Tmw Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: TMW BOOK 3.txt
Chapter 1 of 86
*TMWBK301*
*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*
https://chat.whatsapp.com/IhAz8h8nRy250ZnGGXwM65
*LAME NIG!*
*KASAITATTUN MATA MUN GAISHE KU*.
*AISHA LAME TA KAWO MUKU DUKKAN NAU'IN KAYAN KWALLIYA*.
*KUNSAN GWANAACE WAJEN BAWA FATA HAKKIN TA*
*KUN TUNA KYUAN FATAR GUDUYO KO?*
*KUN TUNA DAI YADDA BULKACHUWA KE SIYAWA YABI KAYAN KWALLIYA NA ORIFLAME KO?*
*TO KEMA GARZAYO KI ZABI NA KI, KO TA ZABA MIKI WANDA ZAI FI DACEWA DA FATARKI*.
*BA IYA KAYAN ORIFLAME BA KAD'AI.*
*TANA DA PRODUCTS DABAN DABAN MASU KYAU, MASU MASTAKAITAN FARASHI*.
*KU TUNTUBE JIKAR DADAR MARINA A WANNAN LAMBAR 07036662633*.
*ADO DA KAMSHI NE SIRRIN GAYU*
Ina tafe ina hard'ewa kamar zan Fad'i saboda sauri da waige waige, burina kawai na yi nisa da gidansu Assadiq kafin abunda na ke gudu ya faru dani.
Ni dai a sanina babu wanda yaga fita ta sannan har na fara nisa ban ji takun wani na bin bayana ba.
Har na cire mayafina a saman fuskana na saki jiki na fara tafiya ina Duba abun hawan da zan samu ya kaini tasha.
Kamar daga sama naji an kira sunana da karfi
"HASIYA..!"
Gabana ya fad'i ras! Jikina ya fara rawa na kasa juyawa Saboda Tsabar Rude'wan da na yi sai naji kamar Muryan Assadiq.
Tahir bai jira sai Hasiya ta juyo ba ya taka ya sha gabanta, cikin mamaki na Dago ina kallonsa da sakin baki da mamakin me yasa ya Biyo ni?
Kuma daman yaga Lokacin da na fita ne? Sai wata zuciyar ta ce min kila Assadiq ne yaga fitar ki ya kuma aikosa wajen ki.
Sai naji na samu yar salama kad'an sai dai Lokaci d'aya in ka kalleni zaka san ina cikin yanayin Tsoro da Firgici.
Daga sama har kasa ya ke kallona Cikin kallon kaskanci da wulakanci.
Sai na sha jinin jikina na maida kaina kasa ina rawan baki na kasa mgana.
Cikin kaushin Murya Tahir yace"Ki gayamin gaskiya shin da gaske ne har yanzu akwai aure tsskanin ki da Sadiq?
Gabana ya kara bugawa Dam! Da Sauri na Dago ina kallonsa cikin mamakin kalamansa, kara had'e rai ya yi ya na kara kaurara Muryansa yace"Ki gayamin gaskiya in kina so ki Tsira da mutumcinki, in kuma kika yi min karya sai kin raina kanki wlh."
Jikina ya fara rawa na fara kokarin ja da baya, da ya ke yadda muke Tsaye ba wanda zai fahimci wani abu za'a yi Tunanin ya Tsaidani muna magana ne.
Na rasa me zan ce masa Tunda Assadiq bai bani wannan Hurumin ba, Sannan bazan so na zama mai Tona masa asirin da Allah ya Rufa masa ba gwara na bari in za'a ji komai a ji a bakinsa, kila ma zamana da Assadiq ya zo karshe in na fad'i abunda ke Tsakaninmu zai zo ya lalata komai tunda a kalaman Abokinsa na Fahimci shima ya yi Tunanin Assadiq ya sake ni Tuntuni.
Ina cikin wannan Tunanin naji ya Dakamin Tsawa ya na kara fad'in"Kina batamin Lokaci malama ki fad'amin gaskiya ki yi tafiyarki cikin salama in kuma ba haka ba? Umh!"
Ya fad'a ya na wani Cije baki, ganin haka yasa idanuwana suka kawo kwallah cikin rawan baki da na gabban jiki nace"Ba ba. Ba komai a tsakanina da shi."
Kallon da naga ya na yi min ne yasa na kwaso rantsuwa ina fad'in"Wallahi gaskiya na.."
"Karya ki ke fad'amin ba gaskiya ba ne malama."
Kalamansa suka katseni ai sai na yi shuru ina raba idanuwana kamar wacce ta yi karya, duk da daman karyan na yi sai kokarin Danne kukan da ke tasomin na ke yi Kada kukana yasa jama'a su fahimci wani abu su taru faruwar haka kuma daidai ya ke da lalacewar komai a wajena ni Hasiya.
Tabbas yasan karya ta ke yi, domin Sadiq bazai taba gayamasa abunda ba gaskiya ba ne, tunda ya furta yasan akwai wani abu a kasa.
Cikin Daga murya yace"Sadiq ya fad'amin komai akan cewa har yanzu ke matarsa ce, kinga kenan karon Farko kin yi min karya kuma sai da na gargad'eki a kan haka."
Ya fad'a ya na nuna ni da yatsa da Sauri na had'a Hannayena waje d'aya ina fadin"Don Allah ka yi hakuri ka Rufamin asiri ka barni na yi tafiyata."
Da Sauri yace"Zaki tafi yanzu ammh sai kin fad'amin wa ya kawo ki gidan nan? Ki ka kara gayamin karya wannan karon bazan Daga miki kafa ba."
Da Sauri nace"Eh Saliha ce, Saliha ce kawata ita ta gayyaceni."
Cikin mamaki ya ke kallona kafin yace"Saliha? Ta ina?
Cikin Rawan baki nace"Saliha yayar Assadiq wacce ke aure a garin Ibadan"
Cikin Dage gira yace"I see garin ya ya? A ina kuka san juna?
Ina goge hanci na fara bashi Labarin farkon had'uwata da Saliha da kuma Dangin Assadiq a kaduna.
Cikin mamaki yace"Ke yar'uwan mijin Salima ne?
Sai na gyad'a masa kai da Sauri ina goge kwallar da kawo cikin Idanuwana.
Cikin mirmishin Mugunta Tahir yace"Wato in na gane kinsan daman Waye Assadiq ammh duk da haka sai da kika zo domin ganin ma idon ki ko?
Sai na kasa mgana shi kuma ya Cigaba da fad'in"Good. na ji dadin haka gwara da kika zo, ki ka ga abunda zaki kara Fahimtar cewa Sadiq ba Tsaran auran ki ba ne, sannan ki kara gane cewa ba rayuwarku d'aya ke da shi ba."
Ya dakata ya na maida Numfashi kafin ya Daga hannu ya na nuna min gidansu Assadiq lokaci d'aya ya na Fad'in"Kinga wannan gidan? Da duka mutanen da ke cikin shi?
Sai na gyad'a masa kai Kamar wacce ta yi karya , bai damu ba ya cigaba da Fadin"To wannan itace hakikanin gaskiyar Rayuwar Sadiq. wacce kika sani a baya ba ita bace Rayuwarsa wannan rayuwar ta karya ce, ita wannan da kika ganin ma idanuwanki itace Zahirin waye Abubakar Sulaiman Abubakar Shinkafi ina fatan kin gane?
Da Sauri na gyad'a kai na cikin mutuwar jiki da na zuciya.
Shi kuma ya cigaba da fadin"Kinga Iyayensa da Ahalinsa tare da yan'uwansa Uwa uba matarsa, to ina so ki saka a ranki Assadiq din da kika sano a zariya karya ne, Sadiq da kika gani a Gusai shine zahiri, shawara da zan baki guda d'aya ne ki yi nisa da Rayuwarsa domin baki da kofa ballatana Muhalli ki je ki nemi daaidai da ke, daman kuma Daga taimako ne sai kuma abu ya zame masa karfen kafa, Sadiq ya aureki ne Saboda mahaifiyarki ta fad'i Gabansa ta rokesa ta na kuka, ammh bai taba son ki ba, Sultana ce matarsa tun ba yau ba shaidu ne kad'ai ba su shaida ba sai yau, kuma ya yi min alkwarin sakin ki tun a lokacin da zaman mu ya kare a zariya, sannan ya tabbatar min da ya sake ki, ban kuma san me ya faru yanzu naji wani Labari na Dabam ba, to ko ma menene wannan ba shi ba ne a gabana, abunda ke gabana shine ki yi nesa da Rayuwar Sadiq aduk in da ki ke zai aiko miki da Takardan sakin ki"
Ya karishe fad'a ya na kallona, nima Tunda ya fara mgana shi na ke kallo cikin mamakin kalamansa.
Da gaske ya ke yi Assadiq baya so na? Kuma yace daman in ya aureni zai sakeni?
Kamar Tahir yasan abunda na ke Tunani ya fara gayamin yadda suka yi da Assadiq a daran da aka Daura mana aure har zuwa ranar da zasu koma Garinsu bayan sun gama Bautar kasa da ce masa da ya yi ya riga ya Rabu dani bayan ya bani jari mai Tsoka.
Bansan ina hawaye ba, sai da naji saukarsu a saman kumatuna, sai dai daga saman lebena ina mirmishi a raina ina fad'in"Tabbas ya bani jari kyakyawan jari a rayuwata."
Batare da wani Tunani ba na kalli Tahir ina fad'in"Naji shawaran ka, kuma in sha Allahu zan yi amfani da ita nagode."
Da haka na share hawayena da gefen mayafina na rab'a ta gefensa na Cigaba da tafiya, sai da na yi nisa da shi kad'an na tsaida adaidaita na gayamasa tasha zai kai ni yace na Shiga, ina kallon abokin Assadiaq har Adaidaitan da na hau ta fita daga Layin gidan su Sadiq bai bar wajen ba, inaga ya na so yaga tabbacin yin nisa da Rayuwar Assadiq gabadaya.
Muna tafe cikin Adaidaita ina Tuna yadda nazo garin Gusau a jiya ina mai Nadamar me yasa na Biye ma zuciyata na zo?
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.