Tmw Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: TMW BOOK 3.txt
Chapter 36 of 86
Sadiq daman so ya ke daga Umma har Sultanan a yi musu fad'a alokaci daya.
Kwana ya yi yana lallaahina tare da alkwarin bazai taba barina ba.
Ni na ma b'ata masa Lokaci sai wajen goma ya bar gidan ya kama hanyar Abuja.
Sadiq ya fita cikin Damuwa ga koken koken da na kwana yi.
Ga kuma matsalan su Umma da Sultana gabadaya sun chazamasa kai.
Ya bar kaduna kenan da kad'an baisan yadda aka yi ba motar sa ta kwace masa ba, shi dai yaji mota na Tamaula dashi akan Titi daganan Hankalinsa ya gushe.
Yaji sanda motar ta Tsaya ya kuma san ya jisa zaune a inda ya ke
jini na bin fuskarsa tunda ya saka Seat belt.
Daga nesa nesa yaji ana salati da sallallami tare da mganganun mutane daganan yaji Duniyar ta tsaya masa cak.
*Janafty*
*TMWBK3010*
P
*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*
Duk sammakon da Mallam Zakari ya buga daga Gummi zuwa Gusau sai da ya zo ya iske Mallam shitu ya rigasa zuwa daga Shinkafi domin ana idar da sallar asuba ya kamo hanya so ya ke ya yi abunda zai yi. In ya gama ya kama hanya koma can har kuma yaje ya yi yan Harkokinsa.
Sultana sai da ta raina kanta, ta sha Fad'a kamar me, dukanta ne kad'ai Mallam Shitu bai yi ba, bata tab'a sanin cewa ya iya fad'a haka ba Tunda wani abu bai taba had'a su ba, sannan kuma ba ta girma a gabansa ba sai dai zuwa ta na dawowa.
Umma kuma sai ta so ta kareta ita ma Mallam Shitu ya kalleta yana fadin"Maganar gaskiya Hajiya ki daina mara ta baya, da ke har ita baku taki gaskiya ba abunda ku ke son ku aikata ba gaskiya ba ne kuma ba Shari'a bace."
Sannan ya kara kallon Sultana da ke gefen Umma ta na ta faman kuka, har Abba na wajen shi da Innani tunda a shashen innanin ne ake zaman.
Cikin daga murya yace"Ke kuma ki sani in dai kika Boyema zuciya kika ce zaki wulakanta mijin ki, ke ce a kasa matukar kika rasa miji kamar Abubakar ba baki na yi miki ba ammh Wlh tallahi bazaki taba samun kamarsa ba, kuma ina so ki sani bai kamata ki zama Butulu ba, in mahaifiyarsa ta nuna fushi a kansa ta na da gaskiya itace uwa a garesa ammh ke baki da wannan Hurumin tunda kina karkarshinsa ne daidai da rana d'aya in kika sab'a masa sai Allah ya Hukuntaki akan laifin da kika aikata."
Sultana na kuka Fuskata duk hawaye ta dago ta na fad'in"Baba aure fa ya yi bansani ba."
Dakuwa ya yi mata kafin yace"Kin ga naki, ana rabaki da kiwon awaki kina kokarin gayamin kyalla ta Haihu? Ya yi auren sai me? Ke ki kiyayi kanki ai ita ya fara aura in yaso sai yace ya fasa auranki kuma ba mai yi masa Dole, ammh bai yi haka ba sai ke ce don rashin Mutumcin ki ke har kara fad'in aure ya yi, to ya yi auren sai ki hanasa abunda Allah yace ya yi, ni ai da ya Burgeni ma da uku ya aura sai ku zama ku hu'du naga yadda zaki yi, banda shashanci ko ni Ubanki bayan mahaifiyarki matana Biyu saboda Rashin adalci irin naki don mijinki ya yi aure sai kice zaki fara yi masa rashin d'a."
Daga Umma har Sultana suka yi shuru, Umma ranta ya gama baci saboda ta da na tabbacin Sadiq ne ya Kirasa ya fad'amasa kuma taci alwashin zai zo ya sameta sai ya raina kansa.
Ita kuma Sultana kukan yadda Babanta ya kasa Fahimtar irin cin Amanar da Yaya Sadiq ya yi mata ne, ammh kuma sai ya zo ya Bige da yi mata fad'a.
Fata fata ya yi ma sultana itama Umma ya yi mata nasiha yajawo Hankalinta, ammh duk bata ji ba ta dai nuna kamar ta fahimce shi kuma zata gyara ne.
Kafin tafiyarsa sai da ya jaddadama Sultana ta koma dakinta mijinta yau ba sai gobw ba, kuma sannan ta girmama ra'ayin mijinta. in kuma yaji Sabanin haka zai kara dawowa ammh ta sani dawowar bazata yi mata kyau ba.
Ko karyawa bai tsaya ya yi ba wajen Goma na safe ya Juya ransa bace shi kam Abba lamarin ya yi masa daidai.
Innani kuwa kamar an tsaface bakinta bata yi mgana ba sai dai Mallam Shitu ya sha tabe baki da Harara ta zata zai sako sunanta ne ta yi masa wankan Tsarki duk dai tace ta yafe ammh dai duk da haka dai, sai kuma aka yi sa'a bai sako sunanta ba to ina zai sakota Tunda yasan Halinta.
Sultana kuwa bayan tafiyar mahaifinta ta kalli Umma lokaci d'aya ta na fadin cikin kuka"Umma yanzu sai na koma?
Umma ta kalleta ita tsabar takaicin da ta ke ciki ya hanata mgana, ta na ganin Sultana na gunjin kuka ammh ta kasa ce mata ci kanki ballatana ta iya lallashinta
Tafiyarsa ko awa daya ba'a yi ba sai ga Maallam zakari d'aya daga cikin jikokinsa ya rakosa.
Tunda Abba ya kira Umma a waya ya gayamata zuwan mahaifinta nata gabanta ya fad'i saboda tasan halin Mahaifin na su yana da zafi, shifa ba ruwansa komai girman ki kika aikata ba daidai ba gaban ya'yanki zai yi miki Kaca kaca bai damu ba.
Shiyasa tunda Umma taji Labarin zuwansa jikinta ya yi sanyi sannan a gefe daya kuma na zuciyarta ta kara Kullatan Sadiq wato itama bai barta haka ba sai da ya had'ota da mahaifinta lalle zai gane ba shi da wayau in suka had'u.
Shima a bangaren Innani ya sauka daman ta so tazo d'aya da Innani, itama sosai take jin dadin Hira da shi, mutun ne mai fara'a da barkwanci gashi yana Biye ma duk abunda Innani ta zo da shi baya kusheta Shiyasa da ta gansa ta rasa ina zata sakashi Saboda Murna.
Kamar an bude famfo haka ta shiga labarta masa abunda ya kawosa, har da sauran Labaran da bai sani ba na game da Hasiya.
Kai Tsaye mallam Zakari ya kalli Innani kafin yace"Naga matar jiya tare da ita ya biya wajena, yace Zariya zai kwana yau tun safe zai kama hanyar Abuja"
Sai Innani ta rike baki ta kasa mgana, Shigowar Umma da Abba ya hanata wata mgana.
Umma ta duka zata gaishe shi ya daga mata hannu da sauri yana fadin"mike kawai abunki salamatu yau bazan karbi gaisuwarki ba, sai kin gayamin babban Dalilin ki na kin sakama auran da Abubakar ya yi albarka? Ke shad'aniya ce da ki ke ja da Hukuncin Ubangiji salamatu.?
Yadda ya ke fad'an ne yasa Umma durkushewa a gabansa cikin rawan murya tace"Baba ka tsaya ka Saurareni."
Cikin daga murya yace"To ina sauraranki, fad'i abunda ke bakin ki."
Gatse ya yi mata ammh bata gane ba cikin Rawan baki ta fara fad'in"Baba yaron nan fa aure yaje ya yi a Boye bamu sani ba?
Kai Tsaye yace"Shine mene?
Kallonsa ta yi cikin mamaki bakinta na Furta"Baba.!
"Nace shine menene don ya yi aure baki sani ba, sai daga baya kika sani?
Sai Umma ta maida kanta kasa ta riga daman tasan mahaifin nata bayan Sadiq zai bi.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.