Tmw Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: TMW BOOK 3.txt
Chapter 25 of 86
Kai Tsaye Abba ya kalli Sauran ya'yansa kafin yace"ga wata yar'uwa nan kun samu acikin ku, sai ku marabaceta cikin Ilimi kamar daman kun saba, ke kuma Sultana ki yi hakuri Bamu isa mu sauya wannan kaddaran ba, Magajin gida zai zauna da ku dukkan ku a matsayin matansa In sha Allahu."
Umma ta mike a fusace kafin tace"Abban Siyama wannan wani irin Hukunci ne?
Mama na gefe tace"Gaskiya fa, wannan ai ba mgana ba ce."
Suma sauran nata kuskus, Surayya dai batace komai ba Sajida ne ke ta yi ma Sadiya rad'a suna Gulma.
Sultana kuma kamar da kasa sai kwai ta fashe da kuka.
Jin haka yasa kafin ma Abba ya samu Zarafin mgana Innani ta mike kad'an ma ya rage bata fad'i ba Saboda masifa tace"Ishunki Salamatu ai Sulaimanu bai isa ba, samman wannan Hukunci da ka yanke bai yi ba."
Abba ya sauke Numfashi kafin yace"Innani wani Hukunci ki ke so na yanke bayan wannan?
Innani na Huci tace"Ka yi masa fata fata na cin amanarmu da ya yi mana, bayan haka a gabamu ka saka ya saki kilakin nan a yi mata Korar kare shine hukuncin adalci Sulaimanu."
Abba yace"Subhanallah Innani, Magajin gida aure ya yi ba zaman Haramci ba, kuma shi da Niyyar taimako ya yi wannan abun, mun zauna da shi ya yi min bayanin komai kuma ni na aminta da shi."
Umma da ke tsaye tace"Kai ya yi ma bayani ai bai yi mana ba ko?
Abba ya kalleta kafin yace"Hakane to ku koma ku zauna, kai Sadiq juya ka yi musu irin bayanin da ka yi min dazu"
Sadiq da gabadaya yaji gwiwarsa ta sare, ni ya ke kallo ganin na dukar da kaina ina ta kuka komai fa zai Faru bazai bari a Tozartamai mata ba.
Cikin gyara zama ya fara bayaninsa haduwarsa da Hasiya da auransu sai dai kamar yadda Abba ya Bukata ya Boye wasu abubuwan.
Ya karishe da fadin"Kuma ni har Allah acikin zuciyata Tausayi ne, sai daga baya na Fahimci ba'a Tausayi in ba so, ina son Siya sannan Kuma ina son zama da ita har karshen Rayuwata Umma don Allah Ki Fahimceni."
Umma cikin harzuka tace"In naki na Fahimceka fa? Nace in naki na Fahimceka fa? Sai aka yi ya ya?
Kansa na kasa yace"Ki yi hakuri Umma, na yi kuskure kuma na yi miki alkwarin in sha Allahu hakan bazai kara Faruwa ba."
Kai Tsaye Umma tace"Abubakar bazan karbi wannan auran naka ba, sannan kuma Wallahi Tallahi sai dai ka zab'a ko Auran da muka sani ko wanda ka yi ma kanka."
Da sauri ya dago ya na kallon Umma kafin yace"Umma."
Hannu ta daga masa kafin tace"Abunda nace shi na ke nufi, kuma anan wajen zaka zab'a, gwara Tun wuri nasan matsayin da ka ijiyeni."
Sai kuma kawai ta Fashe da kuka, Innani ta yi zaraf tace"Kwarai mganar Salamatu haka take, gwara dai mu san matsayin mu."
Abba zai yi mgana Innani ta daga sandarta ta na fadin"Ka na cewa Tak Sulaimanu kagani in ban kwad'a maka sandar nan ba."
Duk da ana cikin Rudani ne, ammh bai hana wasu darawa ba.
Abba sai ya koma kawai ya yi shuru ya na kallon ikon Allah.
Sadiq ya rasa yadda zai yi ya tashi yaje gaban Umma ya duka ya na fadin"Umma don Allah ki janye kalamanki, duka ina son mata na kuma ina son zama da su bazan iya zabar d'aya na bar d'aya ba."
Umma na sharan kwallah tace"Sai dai ka zab'a, tunda har ka iya nuna ko ni mahaifiyarka ba ni da ta cewa acikin Rayuwarka Abubakar"
Yadda ta Juya masa Fuska ne yasa yasan ta riga ta yi fushi.
Mama ya kallah tun kafin ya yi mgana tace"Sadiq gaskiya ne fa gwara dai ka sahale ma kanka, kafin ma ta san irin bakin fentin da ke tare da matar da ka aura."
Ido ya kura mata ya na kallonta Umma ko da Sauri ta Juyo ta na fadin"Wani irin bakin fenti ne Suwaiba? Don Allah ki fad'amin."
Mama ta Juya ta na kallon ya'yanta su Sa'ima su kuma suka gyad'a mata kai alamun ta fad'a.
Surayya kuma Tsoro ya kamata sai ta kalli Sajida ita kuma sai ta ware mata ido alamun ni bansan komai ba.
Mama ta gyara zama ta na fadin"kunsan dai salima na auran danginta, Alhaji jibril da ke kanin babanta da kansa ya ke fad'a ma Salima Matar da Sadiq ya aura Farar kafa gareta, duk wanda ta rab'u dashi ko asaran lafiya ko na dukiya ko na rai, Sannan da bakinsa ya fad'a yace tunda aka haifeta iyayenta ke ganin bala'i har sai da ta yi sanadiyar karayar arzikin Ubanta daga karshe tayi ajalinsa, sannan Mahaifiaryarta ta fara ciwom da aka kasa gane kansa, komai na su ya kare sannan kowa ma ya gujesu har su dangin Uban nasu, Sannan yace auranta Biyu na Farkon shima sai da komai nashi da na iyayen suka kare daga karshe ma zaman garin ne ya gagaresa, na Biyun kuma ranar Daurin aure ya samu had'ari ance har yanzu bai warke ba ya nakasa ga asaran dukiya, Wlh ance duk zuru'ar da ta shiga sai ta tarwatsasu sun rasa komai na su in ba'ayi asaran rai da lafiya ba fa an godema Allah."
Gabadaya Falon sai ya Dauki salatin su Umma, Innani kam kamewa ta yi a zaune Tsabar tashin Hankali.
Surayya kanta ta yi kasa da shi tasan komai ya lalace.
Sajida kuma ta mata alama da Hannun cewa ba ita ta fad'a ba, sai yanzu ta tuna da Hoton da ta Turama Salima shi ya lalata komai.
Kafin kace me salima ta karbi mganar ta na kara maida yarda akayi sai nanata take yi wai ance auranta ma Biyu duka ana sakinta Saboda bakin Jinin da ke tare da ita.
Shahida ta saka salati Kafin tace"Sadiq yanzu wannan Annoban da kowa ke gudu kai ka kwaso mana?
Sadiya kuma tabdijan kawai ta ke fad'i kafin tace"Wlh Umma Canfi gaskiya ne, mun shiga uku."
Abba kuma na zaune yana jinsu, yana maimaita sunan Alhaji Jibril shi sai yanzu yasan Komai da mafarin lamarin.
Yana ganin kimar Alhaji Jibril tun bayan da suka had'a auratayya a Tsakaninsu, ammh kuma wannan Labarin da yaji sai yaji kwata kwata ya raina masa ta ina zaka Biye ma wannan Abun da baka da Tabbaci a kansa? Kawai sai yaji kamar ya raina masa kwata kwata Tunda a baya yana ganinsa mai ilimi ne.
Falon ya kaure da hayaniya Umma kuka kawai ta ke yi ta na Hango kilama ta kusa rasa d'anta.
Surayya bata da mgana Saboda su Shahida da Sadiya suna kara ma Umma Famfo kar ma Sajida ta ji labari.
Sadiq sai kawai ya koma ya Dukar da kansa ya na kuma neman mafita ammh acikin ransa Hasbullahi ya ke ta maimaitawa.
Ba wanda ya san lokacin da Innani ta tashi sai da akaji muryan Abba na fad'in"Subhanallahi Innani lafiya?
Sai aka juyo nan fa aka ga Inanni ta Daga sandarta zata makama Hasiya dake zaune ta na kuka.
Fad'i ta ke yi"Ka bari na Rafketa Sulaimanu, wannan ai bakar dakace ta Shigo Cikin zuru'ata na bani ina jin ma ko mayyace zata lashe kurwan Magajin gida, namiji kwara d'aya kwal da Sulaimanu ya mallaka in wani abu ya sameshi ai mun lalace, ni Dije ina zan saka kaina, yau naga Bala'i ganin idona da maita."
Ta ke fad'a ta na kuka ta na kokarin kwace sandar ta daga hannun Abba.
A tare Surayya da Sadiq suka mike, sai dai ya Rigata isa kaina, tunda Innani ta saki sandarta da Hannu ta saka ta kaimin Dundu sai gadon bayan Assadiq Tunda ya yi min Rumfa.
Bata ma Fahimci shi ta ke duka ba idanuwanta ya Rufe fad'i ta ke yi"Mayya Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu, kurwan jikana Qur wlh, fita ki barmin gidana ki kuma Rabu da zuru'ata gabadaya."
Ta ke fad'a ta na kuka, Sadiq ya Dago a fusace ya Rike Hannun Innani yana fadin"Kada ki kara kiran matata da Mayya. SIYA ba mayya bace itama Mutum ce kamar kowa."
Ya fad'a cikin Tsawa kafin ya wancakar da Hannun Innani ya Dagoni jikinsa ya Rumgumeni kamkam, ni ko ina ta kuka ina fad'in"Assadiq don Allah kada ka rabu dani."
Ya na rike dani yace"Babu wanda ya isa ya rabani da ke Siya."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.