Tmw Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: TMW BOOK 3.txt
Chapter 44 of 86
Sultana da siyama da suka Dawo daga Jarabawa suka samu Labari. sai kishi da bakinciki ya turkuketa har da kuka Siyama kuma sai ta kama Murna tana son ganin yaran kuma ma yan Biyu masu ban sha'awa.
Surayya da ta samu Labari ta fi kowa murna daman kuma tasan girman cikin nan na Hasiya yafi guda d'aya.
Bata yi mamakin jin cewa Sadiq yana zariya ba, daman tasan matukar yana iya tafiya sai ya nemo Hasiya zuwa kuma wannan lokacin tasan yasan komai da ya faru.
Da wayar Tahir ta kirashi suka yi mgana da shi ta yi masa barka, bai yi mata wata mgana ba itama bata yi masa ba sun Rabu akan gobe zata zo in sha Allahu..shi kuma yace zasu kwana a Hotel zuwa da Safe tunda Hasiyar ta Farfado dazu bayan mangariba.
Ni dai kawai farkawa na yi na ganin a gadon asibiti acikin daki na musamman.
Nurse din da ke kaina ta shaidamin aiki aka yi min an ciromin yara Biyu duka maza.
Ba farincikina Haihuwanta na rika yi ba sai na ganin Assadiq a kaina yana rike da Hannuna.
Sai gashi ina hawaye ina fadin"Assadiq daman zan kara ganin ka?
Cikin mirmishi yace"Gashi kin gani, ai na taba fad'a miki ni da ke har Abada ne Siya."
Duk da dinkin jikina sai da na Rumgumesa ina kukan Farincikin sake ganinsa a Lokacin da na Fidda rai.
Ban taba ganin Tahir ya yi min Fara'a irin na yau ba, shi ya mikama min yaron d'aya Assadiq ya kwantar da daya a saman jikina.
Su Adda na gefe suna ta min mirmishi da barka da arziki.
Bansan Sadiq na tafiya da Sanda ba sai da ya mike cikin damuwa na kallesa ina fadin"Assadiq me ya samu kafar ? ita bata warke ba?.
Domin duk naga Tabon ciwukan kansa cikin mirmishi yace"Karayace a kafar ita bata karisa warkewa ba."
Sai gani hawayena na diga saman ya'yan dake zube a jikina.
Mirmishi ya yi min kafin ya Furta"Nagode Nagode sosai Siya, na yaba kuma ina Fatan Ubangiji kema ya yaba miki fiye da yadda ni na yaba miki."
Na kalli yan'uwana a zagaye dani abun Farincikina ganin Assadiq a kusa dani, na tuna a baya sanda na shiga cikin kunci saboda rashinsa.
Har nagama zamana a wajen Amma bata san abunda ya faru ba, saboda kada ta Fahimci wani abu yasa nace zan dawo wajen Adda kafin Assadiq ya Dawo.
Itama da na dawo ban gayamata komai ba, har kuma zuwan Maman suhailat ni nace kada ta sanar da su, hatta kawata Ramatu na Boye mata wannan sirrin Saboda ba na so su rika kallon Assadiq da wani Duba na Dabam.
Safiya kawar Amana ce bata tafi gida ba sai da taga farfad'owata na Tuna gajiya ta yi da kiran wayata a kashe taje gidana maman suhailat tace ina gidan yayata daman kuma mun taba zuwa tare sai gata tazo ganina, da ya ke mun koma makaranta a halin nauyin cikin nan da na ke ciki tara kani makaranta naje na karbo T.P LETTER d'ina ban dai samu na kai makarantar da zan yi Teaching pratice din ba Nagudan Tsaye Tsaye ya kamani, daman kowa na mamakin girman cikina sannan kuma ya wuce wattanin haihuwansa.
Kuma da na dawo naje asibiti suka Dubani sukace lolacin haihuwata bai yi ba, duk da cikin ya wuce wattaninsa ba su ga alamun mahaifa zata Bude ba.
Yadda gabadayansu suka zagaye gadon da ni ke kwance ne ya sakani kwalla, naji a raina ni Ubangiji ya gama mini komai tunda ya barni da Soyayyar yan'uwana tare da gwarzon miji irin Assadiq
Daman na sani ko a jima ko a dad'e Assadiq zai zo ya neme ni shiyasa nima na kasa mantawa da shi acikin zuciyata.
*Janafty*
*TMWB3K012*
*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*
https://chat.whatsapp.com/K3rO5UonX4GDVxtQbA5mZl
PAID ADVERT✅
Assalamualaikum wa rahmatullahi ta'ala wa barakatuhu!!! Wannan group din dai na komai da komai ne. A taiqaice
*Farashin mu na daban ne compared to sauran Yan kasuwa
*Kaya masu kyau da quality. Abinda kika zaba shi za a Baki
* Swift delivery.watau waybill a sauqaqe da Yardar Allah
* Muna sake New Arrivals ka fin su cika Gari
* Muna iya duba maku kaya a good price ko da ba namu ba ne idan kuka Aiko da hoton kayan
Allah sa mu qaru da juna Ameen
Washegari Surayya da ta shirya tafiya Zariya sai da ta biya ta gida ta sanar da Abba zata je ta duba mejego da yara.
Jin haka yasa Abba yace Mama ta shirya sai su tafi tare da Surayya sannan yace nawa suke bukata wanda zasu iya rike ma maijegon wani abu?
Ita daman Surayya ta zo da kaya cike da leda su pamper din yara ne, sai Kayan sanyi masu kyau da mayukan setin na yara.
Sai sauran tarkace irin na kayan yara dai jariri, Jin Abunda Abba yace ne yasa tace ya bari wannan sai sun je sun dawo tukunnah.
Siyama ma jin da Mama Za'a tafi ganin Twins itama ta dauki damara tace sai taje daman da Tunanin yaran ta kwana a ranta, Innani kuma damam Tun jiya ta had'a kayanta tace ai magajin gida ya yi mata alkwarin ita zata yi ma Hasiya wankan jego saboda haka rana fa bata karya sai dai uwar diya taji kunya.
Shi kuma Abba yace a tafi da ita taga ya'yan magajin gida Umma kuma sai ta zama yar kallo Sajida ma tazo gidan gulma taga ko Surayya ba ta tsaya cewa tazo su tafi ba, ballatana Abba da ga ita har Umma sai ya yi kamar bai ma gansu ba, harda Sultana da ta damu kanta da bakin kishi Saboda Haihuwar Hasiyan.
Direban Abba ya tukasu zuwa Zariya ko da suka isa ba su iske Sadiq ba ance ba jimawa suka dauki hanya shi da Tahir, sai wayar tahir din ta kira ya bashi suka yi mgana.
Ita kanta tasan Sadiq ya riketa a ransa saboda ko alama a muryansa ba wannan Fara'a da sakin jiki in yana magana da ita kuma a jiyan ta fad'a masa yau zata zo ta duba mai jego ammh yaki Tsayawa su iso.
Sunan asibitin ma Tahir ta kira da Farko ya fad'a musu da sunan lambar Dakin kafin su isa sannan suke samun Labarin Sadiq din ya Dauki Hanyar komawa Gusau.
Shi ko daman ya riga ya yi ma kansa wani alkwari acikin ransa, in dai abunda ya shafi Siya ne ya Cire kowa a ciki shine mijinta kuma Shine Dolenta ba wasu yan'uwansa ba, Abba ne kawai da Umma suka zame mata Dole suma sabama Ubangiji ya danne Bin umarninsu.
Shi daman Tunda ya samu had'arin nan da kuma jinyar da ya kwanta ba komai daya danganci katunan bankinsa a hannunsa, shiyasa ba shi da kudi sai ya yi ta aron na Hannun Tahir wanda shima yace ba na shi ba ne na ajiya ne, Kamar Abba ya sani da Safe ya kirashi suka yi magana yace ya Turamai account din bankin tahir ya Tura masa 100k.
Da shi ya samu ya yi ma Siya siyayyan kayan titi, kayan yara na pampers da Sauran su, tunda komai na haihuwan da suka tanada na cikin Dakin nan kuma sun tafi da key d'in.
Sai kawai ya bama Adda Wasu kudi yace taje kasuwa ta siyo abunda babu kafin yasan abunda zai yi akan su Sajida.
Ko zuwan su Surayya Abba ya fad'a masa ammh ya ki tsayawa Saboda bai ga abunda Tsayawar nasa zata haifar ba shiyasa yace su koma kawai.
ya so ma Tahir ya barshi ya hau motar haya shi kuma sai ya wuce Daura ammh yace a'a bai gama warkewa ba yana Tafiya da sanda bazai barshi ya yi Tafiya mai Tsawo a motar haya ba.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.