Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 37 of 86

Cikin fad'a Mallam zakari ya cigaba da fadin"Ke Sakarcin ki bai baki yakamata ma ki godema Allah ba, in da ace yau matar bariki ya samu fa ko da kin ji Labari kina da yarda zaki yi ne? Ko kuma ace cikin da ke jikin Matar ba ta hanyar aure ya same shi ba? Sai ki ce kuma mene a wannan Lokacin Salamatu?
Ya fad'a yana kureta da ido Umma sai kuka Innaani na gefe tace"Haka ma Sulaimanu yace min da zai min nasiha shiyasa na yi shu da bakina.".
Mallam zakari ya kalli Innani ya na fad'in"Ke ma ai naga laifin ki Tsohuwa, kema ai uwa ce ga salamatu har da shi Sulaiman din, in suka yi ba daidai ki had'a su ki yi musu Hukunci, ammh sai ki barta ta na azabartar da yaro kan hanyar gaskiyarsa, kuma ma abun haushin duk kuna zaune kuna kallonta yanzu ba domin yaron nan ya yi Hankalin zuwa ya gayamin ba. Da sai abu ya kwabe ya lalace sannan zan sani."
Innani na jin haka kawai sai ta saka kuka har da Cire gilashi ta na fad"in"Ni ina ruwana, mi ye nawa? Na zabi yin shuru ne tunda abu na tsakanin bare da na gida, in na saka baki a kan lamarin sultana sai Magajin gida yace ina ja da Hukuncin Ubangiji in kuma na saka baki na goyo bayansa sai ace naki na gida na Fifita bare, in kuma na yi shuru da bakina shima bazan tsira ba."
Kawai sai ta fara jan Hanci ta na cigaba da fadin"Kuma salamatu naga ranta ya baci, kuma tsakani ga Allah d'anta ne kada na cika saka baki taga kamar zan nuna mata iyakarta ne, sannan shi kanshi Sulaimanu bata ji mganarsa ba ballatani, ni a suwa? danwake ya shiga hotel ai bazata ji mgana na ba, shiyasa na koma gefe na yi Shuu da bakina kaji dai dalilina ni kam a daina ganin laifina."
Ta karishe fad'a ta na share Hawaye da Haban zaninta.
Malam zakari yace"To shikenan ni yanzu zan ci Mutumcinta, in ku ta raina ku ni bata isa tace zata kawo min wargi ba. Bar ganin kin tara ya'ya da jikoki sai na kwade'ki anan wajen Tunda sakara kike kin girma da tunanin da ko yaran ki na tabbata ba zasu aikata abunda kike aikatawa yanzu ba."
Umma dai ba baki sai shesheshekan kuka ta ke yi gwanin ban Tausayi ita tana gani ta na kan gaskiyarta an ki sauraranta
Mallam zakari kuwa Abba ya shiga yima fad'an me yasa ya Biye ma Umma ta na wannan Shirmen.
Abba ya gyara zama yana fadin"Na yi mata uzirin sanin halinta, na barta ta nuna Fushinta tunda ita uwace ammh ban dauka abun nata zai zarce zatona da Tunanina ba."
Mallam zakari yace"Ai kaji inda aka samu matsala, ai su mata ba'a kyalesu ace za'a ga iya gudun ruwansu wlh kana zaune sake da baki sai su wuce Tunaninka  kamata ya yi tun farko ka tka mata Burki ka nuna mata kai ne sama da ita ba ka zauna ka saka mata ido ta na abunda taga dama ba."
Abba dai sai ya fara ban Hakuri, mallam Zakari kuma sai ya koma kan Umma ya na ta yi mata fad'a ta inda ya ke shiga bata nan ya ke fita ba.
Fad'i ya ke yi"Ke bazaki godema Allah ba, Allah ya baki duka yara natsassu, ba wani mara ji a cikin su, menene abun damuwa saboda ya  yi aure baki sani ba? Naji bai kyauta ba Boyemun ku da ya yi, ammh kuma da kika sani me ya kamata ki yi? Ba sai ki godema Allah tunda auran ya yi ba, ki zauna da Danki ku fahimci juna ammh sai ki zauna kina wani shanshanci wai har kece kike fad'in wai sai dai ya zaba Tsakanin ita yar wajen naki da ita matar nasa? An ya salamatu kina da aldaci kuwa a Rayuwaarki? Kuma kina son ki gama da Duniya lafiya kuwa?
Sai Umma ta kara karfin kukanta cikin rawan murya tace"Baba baka san irin yarinyar da ya aura ba ne shiyasa ka ke goyama yaron nan baya."
Mallam Zakari yace"Bansanta ba, kaji min wata mgana jiya nan suna gidana na ganta har mun yi mgana da ita yarinya karama miye laifinta? Sannan ta na Dauke da ciki abun Tausayi ko ta haka bazaki tausayamata ba, tunda ai kema uwace kinsan komai."
Umma tace"Baaba Matar fa an ce fa farar kafa gareta sannan bakar Annoba ce, shi kanshi Sadiq din ya sani duk wanda ta aura ko ya rasa lafiya ko Dukiya ko rai to Baba wannan matar abar so ce? Ai in nace ya saketa ban yi laifi ba."
Mallam Zakari ya yi shuru ya na kallon Umma cikin mamaki kafin ya kad'a kai yana fadin"Eh na shaida ba shhakka, ashe duk ilimin da na baki kin yi watsi da shi, a wani Nafsin akace akwai farar kafa a musulunci? Sannan ita Allah ce da zata Talauta mutum ko ta kashesa! Kaji wani banzan Tunani wajen salamatu Tunani irin na Jahilan farko da ba su san addini ba"
Ya fad'a cikin takaici Abba na gefe yace"Shi na gani, to Ubangiji shine fa komai, ta yaya don wani abu ya Faru da wani sai ace kuma wani ne ya yi masa  kaga ai an kauce ma sanin Allah ta wannan bangaran"
Cikin fad'a ya karb'e da fadin"Tuni ma an kauce ma Fad'in Allah da Monzonsa sannan Tauhidi ya yi Targad'a, babu iklasi kwata kwata a al'amarim salamatu."
Umma na sharan hawaye tace"Baba kuma fa bazawara ce, auranta Biyu kuma an ce duka mazajen sai da ta nakasu sannan ta rabu da su, ina zan saka kaina in na rasa Sadiq shi kad'ai gareni namiji kwara d'aya tak shiyasa nake yin wannan abubuwan saboda kare lafiyarsa."
Mallam Zakari ya katseta da Fad'in"Kafin ki samu Sadiq din a baya kin san zaki same shi?
Nace kin san zaki same shi?
Umma sai ta girgiza kai cikin fad'a ya cigaba da cewa"Baki san zaki same shi ba Allah ya baki shi, to kin isa ki hanashi ya kwace shi Lokacin da ya ga dama ne? Kuma da kike fadin kina yin wannan abun ne saboda kare lafiyarsa wacece ke da zaki iya kare lafiyarsa, ko daman chan ke kike Tsare da lafiyar tasa? Salamatu kina wani abu kamar mara ilimi Allah ne kad'ai ke tsare da bayinsa ba wayon mu ba, kuma ba Dubaran mu ba ke baki isa ki zama kariya ga Rayuwar Abubakar ba Tunda ba tare kike yawo da shi ko da yaushe ba  kuma da kike wani izgilanci fad'in bazawara to sai me? Su zawarawa ba Mutane ne ba ne? Ko su ba su da rai ne? Ki shiga Hankalin ki fa, ke da kike ganin kanki a gidan mijin ai baki wuce a yanzu ki zama bazawarar ba"
Da Sauri Umma ta Dago ta na kallonsa Lokaci daya ta na nuna kanta da fad'in"Ni kuma Baba?
Kai Tsaye yace"Eh ke fa, kin wuce  ki zama bazawar ce? Kuma kada ki manta ke uwace kina da ya'ya mata Rututu suma acikin su baza su wuce kaddaran haka ta faru da su ba sai naga yadda zaki yi, tunda zawara ne su, bazasu kara auruwa ba."
Umma sai ta kara saka kuka Mallam Zakari kuwa bai barta ba sai da ta yi masa alkwarin taji kuma In sha Allahu zata gyara.
Ba zata kara cewa ya zabi daya daga cikin matansa ba, sannan zata cire bakinta a sha'anin matan Abubakar in kuma ya kara ji to ranta sai yafi haka baci.
Umma bata da mafita sai ban hakuri ganin yadda ya Dauki zafi.
Suna zaune yana kara yi ma ta nasiha ganin ya dauki zafi da farko yanzu kuma sai ya koma nasiha da lallashi.
A lokacin a ka kira Abba a waya daga chan Abuja ma'aikatar Da Sadiq ke aiki.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.