Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 78 of 86

Ammh ina so na wallafa wannan Labarin ya fita duniya in sha Allahu
Mun jima muna mgana Sultana ce ta sake fitowa jinsa shuru ganin haka yasa na yi masa sallama na shiga ciki.
Da safe tun asuba na tashi na shirya yara Naja ma na saka ta shirya.
Weekend ne ranar Asabar daman tun jiya na yi miyar Naman rago sai na soya musu dambun kaji na zuba a roba nace a kaima Umma.
Miya kuma na innani ne baiwar Allah, sai da naga zasu tafi naji dama na Bisu ammh kuma ina Bukatar natsuwa a gida.
Sai da na Boye sannan suka samu tafiya da su Asim da ke ta kuka kayansu na had'a musu da yawa nace su sha hutunsu wajen kakaninsu.
Sai azahar Assadiq ya kirani yace sun sauka, ina tambayansu Asim yana dariya yace Mama taja megidanta Umma ma haka.
Innani na tambaya yace da sauki, bazai dawo ba sai an siya mata keken da zata rika zama akai tunda yanzu ta zama sai dai a kwantar kuma a tayar.
Kafin Assadiq ya dawo na kira Surayya Dee mun yi mgana na gayamata kudurina taji dadi kuma ta bani goyan baya.
Tare da wasu sharwarin, na kuma kira Hajiya Habiba iman itama sosai ta karbeni ta kuma ji bayanina ta kuma bani shawara.
Na sake kira Auntysis saboda gogewarta a harkan Rubutu da Rayuwa gabadaya.
Dukkansu sun bani shawaran na yi Rubutuna a waya saboda yanzu abun ya koma Direct Print in na yi sai a bugamin shi.
Kuma bakinsu ya zama d'aya sunce bayan na buga zan iya sakin Labari a softy Copy yadda sakon da na ke so zai je ma al'umma da dama.
Sun bani shawaran na yi Bincike sosai kuma na nemi mganar malamai da magabata.
Ni kuma nasan ta wannan bangaren bani da matsala ina da Babban malamina a gefe wato Assadiq.
Da ya dawo shi ya taikamin har na fara Rubutun a computer tunda ya siyamin wata na bama Habiba Tsohuwar tawa.
Sannan Saboda ban saba ba Typing din ba, ya na bani wahala ammh hakanan Saboda na saka abun a raina yasa na Dage.
Koda yaushe cikin bincike na ke yi, Assadiq na kara nuna min wasu abubuwan a Labarin Rayuwata nace bazan boye komai ba.
Hatta sunanaye da garuruwan da abun ya faru saboda so na ke mutane su san cewa da gaske ne ba Farar Kafa a musulunci su kuma saki mganar mutane su kama Allah su gane Ubangiji ne ke da alhakin Faruwan komai.
Ammh Assadiq yace ya na da kyau na sauya sunan garuruwa da wasu mutanen, ammh zan iya amfani da sunana tare da nashi sunan.
Ya kawo min Hujja akwai wad'anda Labarin ya shafa kuma yanzu sun yi nesa da Rayuwata ambatan sunansu kan iya zama matsala ko anan gaba.
Shiyasa sai na bi shawaransa na zan sauya garuruwa da sunayen wasu daga cikin su.
Da na Fara na turashi zuwa wayata da Taimakon Assadiq na kuma Tutturama Marubutan da na yi shawara da su, su ka dubamin su ka kuma jinjina min sannan tare da nuna min inda ya kamata na gyara.
Na saka abun acikin raina shiyasa bana jin nagaji.
Kuma ga shi su Asim basa nan da na sallami Assadiq zan dukufa sai da ya fara min fad'a ne ma nake Tsayawa naci abinci, da sai yammah yini na ke yi da yunwa.
Sannan da daddare ma nace sai nayi, shi ya ke hanani ya sakani dole na kwanta na Huta.
Auntysis ce ta  fara ankarar dani ban sama ma labarin suna ba.
Na yi ta Tunanin, wani suna zan sama masa ni da Assadiq mun fi kwana Biyu muna tunanin sunan da zamu saka ma Labarina.
Sai da muka shafe sati sannan mu ka sama masa suna.
Nace a iya rayuwata na Fuskanci Rayuwar TSAKA MAI WUYA.!
Kuma na saka wasu Rayuwaka da Dama da suka Rab'eni acikin TSAKA MAI WUYA.!
Shiyasa wannan Labarin nawa zan saka masa suna TSAKA MAI WUYA(LABARIN HASIYA).
Assadiq yace tabbas sunan ya yi, suma da na tura musu sukace sunan ya hau da Labarin na cigaba da Rubutuna kawai.

Kwarin gwiwan da na samu Daga duka bangarorin yasa na kara zake Damtse, kuma yan'uwana ba wanda ya sani Amma kad'ai na gayamata Tunda ita uwace.
Ta kuma sakamin albarka acikin Lamarin, ni ba suna na ke so na yi ba, sannan ba sha'awar Rubutu ne a raina ba kawai dai ina son na Rubuta Labarina ne domin  masu Tunanin akwai mata masu Farar kafa su daina
Da masu tunanin wani zai iya yi ma wani abunda Allah bai yi masa ba.
Da masu Tunanin zawara ba mata ba ne sannan ba su da yanci da gatan da Sauran mata suke da shi.
Wannan shine suka kara sakamin kaimi da Himma wajen Rubuta Labarina.
Kwatsam ina cikin Rubutun karamin ciki ya Bulla a jikina Laulayi ya sakano gaba da dole na ijiye Rubutu a gabana na koma ina fama da kaina.
Allah ya taimakeni sai da na yaye su Asim duk da ban ji dadin cikin alokacin ba ammh ban yi ma Ubangiji Butulci ba.
Na tatattara Rubutun na ijiye a gefe ammh ba wai na hakura da kudurina ba ne.
A cikin raina na saka ko shekara nawa zai daukeni kafin na gama zan yi kokarin na ga mashi in dai da rai da lafiya.

Mata muntashi tsaye mu yaki infection (sanyi) Wani ciwone Mai nacin gaske Wanda idan kikayi wasa xaihanaki jindadin Aure Sannan maganin shi saikin daure da nacin shanshi Akai Akai toh kufito🤌🏽 KUSAI TSIMIN TABAJE DOMIN MUNA DAFASHINE DA INGANTATTUN SAIWOYI MASU AMFANI AJIKI DAKUMA LAFIYA, CIWON SANYI, SANYIN MARA, BASIR DASAURANSU INSHA ALLAH DUK WANI CIWO INDAE NA SANYINE ZAIZO KARSHE DA YARDAN ALLAH KIDAE KIDAURE KIDUNGA SIYAN TABAJE KIJEFI TSUNSTU GOMA DA DUTSE DAYA💃💃💃
Akwai infection Wanda yake nuna kanshi Akwai Kuma kurman infection Wanda baxaki San kinada shiba Amma yanacan yana Miki illa domin duk kyan Kayan mata baxakiga aikinsu ajikinki ba ko Kuma sumiki aiki bayanda akaso ba
Anason duk bayan wata 1 mace tasha maganin infection sbd samun lafiyar jikinta
Alamomin shi sune
Fitar farin ruwa
Kaikayin gaba/ko kuraje
Jin zafi yayin sex
Daukewar ni'ima
Daukewar sha'awa dadai sauran su
Kafin kifara Shan maganin mata yakamata ki fara Shan maganin infection
Ina Yan mata Budurwa kema Yakamata kidinga Shan maganin infection Dan kariya da lfy ki karsai kinyi Aure infection ya Riga yamiki illa Baki saniba Allah y bamu lfy y karemu Ameen 🙏

*Janafty* 
*TMWB3020*

*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*

https://chat.whatsapp.com/K3rO5UonX4GDVxtQbA5mZl
PAID ADVERT✅

Assalamualaikum wa rahmatullahi ta'ala wa barakatuhu!!! Wannan group din dai na komai da komai ne. A taiqaice
*Farashin mu na daban ne compared to sauran Yan kasuwa
*Kaya masu kyau da quality. Abinda kika zaba shi za a Baki
* Swift delivery.watau waybill a sauqaqe da Yardar Allah
* Muna sake New Arrivals ka fin su cika Gari
* Muna iya duba maku kaya a good price ko da ba namu ba ne idan kuka Aiko da hoton kayan
Allah sa mu qaru da juna Ameen

Ashe bansan cikin su Asim kamar Bonus ba ne sai da na samu wannan, gabadaya na zama a rikice ba na iya komai laulayi na ke yi mai zafi ga Amai da miyau kamar na wanchan.
Ga shi ba na son warin Tafasan abinci warin magi ma ba na so, ballatana na mai ko wani abu.
Shiyasa na daina girki saboda in dai na shaki warin magi ko kamshin Tafasan girki in na rika Amai ranar kamar zan Amayar da Hanjin cikina.
Mun je asibiti an gwada jinina duka duka cikin wattani biyu ne da wani abu, sau biyu muna zuwa ana sakamin Drip saboda karfin jiki sannan ba na iya cin abinci.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.