Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 52 of 86

Shiyasa na yi masa Mirmishi nace"Ai komai ya wuce yanzu in sha Allahu."
Kamar  dai ba haka ya so ba, Sai dai bai kara mgana ba, ban wani jima ba daganan na biya gidan Goggon kona muka gaisa ita kam sai faman bugun Ruwan cikina ta ke yi taji halin da na ke ciki da yan'uwan mijina ni kuma ina ce mata komai lafiya.
To ai taga haka dagani har ya'yana muna cikin kama mai kyau ba ma cikin wahala.
Sai da na tabbatar da naje gidaajensu na gaishe su kamar yadda Amma ta bani umarni, har gidan su Safiya naje na yinin mata, Domin ai Safiya kawar Amanace sannan ta zauna a gida na fara shan mganin gyarana da akq aikomin daga kano.
Tunda a satin Assadiq yace min wajena zai sauka sai faman rawan jiki ya ke yi min nasan kuma ba sauki Shiyasa na dagee ina ta amfani da mungunanan kuma naji dadin su sosai.
Kafin ramar jumma'a sai da na tabbatar da nayi zam, ni kaina naji ina son kasancewa da mijina da yammah ya iso, Habiba da rana ta koma gidan Adda Fati ammh kafin ta tafi sai da ta tayani aiki na yi masa girke girke masu dadi da lemuka.
Tuwon shinkafa miyar a gushi da Tokfish, da ganda sai zobo da kunin Aya.
Allah yasa yau su Asim naji abun arziki ba su yi min rigima ba Tunda na yi musu wanka suka ji ruwan zafi sai barci.
Har ya dawo ba su tashi har sai da ya yi wanka ya ci abinci sannan ya tada su da kanshi yana yi musu wasa.
Yara nan kamar su san babansu ya Dawo ba su yi mana kukan dare ba.
Suka bar Babansu ya sha Shagali.
Da asuba ne suka fara kuka sai na Dauke Asim na fara bashi Nono shi kuma sai ya Dauki Asif yana lallashinsa.
Ni ce ina dariya nace"Yara nan sun bani mamaki, ko kukan daren da suka saba mana yau ba su yi ba."
Na tuna ranar da ma kai su allura irin kukan da suka kwana suna yi mana.
Mirmishi ya yi kafin yace"Yaran albarka kenan, baza su takurama Abban su ba"
Yaso ranar muje gaida Amma, ammh sai na rokeshi in ya kaimu ya barni na kwana biyu a wajenta shiyasa sai ya bari sai Ranar litini ya kaini daganan ya wuce Abuja.
In na gama kwanakina sai na dawo, kuma hakan ce ta faru weekend din nan tare muka yi shi, ni da mijina da ya'yana.
Shi ya ke tayani Renonsu kamar kada ya tafi, ina jinsu wani Lokacin suna waya da Sultana, ni ma kuma ina waya da su Anty Surayya Anty Saddiqa da Saliha.
Sai Anty Sa'ima da Umma da tafi kowa kirana yanzu Saboda Darajan su Asim.
Muna hanyar zuwa wajen Amma ya ke fad'amin yaushe ya kamata na Shirya tafiya gusau.? nace masa kafin dai a koma makaranta Saboda Tp na
Sai yace wannan ba matsala  ba ne sati daya dai ai bazai zama abun damuwa ba.
Mun isa da wuri tunda da safe muka kama Hanya Suprise na yi ma Amma sai dai kawai ta ganmu kamar daga sama.
Ta yi murna sosai ta rasa ina zata sakamu Saboda Farinciki, Barin ma Assadiq da ta rika yi masa barka da arziki.
Shima dalilin yi mata gaisuwan Adda yasa ya zo, sannan da kuma kawo mu ni da yara bai wani jima ba ruwa kawai ya sha ko lemun da Hamma Isuhu ya kawo masa bai sha ba.
Ya yi ma Amma gaisuwa tare sallama sannan ya tafi, 10k ya ba ma Amma ta yi ta godiya ita ai ganina cikin Farinciki ya isheta komai.
Na rakasa har mota su Asim na barci sai dai ya yi musu Rumguma daya bayan daya da Sumbata.
Nima haka ya rumgumeni ya sumbaceni cikin kauna kafin mu yi sallama da cewa sai mun yi waya.
Daganan Abuja ya wuce tunda Hanya ce.

Ni kuma ya barni wajen Amma ta da naji kamar an sakani a cikin aljannah.
Amma tunda muka zo ita ke wahala da su Asim Allah sarki sai fadi take yi"Allah ya sa ina raye gashi ina Goya ya'yan Hasiyata a bayana. Allah ya jikan Adda ta sha fad'amin kema watarana zaki ji dadin aure kamar kowata mace."
Sai ga Amma na hawaye sai na koma lallashinta.
Na zo mata da Sabulan wanka da na wanki da su omo sannan cikin kayan sunan da na samu na kawo mata leshi daya da Atamfa.
Amma na ta godiya tana kara godema Allah Hasiya ma ta samu Farincikin da ta ke mata fata.
Kwana Biyar na yi a wajen Amma sannan Hamma Isuhu ya kaini tasha ya sakani a motar zariya.
Ina mota ina Tunanin Hirar mu da Amma, ni na bata labarin irin yadda Umman Assadiq ta ke kirana saboda su Asim sannan yanzu ma ta matsa sai na je gusau.
Ammh tace na shirya naje, Sannan daman ta jima tana kai kukanta ga Allah, akan Allah ya dora kaunata a zukatan yan'uwan mijina ko Saboda Darajan yaran nan kuma tana ji a jikinta Allah nee ya amshi addu'arta.
Ta bani shawaran na yi hakuri na maida kaina wajen biyayya ga Mijina, sannan na bi yan'uwansa sau da kafa sannan in zan je na je musu da wani abun saboda alheri da kyautatawa na da dad'i.
Da wannan na fara Tunanin abunda zan kai ma Umma da Abba ga Innani ga Mama, Amma tace har Sultana in naje na yi mata alheri bakomai taci Darajan Abubakar.
Washegarin ranar da na dawo Assadiq ya kirani yace min yau gusau zai je, saboda haka na shirya sati mai zuwa zai zo ya Daukeni zuwa Gusau achan sai barni na yi koda sati daya ne
Ban yi musu ba nace Allah ya kaimu, daman tunani makaranta ne, sai kuma na lissafi naga a satin ne za'a koma zan iya zuwa na dawo kafin karatu ya kamkama.

******

Gusau.

Kamar yadda ya fad'ama Hasiya Ranar jumma'a ya baro Abuja zuwa Gusai, Ya samu kyakyawan Tarba wajen Sultana kamar yadda ta nuna ta sauya shima sai ya nuna mata ta na da fa da matsayi itama a rayuwarsa.
Cikin Farimciki suka kwana da Safe tare da ita suka je gaida su Umma suka dawo kuma tare.
Abunda ya lura ta rage fara'a saboda tun suna falon Umma da taji Umma na tambayan yaushe Twins za su zo mata ne taji shuru, yace sati mai zuwa zai je ya Daukosu Umma ta fara washe baki tana fara'a.

Abunda ya bama sultana Haushi Umma yanzu hankalinta na kan ya'yan da tace ba ta so, ammh yanzu ita ko damuwa da ita bata yi, har complain taje ta yi mata da cewa ko za su je asibiti ne ciki har yanzu ita bata samu ba, Umma tace wai ta kara Hakuri yaushe duka duka ta koma?
Sai kuma daman su Anty Sajida suna gayamata Umma yanzu son ya'yan nan ya Rufe mata ido bata ganin bakin Hasiya yanzu ta ma daina Zaginta.
Shiyasa tunda suka dawo ta ke masa cin mgana shi kuma sai ya kyaleta bai biye mata ba, shi ke janta ma da Hira ta na wani basarwa.
Sai da rana da ta yi musu abinci tunda yanzu tana gida sun gama jarabawa.
Suna kan Dining suna cin abinci ya kalleta yana fad'in" Siya zata zo kawo ma su Umma  yaran nan su Asim saboda haka zata sauka anan Acikin dakunan ki.  ki zab'a mata guda dayan da zata sauka aciki."
Cikin Mamaki sultana ta kallesa kafin tace"Nan gidan wai ka ke nufi?
Cikin shima mamakin tambayarta ya kura mata ido kafin yace"Eh nan gidan na ke mgana, ko ina da wani gidan da ya wuce nan ne"
Sultana ta tura bakinta gaba kafin tace"Tabdijam ni ai bani da masaukinta a gidana."
Hancinsa a bude yace"Bangane ba? Gidan ki naji kin ce?
Kai Tsaye sultana tace"Eh mana tunda ai saboda ni Abba ya baka kyautar gidan saboda haka da gidan da abunda ke cikin gidan duka mallakina ne"
Tsabar mamaki ya hana Sadiq mgana, kallon Sultana ya ke yi yana kara jinjina karfin halinta.
Cikin dan mirmishi yace"Oh ko Mallam shitu ne ya siya miki gidan sai kika taimakamin na ke zaune nima aciki?
Sultana bata taba tunanin irin amsar da zata fito daga bakin Yaya Sadiq ba kenan.
Cikin mamaki tace"Ni? Mahaifina ka ke zagi Yaya Sadiq a kan wata banzar bazawar..!
Bata karisa ba taga ya mike da sauri ta matsa baya.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.