Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 32 of 86

Hakanan na ke zuwa da Katon ciki gaba ina tafiya a tale kamar wata yar kaciya, aikin gidana kam tuni na yaye shi sai in Habiba tazo ne ta kan taimakamin Tunda cikina yana cikin Watannin fitowarsa Duniya ne.
Assadiq duk bayan sati biyu ya ke zuwa ya ganni, in kuma yana wajen aiki ko da yaushe muna tare da juna ta waya.
Ba abunda zan ce ma Anty Surayya sai Godiya domin ta nuna min dukkan kauna, ita ta yi masa maganar Kudin kayan jariri ya ba kuma bata ta sDiyamin komai har da kayan da zan yi Fitan suna dashi.
Kuma sai da ta turomin kayan na zaba duk da kuma nace basai ta yi hakan ba, zata kirani bayan kwana Biyu taji lafiyata ita ta kara karfafan gwiwan ma kada nace zan zauna a gida na cigaba da zuwa makaranta na Saboda hakan zai taimakamin na samu sauki wajen Haihuwa.
Amma na lissafe da wattanin Cikina ta kuma bani tabbacin Adda zata zo ta zauna dani, Da ya ke ma Addan na ta fama da Ciwo yanzu Amma ita kuma sai ta yi lafiya.
Da watan azumin nan babu abunda Assadiq bai ijemin na kayan abinci ba, sai ma ina kyauta da shi kuma sai da na tambayeshi ya bani izini.
Na dibarma Adda Fati kayan abinci har maman suhailat na ba ta, ta na Godiya Ummi dai ban bata ba, tunda Tuni huld'a a tsakanin mu ta jima da yankewa sai dayan matar ne na ba ma wa kawai.
Sannan na Diba nace Habiba ta kai samaru dogon gida wajen maman boy, tunda yace a yi sadaka ga mabukata ne.
Da ya ke ba su yadani ba Lokaci bayan Lokaci suna kawo min ziyara ne, ni ce ma dai sau daya na taba zuwa anguwan tun bayan aurena da komawar Amma gadan mallam mamman.
Bamu muka gama jarabawa ba sai da aka shiga goman karshe na watan azumin Ramadan, Assadiq yazo sau biyu ya dubani ya kuma yi min Weekend, sai dai abun da ke bani mamaki ya rage zuwa Gusai Kamar baya ina tsoron kada ace saboda ni Umma ta raba shi da matarsa.
Ina so na tambayesa ammh kuma wata zuciyar na hanani ganin kamar ba Hurumina ba ne, kada kuma yaga na tsallako abunda bai shafeni ba.
Hatta kayan Sallar da zan yi fitar Idi da shi yace yana Gusai Big sis duk ta karba kudi ni da Sultana tace zata siyamana.
Jin ya ambaci sunan Sultana sai na samu salama araina nace suna tare kenan har yanzu, na manta ko basa tare kanwa take a garesa zai iya yi mata komai da yaya ke yiwa kannensa.
Salla saura kwana uku Assadiq ya kirani yace gobe yana tafe na shirya tare zamu wuce gusai chan zamu yi sallah.
Duk da har acikin Raina ban so hakan ba , sai dai ban iya ce masa komai ba da yaga na damu sai ya fara lallashina yana nuna min kada na damu yan'uwansa ne ya zama Dole mu'amala ta irin wannan salla ko wata Hidima ta rika had'amu ta hakane har watarana zamu samu Fahimtar juna.

Ba ni da yarda zan yi, hakanan na kira su Adda Fati ina gayamusu ita kuma tace miye aciki naje cikin Dangin mijina na yi sallah Tunda haka ya ke so, Adda Rukayya ce da muka yi waya ta rika masifan kada naje a wulakantani fa, tunda ai Adda Fati ta gayamata yadda komai ya Faru.
Sai na nuna mata ba wanda zai min wulakanci matukar Assadiq na tare dani, har Amma sai da na kira na gayamata ita dai Fatan alheri kawai ta yi mana. Kafin ya iso duk na had'a abunda zan Bukata da yamma ya iso dakyar na iya Dama masa kuni, shima sai ya tsinke zubarwa na yi Maman Suhaihat ce ta bashi abun bude baki tunda ni azumin da na yi duka duka bai wuce goma ba.
Washegari kuma Tun safe muka Dauki Hanya Tunda da Motarsa ya zo,  da na gaji da zama yaga ina ta faman Mutsu mutsu sai muka Tsaya ya Budemin baya na shiga yace na kwanta na Huta shi kuma ya koma gidan Gaba yacigaba da Tukinsa.
Da wuri muka isa gusai Shashen Umma muka fara sauka, kuma kamar yadda na Lura kowa yasan da zuwana Tunda shi Assadiq din ya tabbatar musu anan zamu yi sallah.
Na dauka zuwa wannan Lokacin Umma ta sauko ashe abun ba haka ba ne, da muka shigo ta na zaune afalonta ita da Sultana suna Sauraran wa'azi a tashar Sunna Tv.
Sultana na Sanye da Atamfa Doguwar riga ta na ganinmu mun shigo Umma tace ta tashi ta shiga ciki.
Zan durkusa na gaisheta Assadiq yace na zauna saman kujera daman kuma in nace zan duka to aiki ne babba na jama kaina.
Dagani har Assadiq Umma bata amsa gaisuwarmu ba.
Sai ma wani kallo da ta yi mana ta Dauke kai.
Dagani har shi sai muka yi shuru muka kasa mgana , ni kaina a kasa ina ta fama da faduwar gaba.
Shi kuma yana Tunanin Fushin Umma zuwa yanzu ya yi yawa gaskiya.
Shi a ganinsa tunda ya gane kuskurensa to ta yafe masa kamar yadda Abba ya yi, sannan ta zaunar da shi su yi mgana ta Fahimtar juna.
Zuwa lokacin Har chan shinkafi su san da Labarin auransa kuma sun kikkirasa sun yi masa Fatan alheri.

Baba Shitu kuma mahaifin Sultana shi da kanshi ya kirasa ya fad'a masa abunda Sadiq bai sani ba ita Sultanan ta kirashi ta na kuka ta na fad'amai wai Sadiq yaci Amanarta sai da ya yi mata Fata fata sannan.
Kuma ba wanda yasan Umma ta barota da gidan mijinta ta dawo gabanta da zama ya'yanta na zugata.
Abba kuma har alokacin bai ce mata komai ba Sadiq ya kirasa ya na gayamasa Umma bata Daukan wayansa ko zai yi mata mgana?
Abba yace ya kara bata Lokaci ta Huce Tukunnah.
Kamar daga sama naji Umma tace"Ke bakar Annoba tashi ki fita zan yi mgana da d'ana."
Haka ta fad'a kai Tsaye Lokaci d'aya ta na Hararana.
Da Sauri na mike har sai da bayana ya amsa, Shima mikewar ya yi Umma ta dakamai Tsawa kafin tace"Koma to ka zauna Bita zai zai."
Ba shi da yadda zai yi sai ya koma ya zauna sannan ya kalleni ya na fad'in"Ki shiga bangaren Innani ko bangarem mama"
Ban ce komai ba na kama Hanyar Fita shi kuma sai ya daga murya ya na fadin"Kin ji ko?
Sai na juyo ina daga masa kai idanuwana fal da kwallah.
Na jima a haraban gidan na rasa ina zani sai da na gama kukana na share kwalla sannan na nufi bangaren Mama.
Kaamar Daga sama ta ganni farko Siyama ce zaune a falo  ammh yarinyar nan kallo wulakanci ta yi min sai ni ce na gaisheta sannan nace mata wajen Mama nazo, shima sai da taga dama sannan ta tashi ta shiga ciki ta yi ma Maman mgana sai ga su sun fito tare.
Ita da Fara'a muka gaisa fad'i ta ke yi" yanzu kuka iso kenan? Ina shi magajin gidan?
Kaina na kasa nace"Ya na wajen Umma, shi yace na zo nan na zauna."
Mama ta jinjina kai kafin tace"Allah sarki sannun ku da zuwa ya nauyin jiki? Kai wannan cikin naki akwai girma wa ya ga Runduna."
Kaina na kasa ban yi mgana ba, sai faman hira take min ta min Tambayoyi ni kuma bani da sakewa yasa na ke amsata daya daya.
Ni ce naga ko ruwa ba ta bani ba sai nace mata zan sha ruwa.
Cikin yake tace"Af nafa manta ku bakwa azumi,  Siyama"
Sai ta fara kwalama Siyama kira sai gashi ta fito ta na wani Tura baki Mama tace ta kawomin Ruwa.
A wulakance ta kawomin Ruwan gora kuma don mugunta mai sanyi, ba ta ko Duba Halin da ni ke ciki ba.
Kuma babu ko karamin kofin da zan sha, Kuma gashi ina jin kishi hakanan na sha kad'an na ijiye.
Daga karshe da Mama taga na kasa sakin baki na bata labari sai ta shige ciki su ka barni anan kamar wata almajira.
Gashi Fitsari ya matseni na rasa yadda zan yi, ina zaune kawai ina ta sharan kwallah na tausayin kaina a baya ina Murnan na fita daga cikin Tsaka mai wuya ashe tsuguuno bata karemin ba.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.