Tmw Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: TMW BOOK 3.txt
Chapter 79 of 86
Assadiq duk ya shiga damuwa Umma da taji cewa ta yi ya kawo mata ni Gusau har sai cikin ya yi kwari.
Ni kuma sai naga kamar shawaran bata yi masa ba, sai na yi magana da Adda Fati nace ko Habiba ta turomin ita ta zauna tare dani.
Ashe Habiban bata nan tana wajen Amma tunda suka gama Jarabawa.
Sai Adda Rukayya ce da taji ana Jajen yadda za'ayi ta ce ga Amna ta nan zata iya yin komai ta gama primary bata riga ta shiga makaranta ba.
Ban tab'a tunanin Babanta zai barta tazo wajena ba sai gashi ita Adda Rukayyan ta kirani da kanta ta na fad'amin Amna zata zo wajena ya za'a yi?
Ina kwance Lokacin kamar Ruwa Assadiq ya tafi office, ga shi ma yanzu sun fara tafiye tafiye saboda aiyyukan Titunan da suke yi ana tura wasu daga cikinsu wajajen da suke ayyukan Tsoron Assadiq kada Tafiya ta fad'o har da shi, gashi ni kad'ai kuma bani da lafiya.
Kullum acikin bargo na ke yini Saboda na rika rawan sanyi kenan, kai na kara jinjina ma iyayen mu mata Amma kuma kaunarta da Tausayinta sun kara ninkaya acikin Raina.
Cikin Dakushewar murya nace"Adda Babanta kuma ya barta ta zo wajena? Ko baki gaya masa wajena zata zo ba ne?
Cikin Sauri tace"Haba wlh ya sani na gayamasa, ai yanzu shima ya Fahimci duk canfi ne da mganar Mutane baki da wani matsala a tare da ke tunda yaga shaidar haka kina zaune gidam mijinki lafiya har kin fara gina kyakyawan Zuru'a."
Cikin jinjina kai nace"Allah Sarki! Nagode sosai, yanzu to wazai kawo ta? Kuma kamar ta yi karama ku sakota a mota?
Adda Rukayya tace"Babanta yace bazai yi gangancin Turata ita kadai ba, shiyasa na kira ki naji yadda za'a yi."
Jin haka yasa nace ta bari Assadiq ya dawo in na fad'a masa nasan shi zai san yadda za'a yi.
Haka ko akayi sai da ya dawo na gayamasa, shima sai da zamu kwanta Tunda in ya dawo aiki shi ya kan taimakamin na yi wanka sannan ya matsamin sai naci wani abu.
Ina kwance a saman cinyarsa shi kuma yana aiki Bisa Computer dinsa da ke gefensa ni Tsabar yanayin da na ke ciki na manta da wani Rubutun da na fara jama'a ana ta kai waye zai yi na kaya.
Kiran sunansa na yi ya amsa hankalinsa na kan abunda ya ke yi, ina fad'a masa ya kalleni kafin yace"Bansani ba gaskiya, ammh Tahir yace min za su zo shi da Amaryansa abunda za'ayu zan kirasa na tabbatar shin yaushe zai taho?
In cikin sati nan ne sai nace don Allah ya Biya ta Zariya ya Daukota tunda yace min a ranar da za su taho sai ya shiga kaduna."
Da shawaransa muka Tsaya a daran ma yaso ya kirasa na hanashi.
Cikin daure fuska yace"To uban me ya ke yi yanzu? In amarci ne ai ya gama cinye romon tuntuni."
Ina Mirmishin karfin Hali nace"Kada dai ka kirasa, in har kai da ka ke da ni baka gama shanye Romon ba, shima mai auren jiya jiya ai bai gama Cinye Romon ba"
Yana yar Dariya yace"Ina ta ko shan Romo na mai d'an karen dad'i. Ga shi nan sakamakon Romon ne ya nuna a jikin ki.".
Ya karishe fad'a ya na shafa jikina ni kuma na Ture hannunsa na sauke kaina a saman cinyarsa na maida saman Filo cikin Bushewar baki nace"Assadiq sai da Safe."
Saboda bakina yanzu sai ya rika Bushewa har yana fashewa ni dai wannan cikin naga Jalala kala kala.
Sai washegari da Safe ya kira Tahir ya na tambayansa yaushe zai shigo.?
Shi kuma yace abunda zai kaisa kaduna an daga sai wani sati.
Da Assadiq ya gayamin sai nace zan kira Adda Rukayya na gayamata Amna ta shirya sai ta jira Tahir din Sati mai zuwa ya biya ya Daukota.
Haka muka yi dole tunda ba wanda zai Taho da ita, Assadiq ya gayama tahir yace ba matsala ta zo gidan Adda Fati tunda yasan gidan sai ya Biya ya Daukota.
Yanzu tsakanina da Tahir sai gaisuwan mutumci da girmamawa Sannan zumunci na ke yi da Hauwa'u sosai kamar mun zama yan'uwa.
Allah ya taimake ni a satin Safiya ta kirani tace ta raka Mamansu Abuja bikin diyar kanwarta sun kawo Amarya nan cikin garin Abuja.
Tace ta na so tazo sai naji dad'i daman tasan bani da lafiya nan ta ke na Tura mata Address ba dad'ewa sai gata.
Ta yi jimamin halin da ta ganni, duk na tsumaye na rame kamar ba ni ba sai Farin Fata da ido.
Gabadaya kananun jikina sun kara bayyana daman can a baya gyaran jikin na kama sannan kuma cikin ma ba d'aya ba ne da na su Asim
Wanna daga gani in ban yi wasa ba kafin ya girma sai na zama abun Tsoro.
Ita da ta zo min bakunta itace ta Tube ta zage ta gyaramin gidana tas ciki da waje, Assadiq baya samun Lokaci sai Weekend wannan karshen watan ma saboda ni bai tafi Gusau ba.
Ina ji suna waya da Sultana ta na kananun mganganunta da ta saba.
Ya fad'a mata ina da Ciki kuma ya na wahalar dani zai tsaya ya kula da ni.
Nasan dai Sultana na can bakin ciki kamar ya kasheta.
Ta so ta tafi a ranar tunda tace gobe da Safe zasu koma Zariya ni na Hanata tafiya tunda ta kai Dare, har girki sai da ta yi min ta kuma matsamin na yi wanka.
Ni daman ban iya cin komai sai Farar shinkafa ba mai ba manja ba maggi
Hakanan na ke iya turawa in naji kamshin mai ko magi wlh ranar bazan kwana Lafiya ba.
Shiyasa da ta yi mai miya ni sai naci fara hakanan da Assadiq ya dawo shi kanshi yaji dadin ganin gidan da ni kaina.
Allah Sarki har ya Biya ya siyo abinci ni kuma ban yi hausan na kirasa nace kada ya siyo wani abu ba.
Sai fad'i ya ke yi"Safiya kin zo mana Bakunta muna ta saka ki wahala."
Kai Tsaye tace"Ni ai ba bakuwa bace ni yar gida ce, kuma lalura ce fa."
Ina gefen mijina nace"Tun da ta zo bata zauna ba, sai aikace aikace ta ke yi da na yi mgana sai tace ita ba bakuwa ba ce."
Assadiq yace"Gaskiya ne mun gode sosai Allah ya bar zumumci."
Ranar dai bata tafi ba sai da safe suka fita tare da Assadiq zai kaita kafin ya shiga Office.
Sai naji kamar kada ta tafi ammh ba Dama tunda mamansu na ta kiranta za su tafi da wuri, jin ma ba ni da lafiya ne yasa ta barta ta kwana kuma Safiyan ta bani ita mun gaisa ta yi min sannu.
Na gayama Amma bani da lafiya ammh ban gayamata ciki gareni ba, ita da kanta ta gane sannan sun yi mgana da Adda Fati ita ta gayamata zencen zuwan Amna wajena.
Amma ta kirani ta na cewa"Ko dai Habiba tazo wajen ki ne, ni nan ba wani abunda ta ke yi min naga zata fi Amna amfani tunda ta fita shekaru."
Ni kuma ganin Habiba bata taba zuwa ta jima wajen Amma ba yasa nace ta kyaleta kawai ai ba wani abun wahala ba ne Tunda Adda Rukayya ta bani Tabbacin Amna zata yi min komai in dai ba mai wahala ba ne.
Sai Amma tace shikenan Allah ya kara lafiya.
Kafin mu yi sallama sai da tace"Ina Mazajen nawa? Ba sa cefane kuma ba sa zuwa zence?
Ina dariya nace"Amma suna gusau ba su dawo ba."
Amma tace"Kin huta da yanzu ai aikin ya yi miki yawa"
Kai tsaye nace"Ai nace su yi zamansu can sai na warke Amma bazan iya ba ji na ke yi kamar zan mutu."
Amma tace"Ki bar cewa Haka Haseta. Haka kowani ciki ya ke da na shi Tarnakin Allah dai ya sauwake ya kuma Raba lafiya."
Sai naji kunya amsar ma a sannu na amsa ta.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.