Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 84 of 86

Mun zo har Daura na gaida Hajja Tana ta tambayan Innani Assadiq yace tana lafiya.
Na tuna sanda Assadiq ya kai mata Tahir Lokacin da aka haifeshi ta shafa kanshi tace"Ka yi ma Attahiru takwara saura ni Magajin gida, in ka kara samun mace ka saka mata suna ba Hadiza saboda ko bayan raina ku rika ganinta kuna tunawa da mai suna na"
Innani ita gani ta ke yi mutuwa zata yi ko Rasuwa aka gayamata daga Yan'uwa a shinkafi sai tace sai mun zo Allah yasa mu dace.
Sai da muka dawo daga Katsina muka yi mgana da Hajiya Surayya deee na tura mata kudin ta aikomin da tsumi da kuma kazar had'in uwar gida.
Ta kuma had'omin da saiwowin maganin Sanyinta Sadidan masu kyau da inganci +234 803 277 3332.

Da ya ke Umma ta ba ni wasu na sha acan Sannan Anty Sakeena ma ta kawomin gumba na sha da Nono kuma na yi amfani da su.
Shiyasa da Assadiq ya rab'eni yace Romon siya ya kara zak'ak'wai.
Madallah da Surayya Dee madallah da Saiwowon Kazar Gudiyo da Yabi.
Tunda naga na samu natsuwa Su Asim da alamu dai sun zama yan gusau nima sai hakan ya fi min dad'i.
Junior ba shi da rigima in na yi masa wanka yaji Ruwan zafi shikenan sai barci.
Assadiq kuma na wajen aiki sai na Tattara hankalina na maida shi kan Rubutun da na fara ina so naci karfinsa.
Da karfin gwiwan mijina da taimakonsa tare da shawarwarin marubutan da na nema kan Rubutun na kamallah Rubutun bayan daukn Lokaci mai tsawo.
Wanda daga baya har sai da na Sare kamar na hakura sai kuma Assadiq yace tunda na fara na karisa.
Sai da na gama Tas duk na Tura musu suka Dubamu kuma suka yab'amin sosai.
Auntysis ta yi min sharhi mai Tsawo sosai Anty Habiba kuma tace Rubutun da na yi bata tab'a  tunanin zan iya yin shi ba sanina da ban tab'a Rubutu ba.
Surayya Dee ita ta taikamamin da Editing ta gyaramin ka'idojin Rubutu a cewarta Rubutun zai amfani al'umma zata taikamamin ya fita yadda zai zama mai kyau da amfani wajen al'umma.
Assadiq ya bani shawaran na nemi cikin manyan marubutan maza ko da wata Shawaran da za su taimakamin da shi.
Sai na bashi damar haka, bayan na Tambayi Lambar ALHAJI AHMAD ADO GIDAN DABINO.
Na bama Assadiq ya kirasa ya yi masa bayani mutum mai barkwanci da ba ma mutane Lokacinsa.
Da yardan mijina muka Tattauna da shi ya yi min jinjina sosai sannan yace zai fanshi Copy 10 in na Buga in sha Allahu.
Sannan watarana in na Shigo kano zamu had'u zai taimakamin da wasu daga Cikin Littafansa da za su kara taimakamin sukara karamin kaifin kwakwalwata
A lokacin dariya na yi kafin nace"Ai bazan kara wani Rubutun ba, wannan ma saboda labarin Rayuwata ne shiyasa na Rubuta."
Shima Mirmishin ya yi min kafin yace"Na duba Rubutun ki, kuma na yaba miki ina da kyakyawan yakinin a nan gaba Mutane za su karu da Basirarki."
Da ya ke na Tura masa shima ya Duba min tare da gyaramin inda ya kamata.
A kano suka shigemin gaba na Buga Labarina mai taken TSAKA MAI WUYA.(LABARIN HASIYA)
Wacce HASIYA MAMMAN KONA TA RUBUTA.
A kasa kuma na saka (MATAR ASSADIQ).
na kuma yi sadaukarwa ga Mahaifaina guda Biyu, Alhaji Mamman mammadi kona da Mahaifiyata Hajiya Aisha Jari Mamman.
Sannan nace littafin Babban Tukwaici ne ga Mijina Babansu Asim ABUBAKAR SULAIMAN ABUBUKAR SHINKAFI(MIJIN SIYA).
Na gaida yan'uwana da kawayena da suke tare dani daga Farko har karshe.
Alhamdulillah ba abunda zan ce ma Allah sai godiya.
Assadiq ya Dauki nauyin Buga littafin Copy 200, Tahir ya ce ya fanshi ma Hauwa'u copy goma.
Adda Fati ta fanshi biyar ita da Adda Rukayya.
Ramatu ma haka ita da Safiya.
Abba ma da Assadiq ya gayamasa yace abu me mai kyau ya famshi Copy 30.
Duka yan'uwan mijina sun fanshi Littafan nan kuma sun tayani yawo dashi domin ya samu karb'uwa cikin Sati Biyu wanda aka Buga duka ya kare, kuma ni da farko a kyauta na so na bayar da shi Assadiq yace a'a na amshi kudi ko ba da yawa ba.
An sake Bugawa sannan kuma ya shiga Hannun mutane ta dalilin yan'uwan mijina da yan'uwana Tunda suna harkan jama'a.
Sannan Marubuta ma sun yi min kokari sosai.
Na kuma gode musu, sai bayan da na Fitar da Hardcopy da wattani uku na Fitar da Sofy copy din shi ta Kafafen Sada zumunta.
Ammh Shi a kyauta na ce a yad'a shi kuma Kyauta ne na musamman ga mata da suka Fuskancin kalubale kwatankwancin irin nawa.
Da yakinin cewa suma za su samu Kyakyawan Rayuwa anan gaba kamar yadda na samu.
Sannan da fatan Mutane za su daina kyamarta irin mu da kaddaran kan fad'a mana sai a kiramu masu farar kafa ko wani abun da ba shi acikin Addini.
Su kuma san cewa wani abun ba Aljanu ko mutum ba ne, komai daga Allah ne, sannan duk wani abu da zai faru daman ya na bukatar SANADI kamar yadda ni Hasiya na zama Sanadin Rasa dukiyar Abubakar tare da Rasa lafiya a bangaran Salisu.

Sannan da kara ma zawarawa kwarin Gwiwan cewa suma mata ne, kuma masu galihu kamar sauran mata.
Da kuma nuna ma duniya cewa Zawarawa ba kilakai ba ne sannan ba Yan duniya ba ne, kuma ba'a son ransu suke zama zawaran ba da yawan mu  kaddarace ta ke fad'a mana

*******

*MURFI.*
*BAYAN SHEKARA D'AYA.*
*BBC ABUJA.*

Assadiq ya rakoni ofishin BBC da ke Abuja  inda suka kirani sun gayyaceni za su yi Hira dani.
Tare da Junior muka zo, sai kuma karamar jaririyar da na haifa ko arba'in ban yi ba wacce ta ci sunan Innani Hadiza muna kiranta Afra.
Sanye na ke da wani less golden Mayafin jikina da takalmin kafata duka Golden ne.
Ba kwalliya na yi ba tunda ban saba ba.

A shekara d'ayan da na Wallafa labarina na TSAKA MAI WUYA.
Ya Zaga duniya ya shiga in da ban taba Tunani ko tsammani ba.
Na samu kira kirayen waya akan matan da suka fuskanci Tozarci akan Zargin Farar kafa ba adadi.
Da wad'anda suke kan fuskantan haka, sannan na samu matan da sanadin zawarci ne suke fuskantar Tsamgwama daga mutane da cin mutumcin barin ma in suka samu miji saurayi ko wamda bai da shekaru zasu aura sai a rika kiransu masu kwacen maza.
Matsaloli ga su nan wasu su sakani kuka wasu kuma su tunasar da ni Rayuwata ta baya.
Lokacin da Ma'aikacin Bbc ya ke min tambayoyi, ya tambayeni shin da gaske ne wannan Labarin da na rubuta Labarina ne?
Ina Mirmishi nace"Tabbas Labarina ne, sai dai na Boye sunayen wasu da kuma sauya  hallaya  wasu da garuruwa ammh tabas ni ce wannan Hasiyar ta cikin Labarin TSAKA MAI WUYA, wacce ta fuskanci Tozarci da kyamar al'umma saboda Canfin ina da Farar kafa, kuma ni ce na fuskancin Tashin hankalin kirana da wasu suke yi da sunan Mayya da sunaye marasa dad'i.
Sannan ni ce wacce na yi aure har Biyu ta dalilina mazajen da na aura suka samu rasa lafiya da asaran dukiya, ni ce wacce duk wanda na Rab'a sai ya shiga Tsaka mai wuya sai na raba tashin hankalinn Rayuwata tare da shi."
Dan jaridan ya tambayeni yadda na rika ji in kirana da sunan mayya ko mai Farar kafa?
Sai naji hawaye sun kawo cikin idanuwana.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.