Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 7 of 86

Sai bayan azahar muka tashi muka yi sallar, shi ya fita ya siyo mana abinci da kayan marmari, ni kayan fruit din kadai na sha  suma ba'a wanye lafiya ba na yi ta amai, ya hadamin Tea shima na sha na yi amai, Tuwo nace ina so yaje ya siyomin Tuwon Semo miyar karkashi shi naci ya zauna a cikina.
Duk wasu kayan kwalama sun daina Burgeni, Da daddare kuma Tuwon shinkafa ya siyomin miyar kubewa da ganda, sanda naci lafiyata kalau ammh kwana na yi ina ta faman Amai da miyan yanzu ya yi yawa, shi Assadiq yadda na ke ta bushewa ne damuwarsa da kuma Aman da na ke yi yasa da Safe ya tasani gaba muka koma asibiti ganin Likita.
Bai yarda ba sai da likita ya karanta masa sai hakuri in cikin ya fara girma duk zan daina Aman sannan miyan zai Ragu, Ramar da na ke yi kuma kila Sanadin cikin ne, ammh zuwa gaba in na fara cin abinci sosai zan maida jikina.
Bai bamu komai ba, sai magungunan karin jini na masu ciki ya sake Rubamin, Yace maleria ya rabu dani zazzabin dare da na ke yi cikin ne ya na Tunanin in ya yi kwari duk zan dawo Normal.
Haka muka koma gida, ina kwance jiya da yazo da karfin jikina ammh washegari sai na kwanta kamar ruwa, kuma gashi gobe da Safe zai koma wajen aiki, maganarsa shine bazai barni ni kadai ba, gwara na koma gidan Adda Fati na zauna ko kuma Habiba tazo ta zauna dani.
Ni kaina ina son na Huta sai nace zan je gidan Adda Fati na yi ko sati ne daga baya in zan dawo sai na Dawo da Habiba.
Ga makaranta ma, da ya ke ya kunna min wayata, Safiya ta kira mun yi mgana tace an fara Test ya kamata na zo makaranta, shi kuma yace komai sai da lafiya na bari ko an wuceni na yi Difaring ni ko ina zan bari Yan ajinmu su yi gaba su barni.
Da kansa ya had'amin komai da zan bukata washegari da Safe sai da ya kaini gidan Adda Fati ya kuma barmin isassun kudi sannan ya hau Motar haya Zuwa Abuja.
Ita kanta Adda Fati  taji dadin haka Tun ballatana irin ramar da ta ga na yi, sannan taga laulayin nawa mai zafi ne.
Tunda Assadiq ya tafi a rana ban san adadin sau nawa ya ke kirana yaji lafiyata ni da Baby ba, kullum cikin cewa ya ke da naji wani abu na koma asibiti, ni kenan kullum tuwo da tsaki, Komai baya min dadi, kuma ban daina amai ba ga miyau, maganar gaskiya ina Laulayi mai zafi sosai.
Sati daya na yi gidan Adda Fati ta had'ani da Habiba muka dawo daganan Wajena ta ke zuwa makaranta.

Bayan tafiyar Assadiq sai da na yi sati Biyu sannan na fara farfadowa, na rage Amai sannan na daina zazzabin dare, kuma yanzu zan ci abinci ya tsayamin acikina na wani lokaci a satin ya baro Abuja bisa adalci ya sauka a gusai, ya gayamin ban nuna wani abu ba, Tunda itama matarsa ce kamar yadda na ke da Hakki a kansa itama ta na da Hakki a kansa.
Bai zo zariya ba sai da ya koma Abuja sai weekend Ranar jumma'a ya zo ya ganni, ranar da yazo Habiba ta koma gidan Adda shi kuma ya cigaba da kula dani.
Duk da dai naji sauki sosai, ni kuma na matsa masa ranar litini da ya tafi da Safe ni kuma na Shirya na koma makaranta naje na iske Uban Assigemt sannan an yi abubuwa da dama ba na nan, Sai dai Thanks to Safiya duk ta min wasu abubuwan sannan komawata ta na kokarin koyamin abunda ya wuceni.
Kullum da minti da cingam na ke yawo a jakata ko da kunzo Saboda Miyan bakina, ina shiga cikin jama'a akwai cutarwa saboda wani ya na da kyankyami.
Ramewa kawai na ke yi, sai dai na fara cikar Fuska dagani In ji Adda zan yi girman ciki mai kumburi Domin tun cikina na wata uku da wani abu ya bayyana ajikina, ga shi dai ina da Tsawo ammh Tsawo na bai shanye girman cikina ba, in na saka Hijabi in ban saka hannu na kare ba sai ya bayyana.

Ni da kaina na rage huld'a da Saliha, tunda itama taga ta na bi na ina basar da ita sai taja baya, duk da Assadiq yace mu cigaba da mu'amalan ba karya ba ne ni matar kaninta ne, ammh ni ce a karan kaina na kasa, sai na ke ganin kamar za'a samu matsala.
Ammh lokaci bayan lokaci mu kan gaisa ta waya ko ta chart.
Assadiq ya raba mana kwana ni da Sultana Tunda dukkanmu ba ma zaune waje daya da shi, sai yace duk bayan sati biyu zai fara zuwa ya sauka wajena, in ya koma ya yi sati daya, satin sama kuma sai ya sauka Wajen Sultana haka ya raba mana Tsarin kuma na amimce tunda sai da ya yi shawara da ni.

A koda yaushe in na yi masa maganar Lokaci fa na kurewa yasan hanyar da zai fad'ama su Umma game dani sai yace na kara masa lokaci har yanzu yana Tunanin ta wacce hanya zai saukaka Lamarin, ni kuma gani na yi cikina na kara girma ina Tsoron nan gaba abubuwa su kara Tsami.
Shi kuma Sadiq ya buga duka Hanyoyin samun mafitan ya kasa samu ne, kunya da wani irin nadama sun gama dabaibayeshi.
Ba zai iya taran su Umma da mganar ya auri wata matar shekaru uku da wattani batare da sanin su ba.
Ya zauna ya yi tunanin duk ya kasa samun mafita, Kuma ga shi ba abokin shawara, Tahir ne kuma yanzu yaja baya da shi ranar dai ya kirasa ammah a Dakile Tahir ya rika amsa masa shiyasa shima ya fita batunsa.
Tunanin abun yasa har rama ya fara rashin natsuwa ta fara bayyana masa a fuska.
A cikin irin Tunanin da ya ke yi sai ya yi tunanin Big sis Surayya, duk cikin yan'uwansa ya fi shakuwa da ita, kuma ya na mata kyakyawan zaton zata Fahimcesa, da yakinin zuwa ya gayamata abunda ya faru yaje gusai a satin, sun had'u a gida yace mata zai zo wajenta akwai mganar da za su yi, tace sai yazo anan ma agaban su Umma tace duk ya rame da Farko dai ya fara kiban Amarci.
Mama na wajen tace wahalan zirga zirga ce na jeka ka dawo, Umma ta yi karaf tace sultana na gama makaranta ya sama mata muhalli ta bisa chan sai dai bayan wattani in sunzo ganinsu.
Shi ko har ga Allah baya so Sultana ta bishi Abuja in hakan ya faru Hasiya fa? Kuma ga shi kad'an ya rage ya gama Masters dinsa shiga zariya zai yi masa Wahala  gaskiya.
Ana gobe zai koma Abuja ya shirya da Daddare da niyar tafiya gidan Surayya  ai Sultana na ganin zai fita ta makale masa sai yaje da ita, ba shi da zabi ya sakata a gaba suka je.
Duk yadda ya so ya yi mganar sai kuma yaji ya kasa, duk da Sultana ta ba su waje, ammh kuma guilt din abunda ya aikata yaki barinsa ya fad'ama Surayya komai sai kawai ya Bige da fad'amata in ya koma Abuja zai kirata a waya.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.