Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 69 of 86

*Janafty*
*TMWB3K018*

*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*

https://chat.whatsapp.com/I7uxPXgtPKBHnVQjaEbRlE

*LAME NIG!*

*KASAITATTUN MATA MUN GAISHE KU*.
*AISHA LAME TA KAWO MUKU DUKKAN NAU'IN KAYAN KWALLIYA*.
*KUNSAN GWANAACE WAJEN BAWA FATA HAKKIN TA*
*KUN TUNA KYUAN FATAR GUDUYO KO?*
*KUN TUNA DAI YADDA BULKACHUWA KE SIYAWA YABI KAYAN KWALLIYA NA ORIFLAME KO?*
*TO KEMA GARZAYO KI ZABI NA KI, KO TA ZABA MIKI WANDA ZAI FI DACEWA DA FATARKI*.
*BA IYA KAYAN ORIFLAME BA KAD'AI.*
*TANA DA PRODUCTS DABAN DABAN MASU KYAU, MASU MASTAKAITAN FARASHI*.
*KU TUNTUBE JIKAR DADAR MARINA A WANNAN LAMBAR 07036662633*.
*ADO DA KAMSHI NE SIRRIN GAYU*

Daga Sajida har su Umma ba su tab'a Tunanin Sajida zata iya tsintar kanta a cikin zawarcin da ta samu kanta a ciki Dumu dumu ba.
Sajida ta gama sakankancewa da ta kama gida ta kuma fi karfin wani ya tugeta, ta na ganin Yusuf mai Hakuri ne sannan mai kawaici wanda baya maida kai kan wasu abubuwa kuma ta na ganin cewa ta Haihu ga ya'ya uku a tsakaninsu tana ganin babu wanda ya isa ya iya ja da ita.
Ta saki jiki ta na ta rashin mutumcin da ta saba daman tun tana gidan Sajida akwai munafunci sannan in dai ta zauna a wuri ba ta yad'a alheri, kuma bata sulhu sai dai ta kara Hura wuta.
Bayan ta yi aure ma bata daina ba, a makota ne a dangin mijinta ne duk inda ta shiga ta zauna bata yad'a alheri ba sai dai ta fad'i sharri ta Hura wutar wata fitanar.
Bata kuma shiri da wasu kannen mijin nata tun tuni shima mijin nata ya sha ja mata a kunni karya ne su had'u a taro Sajida ba ta watse taron nan da fad'a ba, ita kanta mahaifiyarsa bata son Sajida sabida tace ba mutuniyar kwarai ba ce.
Bata son zaman lafiya, Ta dad'e ta na yin abubuwa Yusuf din da kauda kai sai wannan na karshenta da wa'adin auran na su ya kare.

A gidan sunan matar kanin Yusuf din, Ta yi fad'a da kannensa har suna zaginta ita kuma tace sun san wacce suka zaga wannan Tsohuwar mai Dattin dankwali na gida.
Ai ko ba sanya suna zuwa gida suka gayama Mahaifiyarsu ga abunda ya faru har suna kari, nan ta ke ta kira Yusuf tace ya sauwake Sajida kila in ta d'andani zawarci zata yi hankali.
Shine dalilin da yasa ya saketa sannan Saboda a kara kuntata mata uwar tace duk ya kwaso mata yaran ya kawo mata hadda wanda ta yaye.
Zaman da Abba ya yi da shi sai ya Fahimci Sajida ta canchanci ta zauna a gida ta ga rayuwa kila ko zata yi Hankali shiyasa shima bai kara neman Yusuf ba.
Ballatana Assadiq da yace Allah ya kara gwara da ya saketa kila nan gaba zata Fahimci rayuwa ko Allah zai saka ta zauna lafiya da kowa.
Ita ko Sajida da farko ta dauka wasa ne, Ta na ganin Yusuf bazai iya Rabuwa da ita ba wasa ya ke yi, zai zo da kafarsa ya neme ta ya kuma bata Hakuri ya maidata gidansa.
Shiyasa ko da ta dawo gida da Abba ma ya kirashi Haushi ta rika ji a tunaninta za'a zubar mata da Ajinta, sai da taga har ta shafe wata d'aya a gida har jini daya ta yi ba Yusuf ba sakonsa sannan ba wayarsa.
Daman tun faruwan abun bata kirasa ba ta zauna ne sai ya nemeta da kansa sai ta fara ganin karshenta.
Umma ta damu da wannan Lamarin sannan nadama ya shigeta, In ta zaunar da Sajida ta na mata fad'a sai ta rika Tura baki tana fadin Yusuf zai zo da kafarsa har dakin Umma ya Duka ya bata hakuri.
Sai da ta ga lokaci ya fara tafiya bai zo ba, sannan bai kirata ko a waya ba.
Sannan ga shi ta fara gajiya da zaman gida kewar ya'yanta take ji sosai da gidanta inda ta ke yi duk abunda taga dama ba nan da ba ta da ikon yin wani abu ba.

Sannan abun da ya bata mamaki yan'uwanta kowa sai yace laifinta ne, ita taja ma kanta saki kowa sai ganin laifinta ya ke yi, har Abba haka ya kirata ya yi mata kaca kaca ita kuma a ganinta bata aikata komai ba sai ma gani take yi da mutane ba sa son gsskiya ne.
Yanzu haka a daki d'aya suke kwana da Sultana tunda a bangaren Umma ba wani daki sai nata, ga shi cikin Dare Mai sunam Umma da suke kira da Ummi akwai kukan dare, Sultana juyawa ta ke yi ta sha barcinta ta barta da renon yarta.
In ta tasheta sai ta tashi ta na alamun barci barci in an samu ta bata Nono sai ta sakar mata yar ta koma ta kwanta tana fad'in kanta ciwo ya ke yi, sannan Umma da farko ta na shigowa ta taimaka mata itama in bata bangaren Abba to daga baya ma sai ta rika barin Sajidar da wahala ta bakinta tace tunda ta na kusa ta taya sultana jegon, kuma ma dai ai ta girmemeta a harkan ta rika nuna mata wasu abubuwan
Sajida ta na shuru da farko sai da taga Sultana ta maidata kamar Nany mai renon yarta, komai na ta ba tsari ba gyara ga son jiki da kazanta komai a watse sai dai in Sajidar ne zata gyara, in kuma ta yi mata mgana sai tace"Ni fa Anty Sajida na gaji ne, da me zan ji da kula da yarinyar ko da gyaran daki da kaya? Ai Umma tace tunda kin dawo gida kina zawarci ki rika tayani kina taimakamin mana."
Ranar Sajida ta sha mamaki kuma ba ta tab'a sanin haka kalmar zawarci ke da zafi ba sai da kanwar bayanta Kamar Sultana ta gasa mata mgana.
Abun ya yi mata ciwo kwarai ta samu Umma ta gayamata.
Umma ta yi wata dariya kai Tsaye ta kalli Sajida ta na fad'in"Ai ba karya ta yi ba, gaskiya ta fad'a tunda kin fito zawarci baki da wani amfani sai na Tayata kula da yarta, daman kuma bata da wata abokiyar shawaran da ta wuce ki ke da Sadiya, to tunda ita Sadiya na gidanta ke ce zaki zauna da ita kinga ma shikenan sai ku yi ta bama juna shawarwari ko?
Sajida bata gane mgana Umma ta gasa mata ba, sai da tace"To Umma ya dace ta wani ce na dawo gida ina zawarci?
Ni ai ba sa'anta ba ne, duk kokarin da na ke yi mata bata gani? Ni fa ban tab'a ganin sangantattaciyar kazamiyar mai jego irin ta ba wlh."
Umma dai yar dariya ta yi a ranta kafin tace tun yanzu?
Ai ta dauka da saura kafin zama yasa kowa yasan halin kowa.
Kuma sannan Sultana sai ta fara yi ma Sajida wani abu sai ana zaune sai ta kalleta cikin kamar mamaki ta na fad'in"Yanzu wai da gaske shikenan Anty Sajida kin zama bazawara?
Tambayar irin cikin izgili da Dariya da Renin hankali.
Sannan kuma ko a gaban waye ta kan fad'i haka ko a jikinta ita a dole da sunan wasa.
Tun Sajida na nuna bata jin haushi har ta fara nuna mata, sai tace ita a wasa ta ke mganarta.
Sannan wani karin abun haushin ma Har makaranta in Sultana zata shiga sai Umma tace su je tare da Sajida ta rike mata Ummi in sun shiga karatu.
Abun kuma da ya faru ba'a shiga da yara a ji, ita kuma Sultana tace a daukan mata mai reno.
Ko kuma Anty Sajida ta rika rakata makaranta ta na rike mata Ummi, ita kuma Umma ta amince tace tunda Sajidan na gidan bata komai idda ta ke yi, kuma tunda fitan ta zama ta lalura ta rika raka Sultana cikin makaranta.
Sajida bata kara jin ta raina kanta ba sai ranar da ta raka Sultana makaranta Lokacin har ta yi arba'in sai dai bata koma gidanta ba sai Assadiq ya dawo.
Yafi wata bai zo ba tun tafiyarsu ta bayan suna yana ta kawo uzurin aiki ne ya rikesa.
Tun safe suka zo, ita ta na waje rike da Ummi ta na fama da ita, ga sanyi Lokacin an fara iskar sanyi Sultana kuma ba su fito ba sai Wajen sha daya na safe sai gata ita da zugan kawayenta.
Suna zuwa suka ga Sajida rike da Ummi, cikin kawayen nata wata ta kalli Sajida ta na fad'in"Nanny ko da kika samu mai hankali daga gani zata kula da Ummi sosai."
Sultana ta kalli Sajida ta wani kyalkyace da Dariya kafin tace"Wata Nanny? Ba fa nanny ba ce Yayar mijina nace Anty Sajida da ya ke baki samu suwa suna ba ne shiyasa baki ganta ba, ammh ai su Maryam su santa."
Sajida ta na ji a gabanta Yarinyar tace"Au yi hakuri, na ganta a nan ne lafiya?
Sultana kai Tsaye tace"Zawarci ta ke yi mijinta ne ya saketa."
Ta fad'a ko a jikinta har ta na wani Dariya wani abu ya daki zuciyar Sajida.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.