Neehal Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 17 of 104
Washegari da yamma Neehal ta zo gidansu Haneefah suna zaune a d'akin Haneefah Neehal ta dubi Haneefah ta ce "Besty ban baki labari ba." Haneefah ta ce "Labarin me?" Neehal ta ce "Yayanah ya kusa aure." Haneefah ta waro ido waje ta ce "Wow, nice story, ki ce su Aunty Hamida an kusa shiga daga ciki.?" Neehal ta ce "Hmmm, na yi farin ciki sosai da Yaya zai yi aure, sai dai kuma har na fara kewar shi." Haneefah ta ce "Iskancin banza, abun da ba kullum ki ke ganin sa ba da ma." Neehal ta ce "Duk da haka." Haneefah ta ce "Sai ki bi shi gidan nashi, dama ba kwa shiri da Aunty Hamida sai ku yi ta fafatawa." Neehal ta ce "Ke ba fa ita zai aura ba." "Kamarya. Haneefah ta tambaya cikin mamaki. "Kamar yadda Allah ya yi, wata tsohuwar budurwarsa zai aura, Hafsat." Neehal ta bata amsa da faɗin haka. Haneefah ta jinjina kai ta ce "Allah sarki Aunty Hamida ta bani tausayi wlh, yanda take son Yaya ban taɓa tunanin ba ita zai aura ba." Neehal ta ce "Nima haka Besty, na yi mamaki, Mama ma duk ta damu." Haneefah ta ce "Allah ya sanya Alkhairi ya kai mu da rai da lafiya mu sha shagali." Neehal ta ce "Amin dai." Haneefah ta numfasa ta ce "Dama a haɗa a muku auren tare da Yaya." Neehal ta mata wani kallo ta ce "Sai dai a haɗa dake, dama na ji Mama ta na cewa Month d'in bikin da za a sa kamar ɗaya da naki." Haneefah ta ce "Sai a haɗa mu duka a mana tare." Neehal ta tab'e baki ta ce "Ke nifa na cire wani zancen aure a tsarina, karatuna kawai zan yi ta yi." Haneefah ta ce "Zance ma ki ke, idan ke kin yarda kin zauna ai Mama ba za ta yarda ki zaunar mata ba aure ba." Neehal ta ce "To za ta mun aure ba miji ne? Ina dai sai na kawo mata mijin?" Haneefah ta ce "Ai miji ba zai miki wahalar samu ba, duk tarin masoyan da ki ke da su." Neehal ta ce "Kan ki ake ji, ni dai na riga na hak'ura da wata maganar soyayya a rayuwata balle kuma har na kai ga aure." Haneefah ganin yanda Neehal take magana bil hak'k'i, ya sa ta saki baki kawai ta na kallon ikon Allah, amma ta mata uzuri, domin ta san har yanzu Anwar ya na nan a cikin ranta, shi ya sa take ganin kamar ba za ta iya ƙara tarayya da wani ɗa Namijin ba.....
*********** *ABUJA* ***********
Mommy'n Hameedah ce tsaye a falonta ta na zarya cikin tsananin ɓacin rai da damuwa. K'awarta mai suna Haj. Saratu dake zaune a falon ta dube ta da mamaki ta ce "Wai Suwaiba lafiya kuwa, na ga kin fito daga d'aki kin hau zarga-zurga kamar wata me fareti?" Mommy ta ja wani dogon numfashi ta sauke cikin tsantsar ɓacin rai ta ce "Ina fa Lafiya Saratu, waccan munafukar matar 'yar abu ta kazar uba ta shirya makircin da ta saba." Haj. Saratu ta ce "Wake nan.? Mommy ta ƙaraso kujerar da Haj. Saratu take ta zauna a gefenta, cikin ɗacin rai ta fara magana. "Yanzu nan Yayana na Kano ya kira ni, ya ce mun za mu yi wata magana, na tattara hankalina duka na bashi dan na ɗauka wata maganar arzik'in ce, buɗar bakinsa sai ce mun yayi. Suwaiba! Magana za mu yi a kan yaran nan Ameen da Hameedah. Na gyara zama cikin jin daɗi na ɗauka zai ce mun za a yi maganar bikin su ne, amma sai na tsinkayi muryarsa da faɗin akasin haka, wai ya kira Ameen ya masa maganar Aure ya ce ya fitar da mata, shine Ameen ɗin ya ce ba ya son Hameedan wata yake so, yanzu maganar da yake mun har sun je gidan su yarinyar an yi magana, next week za su kai kuɗi a yi Engagement ɗinsu haɗe da sa rana." Wani uban ashar Hajiya saratu ta narka ta ƙara da faɗin "Eh, lallai kam dole ki ce makira ta yi markici, dan wannan ko tantama ba na yi shirin wannan Matar tasa ne, me ji da kanta kamar tafi kowa." Mommy ta ce "Ai dama ni na san za a rina, domin matar nan ba ta k'auna ta da ni da ƴaƴana, amma wlh wannan karon ba ta isa ba, zan nuna mata asalina za ta san ko wacece Suwaiba, shima Yayan dan takaici kashe wayata na yi, ya tsaya ya na mun wata nasiha wai matar mutum kabarinsa, komai na Allah ne, Ni ko gama saurararsa ma ban yi ba." Haj. Saratu ta ce "To yanzu mene abin yi?" Mommy ta ce "Ni na san me zan yi, dan idan kinga ba a yi auran Ameen da Hameedah ba to wlh sai dai in ba na numfashi. Amma kafin na yi abin da zan yi bari na fara kiran ita makirar na ci mata mutunci." Mommy ta ƙarashe Zance tare da mik'ewa ta shiga d'akinta ta ɗauko wayarta, jikinta har tsuma yake ta nemo number'n Mama ta danna mata kira. Mama ta na asibiti ta na ƙoƙarin tafiya gida ma tunda yamma ta yi kiran Mommy ya shigo wayarta. Ba tare da tunanin komai ba ta ɗauka, dan ita ba ta masan Dad ya kira Mommy'n ya mata maganar ba.
"To makira, munafuka Algunguma, wato kin yi halin naki da ki ka saba kin hana ɗanki Auren 'yata, dan nasan Ameen haka kawai ba zai ce ba ya son Hameedan ba, wa ya sani ma ko hadda siddabarunku na Fulani ki ka haɗa masa saboda ya ƙi amincewa." Kalaman da Mama ta ji kenan lokacin da ta kai wayar kunnenta, wani ɗan guntun murmushi ta yi, cikin maganarta mai cike da aji da nutsuwa ta ce "Na isa ne ai Suwaiba na hana Ameen abu kuma ya hanu, dan haka ki yi duk abin da za ki yi a kan hakan." Kamar mahaukaciya Mommy ta ce "Wlh kuwa za ki ga abun da zan yi, za ki san da ni Suwaiba ki ke maganar." Ta ƙarashe zancen ta na bubbuga k'irjinta. Mama ta yi tsaki ta na ƙoƙarin cire wayar daga kunnenta ta ji Mommy na faɗin. "Kuma nasan duk saboda me ki kai haka, dan tun ba yau ba na fuskanci wannan figaggiyar yarinyar da danginta suka kasa riƙe ta ki ke son bawa Ameen." Mama harda za ta bata amsa sai kuma ta kashe wayarta, domin ba ta da time ɗin Mommy'n. Mommy kuwa jin Mama ta katse wayar hakan ya ƙara k'ular da ita, ta yi ta masifa da d'uran_d'uran ashariya kamar sabuwar kamu. Haj. Saratu na ƙara zugata.
Daf da Magriba Hameedah ta dawo gidan daga gurin aiki a matuƙar gajiye kamar wadda ta yi aikin ƙarfi. Jakarta da mayafinta ta cillar a kan kujera sannan ta zauna tare da faɗin "Wash, Mommy na gaji." A dak'ile Mommy ta ce "Sannu" Hameedah ta kalli mahaifiyarta ta, yanayin da ta mata magana ta gane ba k'alau ba, da mamaki ta ce "Mommy what happened na ga kamar ranki a ɓace?" Mommy ta ce "Akwai matsala ne Daughter babba ma kuwa." A ɗan firgice Hameedah ta ce "Me ya faru Mommy? Har kin sa hankali na ya fara tashi." Mommy ta ce "Hmmm, bari kawai Hameedah, ni da waccan matar ne Fateema matar Yaya......." Labarin duk abun da ya faru Mommy ta faɗawa Hameedah. Wani irin ihu Hameedah ta yi tare da mik'ewa tsaye cikin tashin hankali ta ce. "Wallahi Momy ba zai yiyu ba, shekara nawa ina zaman jiran shi sai yanzu a ce ba ni ze Aura ba." Ta ƙarashe zancen tare da fashewa da kuka. Mommy ta taso ta zo kusa Hameedah, dafa kafadunta ta yi cikin lallami ta ce "Share hawayenki Daughter, indai Ina raye babu abun da zai hana auranki da Ameen, ki kwantar da hankalinki." Cikin kuka Hameedah ta ce "Mommy Dan Allah ki san abun yi, wlh ba zan iya rayuwa babu Ya Ameen ba" Mommy ta zaunar da ita a kan kujera ta ce "Ki kwantar da hankali kamar tsumma a cikin ruwa, ki sa a ranki ma auranku da Ameen tamkar an yi angama."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.