Tmw Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: TMW BOOK 3.txt
Chapter 47 of 86
Karisowa falon ya yi yana gaida Umma, rabon shi da ita tun safe ta amsa lokaci d'aya takallesa kafin tace"Ya karfin jikin naka?
Ya amsa mata da Alhamdulillah.
Umma ta mele baki kafin tace"Ka dai rika Hutawa ina lura da kai cikin kwanaki nan baka san zama waje d'aya kada dai ka manta har yanzu jinya ka ke yi baka gama warkewa ba."
Abba na gefe ya yi yar dariya kafin yace"ina shi ina Hutawa baban yan Biyu ne fa, abun alheri ne ya same shi fa sai ki ce ya koma ya zauna kuma salamatu"
Jin Abunda Abba yace ne yasa Umma ta kasa mgana.
Sajida ce ta kalli Sadiq kafin tace"Sadiq ba mgana"
Kallonsu ya yi dukkansu a dage kafin yace"Sannun ku."
Sadiya ce tace"Wai ya sunan yaran ne?
Domin sun ji kishi kishin sunan yaran, har Umma suka fesama ammh bata ce musu komai ba.
Shi kuma da gayya yace"Sulaiman da Muhammad"
A tare suka had'a baki wajen fad'in"Allah ya raya."
Dagaji ba har zuciyarsu ba ne.
Shuru suka yi gabadayansu ransa sai ya fara baci ganin suna ta kuskus har ya mike kome ya Tuna sai ya koma ya zauna ya na kallon Abba kafin yace"Abba daman ina so mu yi mgana."
Abba ya gyara zama yana kallonsa kafin"Ina sauraranka Abubakar"
Sadiq ya gyara zama yana fadin"Lokacin da Hatsarin nan ya Faru dani ka samu Labarin Sadiya da Sajida sun bi matata har zariya sun ci mata Mutumci da Tsohon ciki suka koreta suka kuma kwace makulin dakin da wayarta har da Atm din bankinta? Ko ka samu Labari?
Abba ya jinjina kai kafin yace"Tabbas na samu labari. Surayya ta sanar dani komai tun a lokacin."
Ya fad'a ya na kallon Umma da ta Tsargu ta sunkuyar da kanta
Su Sajida kuma sai suka fara Zare ido.
Cikin gyada kai Sadiq yace"Yauwa daman dalilina na yin shuru ban Dauki wani mataki ba shine ina fama da jinya sannan aka zo aka yi ma Siya aiki na samu karuwa, kuma ni daman na Riga na gama Tarasu ne Abba zan yi musu iyaka da iyalina kada kace ban kyauta ba."
Kai Tsaye Abba yace"Ka yi musu duk abunda ka yi ra'ayi, domin wannan karin nima sai naci mutumcinsu Tunda sun Tsallake Hurumin da ba na su ba."
Jin haka yasa Sadiq ya mike Zumbur ya nuna su Sajida da yatsa kafin ya fara fad'in"Wallahi Tallahi kun ji rantsuwar d'an musulmi in dan ku ka kara shiga Hurumin matata sai na saka Shari'a ta yi min iyaka da ku gabadayan ku."
A razane suka kallesa Sadiya tace"Eh Saboda mace za ka saka shari'a ta yi mana iyaka fa kace Sadiq?
Kai Tsaye yace"Kwarai ma da gaake, ai ko a yanzu sa'a kuka ci wani abu mara dad'i bai samu matata ba da na rantse da wanda raina ke hannunsa sai na yi kararku, kuma kunsan Tsab za'a hukuntaku saboda kun Shiga Hurumin da na ku ba, uwa uba kuma kun ci zarafinta a matsayinta ta yar Adam kuma yar kasa."
Mamaki ya hanasu kara mgana sai kallonsa suke yi baki bud'e.
Umma kuma sai Harara ta ke jifanshi dashi baisan tana yi ba.
Cikin Fushi ya Cigaba da fadin"Ina ruwan ku da ita? Ko ku kuka auramin ita ? Ba wanda ya taba taimkamin da sisin kwabo wajen Rike ta, shine kuma zaku rika shiga cikin Rayuwata kuna min katsaladan? A kan wani Dallili na saka ku ne? In ku baku yarda da Allah ba ni na yarda da shi na kuma san duk abunda ya Faru dani mai kyau ko akasinsa daga Ubangijina ne Siya bata isa ta zama Silar faruwar wani abu gareni ba face abunda Ubangiji ya kaddaramin, Kashedi na gare ku shine ni ne dolen ku, dani ku ke da alaqa ba da ita ba, so ban yi ma kowa Dole ya karfafa alaqa da Siya ko ya'yana ba, ku kyale ni da su ni ne Dolensu ita din matatace ni ya kamata na kula da Hakkokinta tare da Amanarta, ban kuma ce kowacce taje ta yi mata barka ba, ban kuma ce nima ku yi min ba, duk ku je na yafe wanda yaga dama ya yi abu mai kyau kansa ya yi mawa ba ni ba, ni dai karfafan Kashedi na shine ba Ruwan ku da matata in kuma baku ji ba ku sake Shiga harkaarta ku ga yadda Shari'a zata Shiga tsskanina da ku."
Sajida sai ta saka kukan munafunci ta na fadin"Abba Umma kuma gani dai ko? Kuna ji yana fadin zai yi shari'a damu Saboda matarsa ko? Ai dai mu ci Darajan mu yayyensa ne muna gaba da shi."
A fusace Sadiq yace"In kun girmeni ai baku halliceni ba? Ko kuma domin kun girmeni sai na zauna kuna min cin kashin da kuka dama?
Ai girma ba Haihuwa ba ne, bazai hana naci zarafin duk wanda yace ni zai ci nawa zarafin ba, ko da akace bin na gaba na tare da Bin Allah, in babba bai kama girmansa ba karami na daidai da ya taka girman babban ya wuce abinsa."
Umma ta gaji da jin mganganunsa ta mike ta daka masa tsawa kafin tace"Kaji kunya, kai yanzu Saboda Mace ka ke zagin yan'uwan ka?. Mace ma wata bakar Annoba wacce ta so kashe ka."
Kafin Sadiq ya yi magana ya Rigasa da cewa"Salamatu ki koma ki zauna."
Cikin mamaki Umma tace"Abban siyama."
Kallonta ya yi yasa bata karisa mgana ba ta koma ta zauna.
Shi kuma Abba sai ya kalli Sadiq kafin yace"Kyalesu hakanan ai ka yi musu iyaka, nima kuma na shata musu layi matukar ba alheri ne zai kai ku kusa da iyalamsa ba kada ku kara zuwa, sannan mgana ta karshe duk abunda kuka san kun amsa daga Hannunta ku taka da kafarku kuje ku maida mata sannnan ku tabbatar da kun bata Hakuri, in kuma ba haka ba wlh dukkan ku sai na yi mummunan saba muku"
Suna jin abunda Abba yace suka fashe da kuka gabadaya wannan karon na gaske ne.
Tunda ba su dauka har Abba zai Bud'e musu wuta haka ba, Umma kuma da suka Dogara da ita Abba ya hanata mgana.
Sajida cikin kuka tace"Don Allah ka yi hakuri, mu fa Umma ce ta ce mu je mu koreta ba laifin mu ba ne."
Umma ta kallesu ta na Hararansu Abba ya ya hade rai kafin yace"Ya rage naku, ni dai kun ji matsayata itama wacce ta saka kun zata karbi nata Hukuncin daidai da abunda ta aikata."
Zasu fara magiya yace su tashi su bar masa falo.
Shi daman Sadiq yana gama mganarsa ya fita ransa bace.
Suka tashi suna sharan kwallah suka Fice, suna fita Umma ta kalli Abba tana fadin"Abban Siyama ai ba laifi ba ne domin na saka an kori wannan bakar Annobar, wacce ta so ka kashe mana d'a daya Tilo namiji da muka Haifa"
Ko kallonta Abba bai yi ba taga ya Dauki waya ya na Dannawa ba ta ankara ba sai da taji suna gaisawa da Mallam zakari ta Rude.
Tana rokonsa da ido da Hannu ammh Abba ya yi kamar bai ji ba.
Ya kwashe duk abunda ta aikata ya sanar ma da mallam zakari.
Dagacan bangaren ransa ya baci cikin Fushi ya fara magana Abba na jin haka ya saka mata a amsa kuwwa.
Cikin ba da Umarni Mallam zakari yace"Sulaimanu ka fattake ta daga gidanka Tunda Salamatu ta zama zakka, ni kuma ka sanar da ita Tunda ni Uban banza nake gareta ta bid'i wani gidan Uban ba dai nau gidan ba ka hid'i mata haka Tunda Shawaran ki uwa take mara lissafi."
Abba ya kalleta alamun kinjin dai ko sannan yace ai tana jinsa.
Nan yace a bata waya ya yi ta bacinta Umma tana kuka tana bashi Hakuri ya kashe wayarsa.
Abba kuma ya karbi wayarsa ya mike yana fadin"Bazan kore ki ba, ammh ki sani itace damarki ta karshe, nagaji da d'aga miki kafa salamatu."
Daga haka ya tashi ya bata waje, Sai ga Umma da kuka har shashenta.
Su Sajida da suka zauna ta dawo su kara zugata sai kuma suma suka ga ba Dama.
Sultana dai suka gama zaunarwa suna kara zugata, Umma kam ciki dakinta ta shiga ta maida kofa.
Me ta saka me ta saka oho, ta ga dai bata da mafita su Sajida ma bata san tafiyarsu ba.
Tun safe ta je bangaren Abba bayan Mama ta koma shashenta ta Durkusa ta na bashi Hakuri shi kuma yace bakomai.
Fatansa ta sakama auran magajin gida albarka sannan ta maida masa matarsa tace duka zatayi.
Daga karshe yace bayan suna taje taga Jikokinta ta yi ma matar Sadiq barka taje to.
Ta rokesa ya kira Mallam Zakari yace masa ta bashi hakuri, shi kuma yace sai in yaga da gaske ta ke yi hakurin da ta bashi Sannan zai kirashi ya gayamasa.
Tana komawa bangaranta ta kira Sajida da Sadiya da Sa'adatu tace su shirya suje Zariya suna.
Sannan ta kira Surayya tace ta zo gida tana nemanta.
Daman kuma Surayyan zata Biyo Tunda Abba yace har da Mutanen shinkafi za su tafi Sakeena ta kira ta tace itama zata je.
Ta d'an bata Lokaci tunda ta siya wasu kaya aka kawo mata daga kasuwa, Suba'atu da Saddiqq sun turo kudi a siya ma maijego kaya ita da Twins.
Ta yi mamaki da ta zo Umma na bata Hakurin ta jira sauran yan'uwanta su tafi tare, sai ba ta ja ba tace su yi sauri saboda kada su yi dare kuma sai Gobe za su dawo.
Bata gama mamaki ba sai da Sadiq ya Shigo Umma ta yi masa Barka da kuma saka albarka ya amsa bakinsa har Kunne yaci fararan kaya ya Fito sak angon karni karni.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.