Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 83 of 86

Wannan karon a Abuja na Haihu ammh kuma a Gusau aka yi taron suna. Kuma na haihu da kaina batare da an sake Farkani ba
Ban samu macen da na dinga kwad'ayi ba namiji na kara haifa.
Assadiq kuma ya saka masa suna TAHIR.!
Tahir ya yi murna Farincikin da ya Hauwa'u ta yi min sati a Gusau ta kuma zo min da kayan arziki daga Takwaransa Tahir Yusuf Daura.
Tahir da ya zo barka ya Dauki takwaransa ya rike cikin Farinciki yace"Abokina me na yi maka da na Cancanci ka Tsallake sunayen mutanen da suka fi daraja ka saka ma d'anka sunana?
Kai tsaye Assadiq yace"Da taimakon ka na auri Siya, Tahir ka yi min komai da  bani da bakin da zan gode maka."
Tahir kamar ya yi kuka yace"Me na yi maka! Ni da na rika adawa da auran ina ta cewa baku dace da juna ba, ashe muna namu Allah ya gama nashi ashe ashe har Takwara ma yar Zabiyar matarka zata Haifa min Nagode kwarai Allah ya raya Junior Tahir yasa ya Biyo mai halinsa."
Assadiq na jijjjiga kafad'ansa yana fad'in "Ameen ammh dai ka kara sani sunan Matata Hasiya ba Zabiya ba."
A tare duk muka saka musu dariya ni da Hauwa'u.
Kowa yaji sunan yaro sai yace Tahir ya cancanta.

A gusau na yi jego na Umma da Mama na Tsaye kaina suna kula da ni.
Sai dangina suka zo nan gusau karon Farko da su Adda Fati suka tako gidan su Assadiq.
Wajen kwanansu hud'u sun kuma ga karamcin da mutuntatawa.
Ramatu ta zo har da Inna Talatu itama Habiba ce bata zo ba tunda ta jima wajen Amma.
Bani da matsalan komai ina Bangaren Assadiq Sajida na shigowa ta zauna dani mu yi ta hira kamar bamu tab'a fad'a ba.
Assadiq kuma na tare da matarsa yar Rigima, Sultana dai bata samu ciki ba ta gama rigimamta ta Hakura.
Ammh har yau har gobe ba wani jituwa tsakanina da ita.
Ni kuma in muka had'u ni ke fara gaisheta ko da bazata amsa ba.
Daga baya da taga ina tura mata Aniyarta sai ta dawo tana gaisheni in muka had'u ammh shima ba koda yaushe ba.
Wannan karon na tada ma Amma Rigima sai da tazo har Gusau ta ganni ita da Matar Hamma Isuhu da Habiba da Badd'o
Umma ta yi musu kyakyawan karb'a.
Sai anan taga kammanina da Amma.
Ta ga inda na Dauko hasken Fatata kamar ita jajir.
Duk da yanayin Rayuwa da yasa Hasken Fatan Amma ya dishe ammh har yanzu da haskenta sannan Zanenta na Fulani na nan a gefe da gefen bakinta.
A bangaren Umma ta sauka nan Taga su Asim sun girma da suka ganta sun manta da ita sai da suka kara ganinta sannan suka fara yarda da ita.
Umma da ta kai Amma bangaran Innani tace mahaifiyata ce.
Innani na saman kekenta ta rika sakama Amma albarka ta na fadin ni alheri ce ga Rayuwar magajin gida.
Amma bata so ta jima ba kwana Biyu ta  sobsu yi su koma na lallab'eta ni da Assadiq ta amince zata yi sati.
Anty Surayya ta zo ta gaida Amma kuma har girki ta yi ta aiko mata dashi.
Ana gobe Amma za su tafi, yan'uwan Saurayin da ya ke son auran Sajida suka zo har gida har Falon Umma suka yi tijaransu.
Da sunan cewa su dan'uwansu bazai auri bazawara alhalin bai bata aure ba ita kuma Sajidan suka ja mata kunnin ta rabu da d'anuwansu ruwa ba sa'an kwando ba ne.
Tana bazawara sai ta makale ma Saurayi tace zata aura ko kunya bata ji ba?
Umma da ta yi musu magana tace ai hakan ba Haramun ba ne.
Wata cikin su ta kalleta kai Tsaye tace"Malama Rufe ma mutane baki, kinsan da haka nan da d'anki ya auro miki bazawara ki ka tada tsiyan sai ya saketa? A she wanzami baya son Jarfa ita wato ba yar ki bace tunda yanzu yarki ce kin ce ba Haramun ba ne mana."
Sai Umma ta yi shuru ta koma ta na kuka Sajida ce tace su bar musu gida in Allahu ta rabu da Isma'il tunda abun ya zama haka.
Har da Amma a masu ba ma Umma hakuri tunda suna wajen aka yi ni sai daga baya Sajida ta zo ta na fad'amin.
Umma ta yi ta kuka ta na fadin alhakina ne ya kamata.
ta tozartani da Farko gashi itama abunda ta aikata ya na dawo mata a kanta.

Har Amma ta yi ta bama Hakuri akan abubuwan da ta had'a kai da ya'yanta suka yi ta min harda na korana Lokacin da na ke da cikin su Asim.
Amma tace mirmishi kafin tace"Ni Hasiya ba ta tab'a gayamin kun yi mata wani abu ba, koda yaushe alherinku ta ke fad'amin na rantse da Allah ban da yanzu da kike fad'amin da bakin ki bansan da Labarin abubuwan da suka faru ba, ta Boye sirrin auranta ta zauna lafiya mu ma ta bari zukatanmu sun zauna lafiya."
Umma ta yi ta mamakin halina ta kuma ta yabona a gaban Amma.
Har Amma tace mata"Hasiya ta dabam ce acikin ya'yana mai Raunin zuciya ce ammh kuma mai kirki daga da yakana daga cikinta."
Sajida ke ta maimata komai ta karishe da fad'in"Yanzu kina nufin har koran nan da muka yi miki ba wanda kika fad'amawa?
Tab a gaisheki Hasiya."
Ina mirmishi nace"To miye amfanin na yi ta gaya? Yanzu ba ga shi komai ya wuce ba, da ace na yi ta gayamusu duk wani abun da ya faru da ni sai na yafe muku su kuma su rika ganin ku da abun su kuma kasa mantawa."
Sajida ta jinjina kai kafin tace"Hakane na dauki wannan dabi'ar in sha Allahu ina na samu na yi wani auren zan zauna lafiya da mijina sannan na Rike sirrinsa kuma na daina kokarin shiga Rayuwar auran wasu."
Sai hawaye ni na zauna ina ta bata baki da komai taga ya faru daga Allah ne.
Sai ranar da su Amma za su tafi Sultana ta zo gaisheta kuma Assadiq ya gayamata ta rika cewa saboda makaranta.
Kuma Naja fa ta na wajenta Saboda Sultana Assadiq ya nemi alfarma aka basu ita har sun sakata a makaranta.
Amma ko a fuska ba ta nuna ma Sultana wani abu ba.
Ta dauki Ummi ta na yi mata wasa har da Goyo kunya yasa sultana ta kasa mgana.
Ta ga duk rashin mutumcin da ta ke yi min uwata ta zo ta na wahala da Yarta.
Shiyasa na ganta cikin masu Rakiya Abba ya ba da Mota aka kaisu har Zariya Umma ta bata atamfofi harda Hijabai Mama ta yi musu alheri Abba kuma 20k ya ba su.
Naji dadi sosai bakina yaki Rufuwa abun akwai dad'i kaga an yi ma naka wani abun alherin.
Zariya Amma ta wuce sai da ta kara kwana Biyu sannan ita da matar isuhu da Badd'o suka koma gida.
Hankalin Amma ya kwanta na samu Rayuwar da ta ke yi min Fata Fiye da Fatan ta ma da Tsammaninta.
Ni kuma wajen wata Biyu na yi a gusau sai Junior ya fara wayau sannan naje Zariya na yi ziyaran yan'uwana da kawayena.
Daganan na wuce naga Amma na kwana d'aya na wuce Abuja daganan
Tunda Assadiq ya rigani tafiya shi ya tafin ma da wasu kayan.
Ina da sati biyu da dawowa muka je katsina gidan Tahir muka yi musu wekeend naji dadin zuwana katsina sosai.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.