Tmw Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: TMW BOOK 3.txt
Chapter 67 of 86
Kwana uku muka yi ranar Litini da Safe muka koma Abuja, sai kuma Bikin Tahir da shima saura wata Biyu har Abuja yazo ya ga inda muke.
Tunda Taron siyasa ya shigo da shi garin Ranar har wajen 12 na dare suna falo da Assadiq suna hiran su.
Yanzu Tsakanina da Tahir sai gaisuwan mutumci da girmamawa.
Mutanen Zariya kuma sai dai mu yi magana ta waya.
Hankalin Amma a kwance tunda ta na da tabbacin ina zaune lafiya da mijina tare da kyakyawan Rayuwa ni da ya'yana.
Bikin Tahir ya matso kuma Assadiq ya gayamin kila Sultana sai ta haihu kafin a yi bikin Tahir, ni kuma a raina sai nake fatan Sultana ta riga haihuwa in muka tafi gusau daga can muka tafi katsina Biki.
Tunda Ankon bikin ma ta hannun Amaryan Assadiq ya siyamin, Tahir ya bata lambata ta kirani na fad'a mata masearuement dina.
Shikenan sai muka fara gaisawa ta Chart, ta na tambayansu Asim tunda tace Tahir na Tura mata Hotonansu.
Hauwa'u Amarya ta gayama Angonta Katsina zan zo wajenta Biki, sai dai na bari in za'a kawota Daura na Biyota tunda anan babban gidansu za'a yi walima sai ta kwana Biyu sannan Mijinta ya dauketa su koma Katsina.
Assadiq yazo yana gayamin nace masa shikenan nima tamin mgamar nace sai abunda Mijin Siya yace.
Shi kuma yace mijin siya ya ba ta dama ta fara sauka katsina a sha Biki lafiya.
Ana saura Sati Biyu Bikin Tahir Sultana ta Sauka an samu mace, na ci Dariya Sanda Siyama ta kirani ta bani Labarin abunda ya faru a asibiti Lokacin da Sultana za ta haihu.
Tun naguda bata kankama ba ta kwanta ta na Raki Umma da Mama suka kwasheta sai asibiti.
Suna zuwa ta rika ce ma likita ita yan Biyu ne acikinta bazata iya haihuwa da kanta ba sai an yi mata C.S.
Likita ya fito yana gayama su Umma su Daya suka gani acikinta.
Sannan Mahaifarta ma bata Bud'e ba kuma zata iya haihuwa da kanta ammh tana fadin ayi mata aiki yan Biyu zata haifa.
Kuma Nurses sun sha Fama da ita a dakin haihuwa ta ki bude kafa ballatana su yi aikinsu ai ta dauka Haihuwan wasa ne sai da ta ganta zahiran ta gane bata da wayau bakinta ya Mutu.
Tana gayamin Umma na ta fad'a tana fad'in bata tab'a sanin sultana mahaukaciya ba ce sai ranar, Ita a tunaninta C.S din wani kayan gabas ne, ko kuma Haihuwan wani cin Tuwo ne ai da ta haihuwa sai bakinta ya yi murus sai ido ga shi ta karu ta sha Dinkin adadin kuka da Ihun da Sultana ta yi bai da iyaka.
Assadiq ko ya sha Allah ya isa yafi cikin kwando.
Tun ballatana da ta farka taga bai zo ba harda kukanta da ya kirata ta fara mai korafin bai zo ya ganta ba Alhalin ya gama kunsa mata wahala ta kusa mutuwa.
Ammh nan da matarsa zata Haihu bashi da ko lafiya a haka yaje ya ganta, ita ko tunda bata da matsayi bai zo ya ganta ba ballatana yaga abunda ta haifa.
Shi dai hakuri ya bata Tunda Talata ne ta Haihu da safe kuma ranar aiki ne shiyasa yace sai Ranar jumma'a zai taho gabadaya tare da Siya.
Sannan can gida ne kowa na tare da ita kuma suna waya da Umma yana jin Halin da ake ciki a ganinsa zuwansa kuma sai ya ke ganin kamar raina kokarin Su Umma ne.
Ita ko daman ga rashin haihuwan yan Biyu sannan ga shi ta Haifi mace gani ta ke yi kamar Darajanta ya sauka.
Hasiya tafi ta har yanzu, kiri kiri taki bama yarinyar Nono wai zafi take ji sai da Umma ta fita yamma da Hankalinta sannan ta fara bata Nono ta na yi ta na kuka.
Kwanan su Biyu a asibiti aka sallamota zuwa gida Bangaren Umma ne tunda itace uwa Dakin ta na baya tun na yanmatanci nan aka gyara mata zata yi zaman jego.
Ko'ina kuma an sanar da Haihuwarta Mutanen shinkafi dai nata mamaki jin ance mace ta haifa kuma ba yan Biyu ba.
Da kuma an ce Sultana ya muka ga D'aya ba Biyu ba? Sai ta fashe da kuka kamar wacce aka yi ma duka.
Tunda kuma ta haihu ta yi ta Turen turen baki ita a dole Assadiq bai Dauketa da Muhimmanci ba.
Ta yi ta kiranshi tana yi masa korafi shi wlh har fama ya ke yi da Fad'uwan gaba in yaga kiran Sultana saboda yasan matsalace da korafi da ba'a yi mata daidai ba.
Tun kafin mu taho na saka Siyama ta turamin Lambarta na kirata domin na yi mata barka.
Inaga ta gane muryata ne cikin Gadara tace"Wa ke mgana?
Ni kuma kai Tsaye nace mata"Hasiya ce an sauka lafiya?
Kawai sai ta yi tsaki ta kashe wayar na yi ta mamaki daga aabun arziki.
Daganan ban kara kiranta ba sai itace ta kara kirana na dauka ma bata ganeni ba ne daga farko.
Ina dauka ta fara fad'amin mganganun banza wai na hana Assadiq zuwa ya gansu to na sani ban isa na shiga tsskaninta da Mijinta ba.
Har zagina ta yi tana kirana Annoba kuma bazawara.
Ni na gaji da jinta na kashe wayata ta yi ta kira ban dauka ba sai Sako ta Test massages har da wai kada na yi tunanin na haifi maza na cinye gida itama zata haifi nata na zura ido na yi kallo.
Abun nata ma sai ya koma min kamar bata da Tunani yarinyar nan gaskiyar Umma ne mahaukaciya ce.
Ko Assadiq ban gayama ba, na dai ce masa na kira sultana na yi mata barka kuma naga yaji dadin haka.
Su Umma daman tun ranar da aka yi haihuwan na kira su na yi musu barka hadda Abba.
Shirin gabadaya ni na yi tare da yara Tunda daganan katsina zan wuce bikin Tahir shi kuma zai dawo Abuja daga Abuja zai zo katsina Saboda ya Samu Daurin aure.
Ranar jumma'a da yamma muka iso Gusau.
Yara tun a haraban gidan muka Rabu da su to ya'yan dangi ne fa Tare da Assadiq muka fara shiga wajen Abba muka gaisa sai Bangaren Innani.
Allah sarki yau jikin da dana ma, ta na kwance sai dai bakin ne yau ya Bude har suka yi ta hira da magajin gida.
Ni nan na barshi na tafi zuwa bangaren Umma kayanmu kuma an shiga da su shashen Assadiq.
Ko da na shiga shashen Umma cike da baki masu barka.
Anan naga su Anty Sakeena ita kadai ta tarbeni, Sai Umma da tun a haraba muka had'u muka gaisa.
Dakin mejego kuma cike da kawayemta yan makaranta da su Sajida da Sadiya.
Sakeena ta rakani na shiga domin na yi mata barka ammh ina gaishe su ba wacce ta amsa sai kallon banza.
Itama Sultanan kai ta kauda ta na mgana da wata a kusa da ita.
Ni dai naga suna nuna ni suna Dariya suna kuskus kasa kasa.
Sakeena ce ta kalli Sultana kafin tace"Sultana baki ji Hasiya na miki barka da sauka ba ne?
Baki ta tabe kafin tace"Ban ji ba yauwa.!
Daga haka ta cigaba da mganarta ina Tsaye ina yake sakeena ta isa kusa da Sajida ta na fadin"Sajida bani jaririyar Hasiya ta ganta."
Kamar ta watsa mata kankara haka ta mike a firgice ta na fad'in"Wata jaririyar? Wannan?
Ta fad'a ta na nuna jaririyar da ke cikin kayan sanyi a gefen uwarta.
Sultana ta yi caraf ta dauke yarta ta na Fadin"A'a kada a goga ma yata Mugun Jini."
Sadiya ta karbe da fadin"Wlh kuwa gwara ki yi can haka da ita, kada yanzu kajin Tsiya da bala'i su fara Bibiyanta"
Gabadaya sai naji na muzanta idanuwana suka tara kwallah ammh sai na Shanye.
Sakeena ce tace"Haba don Allah, daga abun arziki kuma miye ya kawo wannan mganar?
Sajida tace"Wani abun arziki waya san abunda ta kunso a hannunta tunda ba Allah a ranta? Kawai ta Dauki yarinya ta goga mata wani abun tsiya, tunda ita dai Bakar Annoba ce Tsiya tsiya jinin bala'i da Farar kafa. Tsiya nan ta ganta ta barta ke ai ganin ki bala'i ne da masifa in da kuma kika shiga kika zauna shima bala'in ki zai iya fad'ama waje, gwara ki koma inda kika fito barka ne ko? To mungode Allah ya ba da lada ammh a kara gaba, ban da munafunci miye na Biyo miji barkan kishiya? Zugwai zugwai ko kunya baki ji ba."
Ta ke fad'a ta na nuna min hanyar fita, kaina na kasa ina kokarin yaki da kaina ba na so na yi kuka su gani sai kawai na yi mirmishi na juya.
Sakeena na bari ta na yi musu mgana sai abun ya koma kanta itama..na fita falon Umma ba na gani Saboda Duhu ya mamaye ganina da kuka da ya taso min hawaye sun fara zubarmin.
Na ci karo da Sa'ima ma ban sani ba tana min mgana ban Tsaya ba, da gudu na tafi bangarena ina kuka.
Bansan cewa fad'a ya hautsine tsakanin Sakeena da Sajida ba Sai da Anty sa'ima ta shiga tsakaninsu.
Kuma a gaban kawayen sultana to ai suma su san komai tunda ta gayamusu komai.
Mgana ta kai kunnen Umma da Abba har da Assadiq da baya nan yaje gida ya yi wanka.
Anty Surayya ta kirasa tace itama Sa'im ta kirata ta na fad'a mata Sajida ta zazzagi Hasiya.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.