Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 35 of 86

A d'ayan bedroom din Anty Surayya ta kaini na yi alwala na yi sallah.bina zaune ina addu'a Sultana ta shigo ta yi kuma mamakin ganina sai da ta Tsaya shuru sannan kuma ta koma da baya.
Sai da na natsa sannan na fito falon Anty Surayya bata falon ashe waya aka kirata sai ta fita.
Ina shigowa falon sai na tafi kujeran chan nesa da su zan zauna har ga Allah ban ga Tahowar Sultana ba.
Sai da naji ta min wani bangaza kamar na ranar.
Na kusa faduwa da yasa hankalina ya tashi sai da na Dafa kujera.
Cikin sauri nace"Sultana kamar baki ganina?
Sai gabadaya Hankalin su Sajida ya koma kaina.
Kallon cikin ido ta yi min kafin tace"Au Allah? To ban gan ki ba."
Sai alokacin na Lura ta sauya kayan jikinta.
Batare da na kara mgana ba na gyad'a kaina na koma na zauna ina daidaita yanayina.
Sajida ta yi tsaki kafin ta kalleni ta na fadin"Ko da ta ganki ke ya kamata da kika ganta bayan kin kauce mata sannan ki ramkwafa ki gaisheta da ladabi."
Sadiya tace"Tabbas tunda ita kika yi ma kwacen miji."
Na yi shuru ban yi mgana ba Sadiya ta dakamin tsawa ta na fadin"Bazaki duka ki gaisheta ba?
Sai kawai na sauko daga kan kujera na Duka kan kafafuwana ina cije baki na kalli Sultana dake tsaye nace"Ina yini sultana?
Idanuwana sun ciko da kwallah.. shewa suka saka gabadayanau suna min dariya.
Sajida tace"Kowa ya tuba  don wuya.".
Sadiya ta karishe da fadin"Ba lada."
Ba su sam shigowarsa ba  ni kaina kamshin Turarensa naji da kuma dagoni da ya yi daga durkushen da nayi.
Sai jin muryansa suka yi ya na fadin"Are u ok?
Sai na gyad'a masa kai.
Shuru suka yi sun sha jinin jikinsu, kallonsu ya yi a fusace kafin ya Tsaida kallonsa kan Sultana da wani hade rai tana marmari da ido.

Har gabanta ya taka bayan ya sake ni, ya tsaya kam sannan ya daga hannu ya nunani kafin yace"Kinga wannan?
To itace matar da na fara aura kafin ke, saboda haka daga yau ya kamata ki sani tana gaba da ke, ke zaki fara girmamata kafin ita ta girmamaki."
Sultana ta kallesa kafin tace"Tab."
Ta fad'a ta na Tura baki.
Sadiq ya jinjina kai kafin yace"Eh haka nace saboda haka daga yau in kika ganta ke zaki gaisheta ki, ya kamata ki haddace cewa ita na fara aure kafin ke, ni kuma ba sakaran namiji ba ne da zan zauna kina wulakantamin mata ba, Sonta na ke yi shiyasa na aureta kamar yadda kema ina sonki ne yasa na aureki."
Sultana sai hawaye ta na so ta saka kuka.
Sajida ta gaji da shuru tace"Ammh Sadiq baka da kunya wlh."
A fusace ya daga mata Hannu kafin yace"Ban saka da ke ba mallama ki Rufemin baki, ko ina ruwan ki da shiga Hurimin iyalaina.?
Ya karishe fad'a yana nuna ta da yatsarsa.
Ai sai ta kasa mgana ganin ya harzuka Sadiya ma na shirin magana a harzuke yace"Kada wace ta kara sakamin baki acikin magana ta da iyalaina. In ba haka ba  ran mata zai baci na rantse da Allah."
Surayya ta shigo tana gefe ta na mirmishi.
Kan Sultana ya koma yana fadin"Sabosa haka ki shiga taitayinki, in kikace zaki yi ma matata fitsara maganinki zan yi bana son reni kin sani."
Sultana ta mike ta saka kuka ta na Fadin"Ai ba sai ka nun ma duniya baka sona ba, auren hadi aka yi mana shiyasa ka ke kare ma wannan banzar matar taka mai kwacen miji kawai"
Taso mata ya yi kamar zai Daketa ta yi baya sai kawai ga Umma Tsulum a falon.
Shi ya hanasa kara wani motsi ni kaina gabana sai fad'uwa ya ke yi
Sajida na ganin Umma ta Nufeta ta na karanta mata Assadiq ya zagesu saboda ni.
Har yana nufar Sultana zai daketa.
Umma bata wani tsaya Bincike ba ta nuna ma Sadiq kofa tace ya fita ya bata wuri yana Hucin ta hanashi mgana ya fita.

Ni kuma ina Tsaye kafafuna na rawa Surayya ta taso ta wankeni Umma ta d'aga hannu ta na karisowa cikin Falon lokaci daya ta na kallona kafin ta juya ta kalli Sultana tana fadin"Share hawayen ki, matukar ina raye ba wanda ya isa ya Tozarki."
Sultana ko kuka take yi sosai daman ganin kayan mu iri daya yasa su Sajida suka kara Zugata da cewa ita bai Dauketa da Muhimmanci ba muraranta ya ke nuna yafi kaunata sma da ita, ita kuma bakin kishi ke dawainiya da ita.
Umma ni ta kalla a fusace kafin tace"Ai in baki had'a fada tsakanin yan'uwana juna ba baki ci sunan ki  bakar Annoba ba, kin ji kunya kuma kin yi asara ke yanzu a dad'in ki ne ki zo ki raba kan zuru'a? Ki saka d'ana ya na jayayya dani sannan ki sakashi yana Sa'insa da yayyensa to ki saurareni dakyau har Abada bazan taba karbanki a matsayin matar Abubakar ba, Sultana na sani kuma in dai ke ya zaba wlh sai dai na sallama miki shi, shi kadai Annobarki ta kona sa, Fita ki barmin falo kafin raina ya baci na saka ayi miki koran kare."
Daman tun da ta fara mgana na fara kuka ina jin tace na fita na juya ina jin cikina na Juyawa na fita ina kuka.
Surayya ta kalli Umma ba dad'i kafin tace"Umma m."
"Ke ma bita ki fitar min daga falo."
Surayya ta kalli Umma kafin ta kad'a kai kawai ta juya ta bi bayana su Sajida suka rakata da wani kallo aransu suna tunanin Big sis bata kishin Umma.
Ta na fitowa ta ganni ina kuka, sai ta rikeni zuwa mota itama ranta a bace yake Sadiq ta kira tace yazo ya Tukamu zuwa gida.

Ya shiga damuwa ganin yadda nake kuka sai ya fara cewa ita ta lallasheni.
Da damuwa a saman fuskarta tace"Lamarin Umma ya fara nisa, Su Sadiya suna kara zugata ni yanzu kwata kwata ta daina bani fuska."
Sadiq yace"Nima wlh abun duk ya Dameni."
Surayya ta sauke Numfaashi kafin tace"Mallam na gummi zaka je ka sanar ma abunda ke faruwa na tabbata in ya yi mata magana zata ji."
Sadiq yace"Na yi tunanin haka, ammh cewar Abba ne na bata Lokaci Shiyasa ban je na samesa ba"
Surayya tace"Ai kada ka jira, ammh kafin nan gobe ka maida Hasiya gida, zamanta a wajena ni kaina Umma ta fara fushi dani kuma bata da sakewa kwata kwata anan."
Ya aminta da shawaranta yace haka za'ayi in zai kaini Zariya zamu Tsaya anan Gummi din.
Haka ko akayi, tun safe muka tafi Abba kawai da Innani ma yi ma sallama da kanshi ya hanani Shiga wajen Umma, fuskata har ta Kumbura saboda kuka da kuma duka siyayyan da Anty Surayya ta yi min muka taho da su.
Sai da muka fara biyawa Gummi Gidan su Umma kamar yadda yace min suka gana da mallam zakari na wajem awa d'aya.
Da kanshi ya yi mishi bayanin komai, mallam zakariya na ta fad a yace kuma sai ya saba Umma har Abban ma da ya Biye mata.
Sam a gidan ba'a nuna min wani kyama ba nan muka yi azahar muka ci abinci sannan muka dauki hanya.
Sai bayan la'asar muka shigo Zariya ganin yamma tayi yace sai da safe zai wuce Abuja.
A daran ina jinsa ya Kira mahaifin Sultana shima ya karanta masa abunda ke faruwa.
Ran mallan Shitu ya baci yace gobe goben nan zai je ya samu sultana sai ya sab'a mata itama.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.