Neehal Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Neehal_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 79 of 104
Ahmad ta fara kira saboda missed call ɗinsa ya fi yawa. Kamar jira yake ringing ɗaya ya yi rejected ya kira ta. Ta d'aga tare da yi masa sallama. Ya amsa tare da faɗin "Princess!" cikin sauke ajiyar zuciya da jan numfashi. Ta ce "Na'am Uncle, ina yini?" Ya ce "lafiya lau, jikin naki ne har yanzu?" Ya yi maganar cikin damuwa. Ta ce "Na ji sauƙi Uncle." Ya ce "Um,um Princess, sound ɗin muryarki ya tabbatar mun da baki da lafiya har yanzu, ko jikin ne ma nay ta kira baki pick ba." Ta ce "Ciwon kai ne, kuma na sha magani, time ɗin da ka kira ni kuma bacci nake." Ya ce "Oh God! Allah ya baki lafiya Princess sannu kin ji." Ta ce "Amin na gode Uncle, ina twins ɗina?" Ya ce "Suna nan k'alau, suna ta missing Auntinsu, da a cikin week ɗin nan zan kawo miki su, to kuma baki da lafiya, sai kin warke zan kawo su." Ta ce "Dan bani da lafiya baza ka kawo mun su ba." Ya ce "Eh mana, kar su zo su damar min ke." Cikin shagwab'a ta ce "Ni dai na warke, ka kawo mun su." Ya ce "Shikenan Princess zan kawo miki su, suna dawowa daga gidan Ammi, sun je can zasu kwanar mata biyu ne." Neehal ta yi murmushi cikin murna ta ce "Thank you." Ya ce "Uhm, ni fa na gane kin fi son yaranki da ni, da ni na ce zan zo baza ki yi wannan murnar ba." Ta yi murmushi mai sauti bata ce komai ba. Ya ce "Insha Allahu, inna samu chance gobe zan zo na ƙara duba jikinki." Ta ce "Uncle, Jiya fa ka zo, ka yi zamanka Please na ji sauƙi fa." Ya ce "In bakya son gani na ni ina son ganinki." Ta ce "I'm sorry ba haka nake nufi ba Uncle, na ga kana ta wahala...." Ya katse ta da faɗin "Babu wata wahala a zuwa ganin ki Princess, don't worry kin ji." Ta ce "Toh Shikenan Allah ya kawo ka lafiya." Ya ce "Ameen, sai ma in duba jikin naki da kaina in ga me yake damar mun ke haka." Ta ce "Kafin ma ka zo na warke In sha Allah." Ya ce "Allah ya amsa Princess." Daga haka suka yi sallama ya ce bari ya barta ta huta tunda bata jin daɗi. Bayan ya katse kiran ta kira Sadik amma bai ɗauka ba, ta san dama by now yana gurin aiki. Uncle Usman ta kira, yay mata ya jiki da nuna jin daɗin sa akan hukuncin da kotu ta yanke akan su Bilyaminu, dan sun yi waya da Uncle Umar ya sanar masa da komai. Bayan sun gama wayar da shi ta bibbi bayan sauran missed calls ɗin da akay mata.
Bayan Sallar Magriba Haneefah suka zo gidan ita da Mijinta Faruq, ta Æ™ara kyau abinta kana ganinta ka ga amarya. Mama ta tarbe ta cikin mamakin ganin ta tana faÉ—in "Yau Amarya ce a gidan namu?" Haneefah tana murmushi ta ce "Ni ce Mama, dama ina so in zo muku sallama jibi zamu wuce Kogi, ga kuma rashin lafiyar Besty, shine na ce mu zo yanzu kawai na duba jikin nata." Mama ta ce "Har tafiyar ta zo? Sai yaushe kuma zaku dawo?" Haneefah ta ce "Sai week É—in da za'ai resuming School." Mama ta ce "To Allah ya kiyaye hanya, ki hau sama tana É—akinta." Ta amsa sannan ta wuce upstairs. Tana kwance rigingine tana latsa waya Haneefah ta shigo É—akin da sallama. Ta d'ago kanta da sauri ido waje ta ce "Amarya!" Haneefah ta ce "Na'am Ango." Neehal ta tashi zaune tana murmushi ta ce "Welcome dear." Haneefah ta zauna a bakin gado kusa da ita ta ce "Yawwa ya jikin naki? Gaskiya kina jin jiki Besty duk kin rame." Neehal ta ce "Da sauqi, ai na yi kyan gani ma yanzu." Haneefah ta ce "Sannu, Allah ya Æ™ara sauÆ™i yasa kaffara ne." Ta ce "Amin Æ™awata, ina Yah Faruq?" Haneefah ta ce "Yana cikin Mota, tare muka zo." Neehal ta ce "Shine kuma kika bar shi a waje, ki ce ya shigo mana." Ta É—auko wayarta a jaka ta kira shi ta ce ya shigo ciki. Neehal ta ce "Ko ke fa, ya amarci?" Haneefah ta ce "Mu sauka Æ™asa ki tambayi Ya Faruq zai baki amsa." Neehal ta yi murmushi. Sun É—an taÉ“a hira Haneefah ta sanar mata tafiyarsu Kogi, Neehal ta musu fatan sauka lafiya. Sannan suka sauka Æ™asa inda suka tarar da Ya Faruq da Mama suna hira. Haneefah ta É—auki juice É—in dake gaban Ya Faruq tana duban Mama cikin zolayarta ta ce "Mama shi ne ni ba'a kawo mun ba sai shi?" Mama ta ce "ÆŠana kawai na sani, ke ai gidan ba baÆ™on ki ba ne." Haneefah ta ce "Allah sarki ni Mama ta daina yina yanzu." Faruq ya yi murmushi tare da yiwa Haneefah gwalo a fakaice. Sannan ya dubi Neehal suka gaisa yay wa Neehal ya jiki yana tsokanarta gawa ta Æ™i rami. Ana kiran sallar isha'i suka tafi saboda daga nan gidan iyayen Faruq za su biya. Bayan fitarsu Mama ta zubowa Neehal abinci ta tilasta mata ta ci, tunda ta ji sauÆ™i har tana iya surutu abincin ma zata iya ci. Tana tutturo baki ta fara cin abincin kamar bata so, kaÉ—an_kaÉ—an take tsakurar sa tana kaiwa baki kamar mai irgawa, gashi Mama ta ce sai ta cinye wanda ta zubo mata duka. Tana zaune ita kaÉ—ai a falo fiye da mintuna ashirin akan abincin da ba wani yawa ne da shi ba, Ameen da Hajiya suka shigo Falon. Hajiya ta ce "Ke kaÉ—ai ina FaÉ—iman? ta bar ki ke kaÉ—ai kuma ke da ba lafiya ba" Ciki_ciki ta ce "Tana sama." Hajiya ta ce "To ya jikin naki?" Ta ce "Da sauqi." Hajiya ta ce "Ke gashi kin warware, ita kuwa waccan da na je dubowa tunda na je tana nad'e akan gado, sai masu aiki ne ke ta kai kawo." Neehal ta saci kallon Ameen wanda ya zauna akan kujera yana kallon Hajiya. Ta mayar da duban ta ga Hajiyan ta ce "To ai bata da lafiya ne." Hajiya ta ce "Duk da rashin lafiyar, amma kuma da rakin tsiya ma, sai langwab'ewa take kamar lagwani." Neehal ta ce "Dan ciwon ba'a jikin yake ba dole ki ce haka." Hajiya ta wuce sama bata tanka ba. Ameen ya tashi ya koma hannun kujerar da Neehal take kai ba tabo ba fallasa ya ce "How was your body?" Kanta a Æ™asa ta ce "Alhamdulillah." Ya ce "Na ga kin ji sauqi har da magana haka." Ta ce "Ya jikin Aunty Hafsat?" Ya ce "Da sauqi." Ta ce "Allah ya Æ™ara sauÆ™i, ka yi mata sannu." Idansa akan abincin da take ta juyawa da spoon ya ce "Zata ji." Suka yi shiru dukan su, ita bata cigaba da jin abincin ba, shi kuma ya zuba mata ido. A hankali ta ji ya ce "Ki ajiye abincin mana idan kin k'oshi." Ta É“ata fuska cikin shagwab'a ta ce "Mama ta ce dole sai na cinye, kuma da Æ™yar nake ci bakina babu daÉ—i." Sai kuma ta kalli fuskarsa iya gaskiyarta ta ce "Yaya ka cinye sauran Please kafin ta sauko." Ya ce "Uhm, jagwalgwalon naki zan ci?" Ta kalli abincin dan ita bata ga wani jagwalgwalawa da ta yi ba, ta turo baki ta ce "Taimakona fa zaka yi Please." Ya yi wani É—an murmushi ya ce "Sai dai in zaki bani a baki." Ta kalle shi da sauri ta ga fuskarsa babu alamun wasa ya sha mur, kamar bashi ya gama maganar yanzu ba." Ta yi shiru ta rasa me zata ce, shi kuma ya tab'e baki irin zaÉ“i ya rage natan nan." Jin taku ta d'aga kai ta kalli steps, ganin Mama ce ke saukowa sai ta É—ibi abincin ta kai baki tana yamutsa fuska kamar mai cin kashi. Mama ta dube ta bayan ta Æ™araso cikin falon ta ce "Tashi ki kai kitchen ki rufe, cin É—an wannan abincin fiye da 30 minutes kamar mai cin gandar da bata gama dahuwa ba." Ta miÆ™e da sauri ta nufi kitchen É—in. Ameen ya raka ta da ido. Mama ta ce masa "Ya jikin Hafsan?" Ya ce "Da sauqi." Ta ce "Allah ya Æ™ara sauÆ™i, da safe Insha Allahu zamu zo ni da Dad mu duba jikin nata." Ya ce "Allah ya kai mu." Daga haka ya miÆ™e yay mata sallama ya tafi. Bayan Neehal ta yi Sallah suka yi waya da Sadik, sannan ta kwanta. Kafin ta kai ga yin baccin Mama ta shigo ta yi mata allura wanda da Æ™yar ta bari aka yi dan bata son allura ko kaÉ—an, gwara ta sha magani duk da shi ma ba wani son shi take ba, amma duk da gwara shi sau dubu akan allurar. Tana cikin rakinta da shagwab'arta bacci ya yi awon gaba da ita.........âœï¸
[7/21, 9:32 AM] Zee data: *âš¡ NEEHALâš¡*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.