Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 33 of 86

******
A falon Umma kuwa bayan Fitata sai da Umma ta gama shanya Sadiq zaune a gabanta sannan ta gyara zama ta kalleshi Lokaci d'aya ta na fadin"Abubakar dago nan ka kalleni."
Ba musu ya dago yana kallonta Fuskarta ba Fara'a tace"Wacece ni hala a wajen ka?
Cikin mamakin Tambayarta yace"Ke din mahaifiyata ce."
Wani mirmishi Umma ta yi kafin ta daga baki ta kira sunan Sultana ta amsa sai gashi ta fito.
Gaban Umma ta durkusa ta na cewa gata, Umma ta kalleta yadda duk ta rame a tsaye, suma cikin satin da ya fita suka gama WEac Sai neco.
Duk ta rame ta Lalace sannan ba ta da wani Walwala bata da aiki sai kuka.
Itace ya kamata ta share mata hawaye Tunda dai ba ta da wata Uwar da ta wuceta.
Nuna masa ita ta yi kafin tace"Ita kuma miye nata matsayin a wajen ka?
Sai da ya dago ya na kallon sultana wacce ta kauda kai gefe kamar bata son kallonsa.
Cikin sanyin murya yace"Ita d'in kanwata ce sannan kuma matata."
Umma ta jinjina kai kafin tace"Shine ka maida maganata banzaa ko Sadiq? Ba na gayamaka ka zaba ko sultana ko wanchar bakar Annobar ba? Ammh Saboda Alhaji ya baka Dama sai ka saka kafa ka shure mganata ka yi tafiyarka tare da matarka kana so ka nuna min abunda ka ke nufi ko?
Zai yi mgana ta daga masa hannu a Fusace ta na cigaba fad'in"Bana son jin komai daga bakin ka, yanzu zaka gayamin meneme manufarka? Tunda ka tafi ka barni da yarinya kuma baka min wata mgana ba, in ka zab'i wancan ne sai ka sakarmin yarinya domin tasan ta fara Iddarta."
Baki ya saki kafin yace"Me ya kawo kuma mganar Saki anan wajen kuma Umma?
Umma ta balla masa Harara kafin tace"Bansani ba, sallamamme mara Tunani ai na riga na fada maka baka isa ba. Indai ka zabi zama da wannan Annobar to sai ka sakarmin y'a kaji ma na gayamaka."
Shuru ya yi kansa na kasa kafin yace"Umma ba maganar saki Tsakanina da Sultana ballatana Siya, dukkansu ban aure su domin na sake su ba."
Umma ta harzuko kamar zata dakesa ta na fadin"To wlh ahir dinka, kai da dauko bala'in sai dai ya kare maka ammh bazan bari diyata ta zauna da kai ba, tunda ka zabi Ita Bakar Annoba to ka shirya sakar min yarinya kaji ma na rantse."
Cikin mamaki yace"Umma kada ki yi saurin Rantsuwa fa?
Umma tace"Nace wlh tallahi Rantsuwan d'an musulmi in baka saki wannan annobar matar da ka jajibo ba, to auren ka da Sultana na Haramtashi."
Baki sake yace"Umma kada ki zo ki yi kafarra gwara ki janye rantsuwan ki domin na baki tabbacin dukkansu ina son su ba kuma zan iya Rabuwa da d'aya saboda d'aya ba."
Mamakinsa ya kama Umma daman ai tasan halinsa ba'a kadashi a mgana.
A fusace tace"Sai kuma ka yi, tashi ka bani waje ni na riga na gama mgana."
Kin tashi ya yi sai ma ya gyara zama yana fadin"Umma ki yi hakuri don Allah, nasan na yi ba daidai ba ammh tunda nagane kuskurena sai ki yi min afuwa don Allah."
Umma saboda ma tagaji da jin mganarsa sai kawai ta kallo sultana ta na fadin"Ke tashi ki karamin karan Tibin nan ki shiga ciki."
Ba musu Sultana ta mike Idanuwanta har sun tasa saboda kuka ta kara karan talabijin din ta wuce salau salau ta koma cikin daki Sadiq ya bita da kallo.

Kafin ya girgiza kai kawai, bai tab'a Tunanin haka yarinyar ta yi nisa ba sai yanzu, tun bayan Faruwar abun bata bari sun yi mgana ba ya yi ta kiranta bata dauka ba, har Texts ya tura mata na ban hakuri duk da shi a ganinsa bai yi mata wani laifi ba ammh yarinyar nan ta yi masa banza.
Sai cikin satin nan yaga ta turo masa sakon wai ta jisa shuru ta na jiransa.
To alokacin ya dauka ta sauko ne za su yi magana sai ya kirata kawai sai ta rika latsa masa Busy.
Shi kuma da ya Fahimci ba ta da kunya sai ya kyaleta shekaranjiya kuma sai gashi ta kara Turo masa wai tana so tasan matsayinta.
Bai yi mamaki ba daman Big sis tace su Sadiya ke kara zugata ita da Umma.
Kuma daman yasan kowa acikin su musamman Sajida da saboda munafunci bakinta ya yi tsini uwar gulma.
In ta zauna ta na Biye musu ita ta sani shi dai Allah na gani akan abunda ya aikata na raya sunna ma'aiki, kuma yace yasan bai kyauta ba kuma ya ba da Hakuri ammh yarinyar nan na neman kuresa.
Kawai sai ya tura mata da sakon cewa amsar matsayinta na wajenta, duk matsayin da ta yi ma kanta shi a wajensa daidai ne, kuma ya na da tabbacin su suka zugata ta Rubuta masa haka.
Bai hakura ba, ballatana ya Saduda haka ya zauna ya na ta ba ma Umma Hakuri ita ko ta na zaune ta na masa wani kallo.
Sai da taji yace"Umma yanzu in kika ce sai na saki Siya  ina kike so taje da wannan Tsohon cikin? Kuma fa bai hallasta saki da ciki a irin wannan Lokacin ba."
Umma ta daga masa hannu a Fusace kafin ta mike taje ta kashe talabijin da kanta sannan ta Dawo ta zauna ta na fadin"Maimata abunda ka ce yanzu."
Kansa na kasa ya maimaita Umma ta fara fad'a ta na fadin"Ah ba Siya ba Siyoyo kaji min mara kunya, ina ruwana da cikin jikinta kai ke da matsala dashi, abun takaici ma mallam wai ka rasa waxaka aura sai bazawara wacce ta gama yawon dakuna? Kuma nasan kasan  bakar Annoba ce, kowa na gudunta ammh da ya ke kai shashasha ne sakarai sai ka kwasa ka kawo mana cikin zuru'ar mu ko?
Ta fad'a ta na kallonsa cikin Takaicinsa.
Sadiq daman yasan haka zata Faru sai ya yi shuru ya na jin Umma ta na ta zagin Hasiya ta na aibata ta.
Ita kam ai sha kumdum ne bazai iya kare Siya a gabanta ba.
Ammh dai bazai ki gayamata abunda Allah yace ba.
Cikin sanyin murya yace"Umma miye Laifin zawarawa ? Su ba Mutane ba ne? Sannan me yasa a ke son ware su daga cikin mata? Ai suma Mutane ne kuma ba su suka kaddaro ma kansu mutuwar aure ba kaddaran Allah ne, Umma ko acikin ya'yan ki suma Allah zai iya jarbtan daya daga cikin su da Mutuwar aure in wannan ya faru sai ki ce mene?
Umma ta yi hangam da baki ta na kallon Sadiq ya na cigaba da fadin"Kuma Umma sunan nan da kike kiran siya da shi bai kamata ba, ba kyau musulmi ya rika aibata musulmi  dan'uwansa balle kuma ya yi masa Dariyan kaddaransa  dalili shine shima bai wuce kaddaran haka ta fada masa ba, kuma Umma duk fa karya ce ba wani Canfi a addinin mu, bamu san shi ba, Qur'ani ya koya mana sanin Tauhidi da iklasi kuma ni a iya ilimin da na ke da shi nasan cewa Wani abu bai isa ya samu wani bawa ba face abunda Ubangiji ya Shirya masa."
Umma sai kallonsa ta ke yi kamar ta kai masa duka, Sai da taga ya kara wani gyara zama zai kara shiryamata magana Fusace ta dakar dashi da cewa"Kai dalla gafarachan, ni zaka zo ka zauna da d'an iliminka na cikin cokali kana gayamin nima za'a iya sakar min ya'ya su zama zawarawa ?
Cikin mamaki yace"Ni fa ba."
"Ka rufemin baki nace ko? Karya na yi maka ba haka ka zauna anan wajen kana fad'amin ba, tashi ka fita ni bazan gani ba Tunda mace ta saka ka fara musu da uwarka da yan'uwanka daman Tuni ka nuna musu iyakarsu ai sai kaje ita ta zame maka uwa da yan'uwa"
Zai kara magana Umma ta mike ta na fadin"Kada ka fita di'n , ni bari na bar maka falon."
Jiki a sabule ya fita daga bangaren Umma Abba baya nan ammh sun yi waya yana nan dawowa.
Ya dauka ina bangaren Innani sai da yaje yaga ba na nan daga ita sai Farida.
Daman sanda aka yi wannan Cases din bata nan taje ganin gida chan Shinkafi.
Innani ta rika ina ta saka dashi shi kuma yana mata cin magani.
Kula da hakan da ta yi ne yasa tace"Nifa tuni na Saduda na bi Allah Tunda Sulaimanu ya yi min nasiha ina ni ina ja da Abunda Allah yace ayi, Uhm ni wai ita sulsanan Salamatu ta rike ta ta ce bazata koma gidan ka ba ne magajin gida?
Kai Tsaye yace"Haka tace"
Innani ta yi shuru kafin tace"Ba abun na yi mgana ba yanzu sai ace na so bare naki d'an gida."
Kai Tsaye Assadiq yace"To gwara ki yi shurun zai fi miki alheri."
Daga haka suka cigaba da Hirarsu tace ina Matar tasa yace yana ga tana bangaren Mama.
Innani ta tabe fuska kafin tace"Da ba nan ka kawomin ita ba, wai ni yaushe ne zata haihu har yanzu shuru ban ji an ce ta sauka ba?
Sadiq yace"Ki tayata da addu'a Innani ta na watan haihuwanta ne"
Innani ta fara jero addu'o'in Ga Hasiya Sadiq na amsa mata da Ameen
Da yaji dadi kai Tsaye yace"Ke zaki zo mata ma zaman arba'in na Jego."
Innani ta washe baki ta na fadin"Allahu akbar Allah ya nuna min ranar da wannan albarka zata sauka a gidan Magajin gida.
Ya jima a bangarenta sai da Abba ya kirasa yace ya dawo sannan ya yi mata sallama ta na ce masa ya kawo mata Hasiya bangarenta ta zauna har ta na rage murya ta na fad'in Tunda salamatu dai ta cire Allah a ranta ba mutumtata Baiwar Allah zata yi ba. shi dai bai ce komai ba sai Dariya kawai da ya yi.
Bai nemeni ba, sai da yaje shashen Abba suka gaisa ya kuma zauna ya karanta masa komai da Umma ta tareshi da shi.
Abba ya yi mirmishi kafin yace"Rabu da ita, ina mai tabbatar maka itace zata yi kaffara ammh kamar yadda na fad'amaka ba wacce zaka saka saboda wata."
Sadiq yace"To Abba ya zan yi? Umma taki fahimtata."
Abba yace"To ka nemi matarka ka lallasheta mana."
Da sauri yace"Duk su Sajida sun gama zugata bata ko daukan wayata, Allah Abba ka hana su zuwa gidan nan basa yad'a komai sai sharri akaina da Matata."
Abba na dariya yace"Ka kyalesu duk su yi su gama, ai ba su isa su ja da ikon Allah ba."
Jin abunda Abba yace ne yasa sai ya bar mganar.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.