonta ta rasa, haka kawai ta ji jikinta wani iri, zuciyarta har wani rawa take dan fargaba. Ƙara kiran wayar Abba ta yi amma bai d'aga ba, hakan yasa ta kira Umma itama ba ta ɗauka ba, gashi Uncle Usman ba ya nan ya yi tafiya balle ta kira shi, dan ita ta rasa mai yasa hankalinta ya kasa kwanciya da harbukan da akai. Ranar Aunty A'isha bata iya bacci ba, ga wani irin tsoro da ya rufe ta, wadda ko kwakwkwaran motsi tsoron yi take. Sai da aka shiga Sallar Asuba sannan ta iya tashi ta shiga toilet ta ɗauro alwala ta fito ta tada Sallah, tana idarwa kuwa ta yi part ɗin Umma. Da Sallama ta shiga falon Umma amma ta ji shiru, corridor ta nufa inda ɗakunan Umma guda biyu suke suna facing juna, tun daga bakin ƙofar ta fara hango jini ta ƙasan ƙofar, wani mummunar fad'uwa gabanta ya yi, da gudu ta tura ƙofar ɗakin ta shiga, wata gigitacciyar ƙara ta k'walla ganin Umma da Abba kwance cikin jini, kamar kuma wacce aka tsikara ta fito da gudu ta yi waje tana k'wala wa mai_gadi kira, mai gadi da dawowarsa kenan daga masallaci ya fito da sauri yana tambayar "lafiya Hajiya?" Part ɗin Umma kawai Aunty A'isha take nuna masa amma ta kasa mgn, hakan yasa ya nufi part ɗin da sauri a zatonsa ko wuta ce ta kama a ciki. Gigitar da mai_gadi ya shiga baza ta faɗu ba, ga mamakin ta ya ya aka iya shigowa gidan har aka aiwatar da wannan mummunan aikin, dan shi ko da za shi masallaci ma ƙofar gidan a rufe take shi ya bude ta da hannunsa, kuma gidan baza a iya haurowa ba saboda tsayin katangar gidan. Kuka sosai Aunty A'isha ta shiga yi lokacin da mai_gadi ya sanar mata babu numfashi a tattare da su Umma, tana faɗin "Su waye suka kashe ku? Me kukai musu?" Maigadi kuwa da sauri ya fita ya faɗa wa mak'ota, nan da nan kuwa mazan layin suka fara shiga gidan cikin tashin hankali, dan kuwa duk yawanci sun ji harbin da akai, babu ɓata lokaci custom ɗin dake layin ya kira Police aka sanar musu, kafin gari ya yi haske har sun zo gidan. Aunty A'isha kuwa tuni ta suma, wata makociyarsu ce da ta shigo ta ɗauki ƙaramar wayar Umma ta shiga kiran ƴan'uwanta tana sanar musu, haka ma wayar Abba maigadi ne ya ɗauka ya kira ƴan'uwa da abokan arziki yana sanar musu. Aunty A'isha bayan an shafa mata ruwa ta farfaɗo itama tana kuka ta shiga kiran mutane tana sanar musu wannan mummunan labarin wanda take ganin tamkar al'amara ko kuma mafarki take zata farka. Mutuwar su Abba ta girgiza zuk'atan mutane, kafin ka ce me, labari ya fara baza gari, musamman da matasan unguwar suka yaɗa a social media.
Lokacin da Aunty A'isha ta sanar da Mama rasuwar Umma da Abba kusan zaucewa ta yi ita kaɗai a ɗaki, saboda tsananin kaɗuwa dan mutuwar ta dake ta ba kaɗan ba, wayar da suka yi jiya da daddare kawai take tunawa. Da ƙyar ta samu yar nutsuwa ta fara dawo mata sanadiyyar karanta Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, da ta shiga maimaitawa a fili. Miƙewa ta yi da ƙyar ta fito ta nufi part ɗin Daddy, tana shiga ta tarar da shi yana waya. Sai da ta jira ya gama wayar sannan ta rattabo masa abun da faru, iya rudewa shi ma Daddy ya ruɗe, ba shiri ya yi kira a waya dan a yi musu bucking ɗin jirgi zuwa Kano. Neehal tana kwance a ɗaki Mama ta shigo ta same ta. "Neehal, tashi ki shirya zamu unguwa." Mama ta faɗi haka cikin sanyi da raunin murya. Neehal ta tashi zaune tana duban Mama ta ce "Ina zamu Mama? Ni fa Umma da Abba nake son gani." Ta ƙarashe maganar kamar zata yi kuka, Mama ta daure dan kar Neehal ɗin ta gane wani abu ta ce "Daga can zamu biya gida ki ga su Umman." Neehal ta sauke ajiyar zuciya sannan ta miƙe ta shiga toilet, Mama ta bita da kallo cikin tsananin tausayinta. Tashi ta yi ta fice daga ɗakin da sauri jin kuka na neman kufce mata. Neehal kam cikin sanyin jiki sosai ta fito ta shirya, ta rasa me yasa ta ji bata wata murna duk da Mama ta ce mata za su biya ta ga Su Ummanta. Kafin ƙarfe tara su Mama sun ƙarasa Airport, cikin mintuna aka gama komai suka shiga jirgi suka yo Kano, Neehal sai kallon Ameen take cikin zuciyarta tana mamakin tsakanin kamarsu da Mama, daga gaisuwa babu abun da ya kuma haɗa su, dan shi ko kallonta bai kuma yi ba. Sai dai cikin zuciyarsa cike take taf da tausayin ta, dan Mama ta sanar masa rasuwar Mahaifan nata. Driver'n Abba ne ya je ya ɗauko su lokacin da suka sauka a Kano, Neehal ta yi mamakin hakan amma ba ta ce komai ba. Yanda Neehal ta ruɗe, ta gigice tare da firgicewa ba zai misaltu ba, balle ya faɗu, lokacin da ta yi arba da gawar iyayenta kwance duk jini ya ɓata likkafanunsu, duk da Kasancewar ta yarinya a time ɗin amma tasan mutuwa, ta san shikenan ba zata ƙara ganin Ummanta da Abbanta ba sun tafi kenan, ta yi kuka ta yi kalamai wanda sai da suka karya zuciyar duk wanda yake gurin tare da zubar mata da hawaye, haka ta rungume Aunty A'isha sukai ta kuka abun tausayi. Mama ma duk dauriyarta ranar ta ci Kuka. Saboda tsabagen Kukan da Neehal ta sha kafin dare zazzaɓi mai zafi ya rufe ta, sai da aka mata allura sannan jikin nata ya ɗan yi dama, da safe kam jikin sai ya ƙara rikicewa, sai da ta yi kwana biyu ana saka mata drip tare da allurori sannan ta ji sauƙi. Umma da Abba sun yi jama'a sosai wanda suka raka su gidansu na gaskiya, dan Abba mutumin k'warai ne, kowa sai faɗar Alkhairinsa yake, haka ma Umma, gashi kuma sun yi sa'ar dace wa da Ranar Juma'a. Tun daga Ranar da akai kisan jami'an tsaro suka duk'ufa da binkice dan gano waɗanda suka yi nisan, dan har mai_gadi sun kama a tunaninsu ko da haɗin bakinsa, amma daga baya sun sake sa da suka gane babu haɗin bakinsa a kisan, ta ƙofar baya ma waɗanda suka yi kisan suka shigo gidan. Bayan sadakar bakwai kowa ya watse gida ya rage daga Neehal sai Aunty A'isha da hajiyarsu da Yayar Abba. Nan fa mutuwar ta dawowa da su Aunty A'isha da Neehal sabuwa, sai ya kasance Kullum sai sun yi kuka. Nasiha sosai Hajiya da Yayar Abba suke musu akan su yi haquri, dama duk mai rai mamaci ne, kowa jiran mutuwarsa yake fata dai kawai Allah yasa mu cika da kyau imani. Uncle Umar da Uncle Usman ma mutuwar ta dake su ba kaɗan ba, dan suma kuka wurjanjan suka dinga yi. Aunty A'isha kullum tunaninta su waye suka kashe su Umma, kuma akan wanne dalili? Dan a binkicen da akai ya nuna wanda suka yi kisan ba b'arayi ba ne turo su akai, dan babu abunda suka ɗauka a gidan. Kafin a yi arba'in Yayar Abba ta koma Gabasawa, sai Hajiya ce kaɗai take zaune da su Neehal. Kusan kullum suna waya da Mama da Daddy, Mama ta ƙara zuwa sau ɗaya ta duba su. Sosai Ubangidan Abba ya sa aka tsananta bincike dan gano wandanda suka yi kisan su Abba, amma shiru babu wani information, duk da jami'an tsaron na iya bakin ƙoƙarinsu a binkicen.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.