Complete Hausa Novels

Neehal Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 42 of 104

Washegarin Arba'in Uncle Umar ya zo da wata magana wadda ta gigita Su Aunty A'isha ta kuma ba su mamaki, ya zo ya same su suna zaune da Mama, da Yayar Abba da Aunty Sadiya, da Ammi matar Uncle Mahmud wanda duk sun zo ne saboda sadakar Arba'in su Umma. Maganar da ya musu kuwa itace akan rabon gado, wai nan da kwana uku insha Allah za su zo da Alk'ali a raba a bawa kowa nasa. Kuka Aunty A'isha ta saka tana faɗin "Ita bata son wani gado, dan ta riga ta yi rashin da har abada ba zata mai da kamarsa ba, rashin adalin mijinta da kuma Abokiyar zamanta salihar mace." Hajiya da Yayar Abba suka ce "Haba saurin me ake, ya bari Aunty A'isha ta fita daga takaba mana." Amma ya ƙi, wai hakan shine dai_dai. Uncle Usman kuwa k'ala bai ce ba akan maganar ba. Maganar fa ta girmama har gurin manya, dole ba son ran su Aunty A'isha ba aka raba gadon. Kasancewar Neehal ita kaɗai ce 'yarsu Abba ya sa a cikin kadarorin Umma da Abba ya mallaka mata kafin ya rasu sai da aka raba da su Uncle Umar, haka ma na Abba sai da aka raba da Yayarsa. Aunty A'isha ma aka bata tumunin takabarta. Gidan da suke ciki a gadon Neehal ya zo. Sai dai kuma wata sabuwa batun riƙon Neehal, da farko Yayar Abba ta so tafiya da ita Gabasawa amma akace hakan ba zai yiyu ba saboda ƙauye ne, ga kuma karatun Neehal ɗin, idan ta koma Gabasawa zata tawaya. Ƴan'uwan Abba kuwa da suke cikin Kano kowa ƙin ɗaukar ta ya yi, a ganinsu wahala zata zamar musu. Aunty A'isha kuwa tun farko ita ta ce a bata Neehal ɗin zata cigaba da riƙon ta, amma Uncle Umar yay ruwa yay tsaki ya ce ba za su ba da Neehal ga bare ba, tunda ba rasa dangin da za su rike ta ta yi ba, dan haka shi zai ɗauke ta. Ai Neehal na jin haka ta dinga kuka tana faɗin Ita "Gurin Aunty'nta zata zauna, babu inda zata je." Amma Uncle Umar ya sawa idonsa toka, ya ce "Ko kukan jini za ta yi wallahi a gidansa zata zauna, shi zai cigaba da riƙon ta." Aunty A'isha dama ba wani shiri take da shi ba, ta san ko zata mutu tana roƙon sa ya bata Neehal ba zai bata ba, kuma babu yanda zata yi da shi tunda ɗan'uwan mahaifiyarta ne, yafi ta kusanci da Neehal ɗin. Neehal tana ji tana gani Aunty A'isha suka haɗa kayansu ita da Hajiya suka wuce Gombe, tana kuka Aunty A'isha na yi, mutuwar Abba da Umma ta dawo musu sabuwa, duk mai imani idan ya gansu a wannan lokacin yanda suka rungume juna suna kuka mai ban tausayi sai ya zubar musu da k'walla, amma Uncle Umar ko ajikinsa, Neehal har shid'ewa take saboda kuka. A ranar da suka tafin da daddare yasa ta itama ta haɗa kayanta kaf ya tasa ƙeyarta suka tafi gidansa tana ta faman tsiyayar hawaye, dan ya mata tsawa akan kar ya ƙara jin kukanta............✍️
[7/21, 9:02 AM] Zee data: *⚡NEEHAL⚡*

_By_
_Zeey Kumurya_

*2️⃣8️⃣*

Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*

A falon gidan suka tarar da matarsa Aunty Fauziyya hakimce akan kujera suna kallo, yaranta guda biyu mace da Namiji suna ta wasansu a kan doguwar kujera. A hankali Neehal ta shiga Falon tana goge hawayen fuskarta dan kar Uncle Umar ya gani, kan kujera ta nufa zata zauna Aunty Fauziyya ta buga mata wata uwar tsawa tana faɗin "Kar ki kuskura ki zauna mun akan kujera zauna nan ƙasa." Ba musu Neehal ta zauna a ƙasan cikin mamaki, dan ta saba ita a gidansu da gidan Mama akan kujera take zama. Uncle Umar ya zauna yana hararar Neehal ya ce "Hmmmm, yarinyar nan ai sai an dage mata, gaba-d'aya waccan matar da Ƴan'uwanta sun ɓata mata tarbiyya, Ni wlh Yaaya ta ban mamaki da ta yarda suke riƙe mata ƴa." Fauziyya ta tab'e baki ta ce "Kai kwa kuɗii, kuɗi fa aka ce maka, ta ga suna da kuɗi ne shi yasa, ka ga in an ɗan yi Zakka a dinga tunawa da ita ai." Shiru Uncle Umar ya yi jin abun ya fara komawa cin fuska. Yaran su Aiman da iman suna wasa suka fado tim akan Neehal, Uncle Umar ya ce "Subahanallah, Aiman ban hana ku wasan banza ba? gashi nan kun faɗo wa Aunty'nku akai." Aunty Fauziyya dake ta aika wa Neehal harara ta ce "Kamar ya sun faɗo mata? Ita bata gani ne, makauniya ce ita, ai tana kallonsu zasu faɗo ɗin dan baƙin hali ta ƙi matsawa, salon ace daga zuwanta an fara cutar da ita." Neehal dai ba ta ce komai ba, kanta na ƙasa tana ta hawaye. Su Aiman suka kwantar da trolley ɗinta suka buɗe suka fara zak'ulo mata kaya suna yar wa a dakin, Uncle Umar cikin tsawa ya ce musu "Wai wanne iskanci haka, ko kun mata ajiya a cikin kaya ne.?" Cikin tarar numfashi Aunty Fauziyya ta ce "Ka ga, ka dena dakawa ƴaƴana tsawa irin haka, nan gidan ubansu ne ba cin arziki suka zo ba, dan haka dole su sakata su wala san ransu." Tsaki Uncle Umar yay ya ce wa Neehal ta tashi ta tattara kayanta ta shiga ɗakin yaran. Aunty Fauziyya ta ce "Kar kuma ki hau mun kan katifar ƴaƴa, a ƙasa zaki zauna, anan kuma zaki dinga kwana." Neehal dai ba ta ce komai ba ta tashi ta shiga ɗakin tana janye da trolley ɗinta da ƙyar. A ƙasan ta zauna kamar yadda Fauziyya ta ce ta rafka tagumi, kanta ne ke mata wani irin ciwo hakan yasa ta kwanta a ƙasan, amma gaba-d'aya sai ta ji kwanciyar bata mata daɗi ba, ita da ta saba kwana akan luntsumemiyar katifa da lallausan bedsheet ta lullub'a da lallausan bargo, ta yaya zata iya kwanciya akan dandaryar 
ƙasa? A hankali ta miƙe dak'yar ta buɗe trolley ɗinta ta ɗauko kayanta ta shimfid'a a ƙasan ta kwanta akai, amma duk da haka bata wani ji daɗin kwanciyar ba, ya dai fi ta kwanta a ƙasan ne kawai. Allah ya so ma Aunty A'isha ta saka mata bargo acikin kayan nata, da yake ita ta haɗa mata kayan. Amma saboda garin da ɗan zafi shi yasa bata lullub'a ba, ɗakin kuma da fanka amma bata wani ba da iska, ko dan ta saba da Ac ne a gida. Tafi awa da kwanciya amma ta kasa bacci sai juyi take, idanunta dai a lumshe suke kamar mai bacci, tana jin Aunty Fauziyya ta shigo ta kwantar da ƴaƴanta akan katifa ta daura musu Net sannan ta kashe musu light ɗin ɗakin, nan fa sauro ganin duhu ya cewa Neehal salamu alaikum, ita kuwa bata saba da sauro ba, nan da nan ya gigita ta, ta tashi zaune tana hawaye, ga ciwon kai tamkar ana ƙara mata ake, lallaɓawa ta yi ta shige Net ɗin su Aiman dan bata da wata mafita, katifar ma zata ishe su amma ɗan baƙin halin Aunty Fauziyya ta hanata kwanciya akai. Tana shiga ta sauke ajiyar zuciya, ba jimawa baccin wahala ya kwashe ta. Sanyin asuba ne ya tashe ta, cizon sauron da tasha jiya da kukan da tay ya haifar mata da zazzaɓi, cikin rawar ɗari ta sauko daga kan katifar ta dunk'ule a waje ɗaya tana numfarfashi, kayanta data shimfid'a a ƙasa ta rarumo ta rufe jikinta saboda sanyin da take ji. Sai wajen ƙarfe 7 su Iman suka tashi daga bacci, kamar wasu ƴaƴan karnuka da faɗa suka tashi, ga shi sun tsutstsula fitsarinsu a kwance, Allah ya taimaki Neehal ba su ɓata ta ba. Da ƙyar Neehal ta iya tashi ta ƙarasa toilet ɗin dake ɗakin ta yi fitsarin da ya matse ta, da ƙyar take tafiya saboda jiri, ga yunwa dake nuk'urk'usar hanjin cikinta, rabonta da abincin tun lunch ɗin jiya da ta yi a gida.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.