Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 40 of 86

Gwara na je na zauna gaban Amma na haifi abunda ke cikina na Reneshi in Assadiq ya barmin shi ya Rayu dani in kuma bai barmun shi ba shikenan sai na zauna na cigaba da bautar Ubangiji har ta Allah ta kasance.
Ammh na hakura da yin aure na daina jazama mutanen da suka min hallaci wahala a rayuwarsu.
Na isa gada bayan mangariba saboda motar Bus ce, sai dai a halin da na iske Amma aciki bazata iya ma fahimtar nawa Halin ba.
Na iske Adda kwance ba lafiya sosai kuma taki yarda a kaita asibiti, a sanda na isa jikinta ya yi zafi ya'yanta duk suna kanta tare da Amma shiyasa ba wanda ya iya Fahimtar ina cikin wani hali, ni ma ai sai na Boye nawa na koma cikin yan jajantawa.
Amma kuma ba ta cikin natsuwarta a tunaninta na zo ganinta ne ta ma manta cewa Tsohon ciki gareni haihuwa ko yau ko gobe.
Na isa Garin ko awa daya ban yi ba Adda ta amsa kiran Ubangijinta.
Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un
Kullu nafsin za'ikatul maut."
Kowani rai sai ya dan'd'ani dacin mutuwa.
Sai gani ina taya Amma kukan Rashin yar'uwata a raina ina gayama kaina na Dunkule damuwata kada na bari Amma taji, in ba so na ke a yi gawa Biyu ba tun adaran na dauki wayar Amma na kira su Adda Fati na gayamusu.
Suma ta mamakin zuwana su a tunaninsa ko naji tashin jikin Adda ne yasa na tafi ba su san rashin dad'i ne ya kawoni ba.
Har Ramatu sai da na kira da wayar Amma na gayamata tace zata biyo su Adda Gobe da safe.
Haka ko akayi sun iso har da Inna Talatu sun kuma iske har an kai Adda Gidanta na gaskiyaa.
Ya'yanta na ta kuka damu kanmu Sabida mun yi rashi, Amma tafi kowa jin mutuwar nan saboda Adda ce kadai yar'uwan data rage mata Cikim Dangi.
Allah Sarki Rayuwa Allah ai baya barin wani domin wani yaji dad'i.

*Janafty*
*TMWBK3011*

*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*

https://chat.whatsapp.com/K3rO5UonX4GDVxtQbA5mZl
PAID ADVERT✅

Assalamualaikum wa rahmatullahi ta'ala wa barakatuhu!!! Wannan group din dai na komai da komai ne. A taiqaice
*Farashin mu na daban ne compared to sauran Yan kasuwa
*Kaya masu kyau da quality. Abinda kika zaba shi za a Baki
* Swift delivery.watau waybill a sauqaqe da Yardar Allah
* Muna sake New Arrivals ka fin su cika Gari
* Muna iya duba maku kaya a good price ko da ba namu ba ne idan kuka Aiko da hoton kayan
Allah sa mu qaru da juna Ameen

Babu wanda ya lura da Halin da ni ke ciki sai ranar da aka yi addu'ar uku na Adda, sannan ne Adda Fati ta Fahimci ko sau d'aya bata ganni da wayata ba shine ta ke tambaya ta.
Ni kuma cikin sauri na sanar da ita cewa ta lalace na barta a gida ne.
Daganan bata kara tambayata wani abu ba, a ranar Ramatu da Inna talatu suka tafi tare da yan dogon gida na samaru maman boy da maman Salihi sun zo Amma gaisuwa a ranar, sai suka koma tare da su Ramatu.
Adda Rukayya ma sai da ta kara tambayata ina wayata nace ta lalace na baro ta gida, ita dai cikin mamaki tace"To da wata waya ku ke mgana da Abubakar din?
Mirmishin yake na yi mata kafin nace"ai baya garin, ma'aikatan su ta tura su aikin titi wani gari in da ba Service shiyasa ma yace nazo nan wajen Amma kafin ya dawo."
Saboda tun washegarin Biyu da Rasuwar Adda na saci wayar Amma ina ta kiran wayar Assadiq ammh yaren guda d'aya ne wayarsa ta na kashe ne.
A dangin Babanmu Baaba ta lagos ce kad'ai ta kira Wayar Amma ta yi mata gaisuwa tace itama Baba Saminu ke gayamata ki rasa ta ina suke samun Labarin mu. Shi ko gaisuwan bai kira ya yi ma Amma ba ammh ya iya yad'a ma wasu.
Tare muka zauna da Amma har aka yi addu'ar bakwai din Adda, ba na yarda na yi kukana gaban yan'uwana Saboda ba na so su fahimci yadda Rayuwata ta kara yin tsudum a cikin tsaka mai wuya.
Kuma ko da sun ga idanuwana sun kumbura ba su cika damuwa ba, a tunanin ina kukan wannan rasuwar da aka kwantsama mana ne.
A daran da Adda ta yi bakwai ya'yanta suka taramu har da Amma suna rokon mu kada mu ce zamu dauke Amma ta koma wajen mu da zama, bayan Adda ba su da wata uwa da ta wuce Amma saboda haka zata cigaba da zama tare da Hamma Isuhu da iyalansa.
Mu ma daman bamu da wannan niyar ballatana Amma bazata taba aminewa da komawa zariya ba, nan take tace ba inda zataje tana tare da su itama har mutuwarta tazo ta isketa nan da nan sai kuka sai mutuwar ta dawo sabuwa.
Allah sarki ashe mutuwa bata  daukan wanda ke ciwo haka na raya a raina, Amma ce lafai lafai Adda kuma macece mai kazar kazar da alamun karfi Allah dai ya jikanta da Rahma.
Washegari kwana takwas su Adda Fati suka fara Shirin tafiya abunda ya basu mamaki ganina kwance bana shirin tafiya.
Habiba ce ta kalleni ina kwance da katon cikina a gabana tana fad'in"Adda Hasiya ke bazaki tafi ba ne?  naga baki shirya ba ne?
Duk kuma sai da ta yi mgana suka maida hankalinsu kaina har da Amma da ke zaune a gefena.
Adda Rukayya tace"Ina zucci zuccin na yi mgana kika rigani, Hasi nan zamu barki ne?
Ina kokarin tashi zaune nace"Eh yace in ya dawo zai zo ya daukeni."
Sai ba su damu ba sukace Allah ya kaimu ai bakomai sai na kara taya Amma zama Tunda har lokacin bata wani saki jikinta ba.
Amma ta kallo inda jerin akwatunan kayana suke cikin mamaki tace"To zai dad'e ne shi megida naki haka? Naga kin kwaso kaya har akwatina Biyu?
Gabana ya fad'i ammh kuma sai na yi saurin Washe bakina zan yi mgana.
Ammh sai Adda Fati ta rigani da fadin" Amma kika sani ko kayan haihuwa ne, tunda Adda bata raye ke zaki zama uwar zoman Hasiya."
Amma mirmishi kawai ta yi kafin tace"Allah ya jikanAdda, ko a satin da zata rasu sai da tace min Hasiya ta shiga watan haihuwanta ko?
Hasiya na ranta ta yi alkwarin zuwa ta zauna dake ta kula da ke tare da abunda kika haifa ashe Allah mai Hikima bazai bata damar ganin wannan Lokacin ba."
Gabad'ayanmu muka had'a baki wajen fadin"Allah ya jikanta da Rahma."
Amma ta amsa da Ameem Ameen ta na sharan kwallah.
A ranar su Adda Fati da Adda Rukayya tare da Habiba suka koma Zariya suka barni tare da Amma ina sake lallashinta sannan ganina yana sawa tana sakin jikinta.
Ya'yan Adda suma kowa ya koma wajen neman abincinsa mai auran ma mace itama ta koma gidan mijinta daman Badd'o na wajenta tun Adda na raye yanzu ma wajenta ta koma.
Sannan har a lokacin makota da abokan arzuka suna ta shigowa kara yi ma su Amma gaisuwa.
Ni kuma koda yaushe tunanina wani Hali Assadiq ya ke ciki?.
Har yau da Adda ke cika kwana goma da Rasuwa na kara gwada layinsa ammh amsar dai iri d'ayace a kashe.
Sai na fara tunanin ko dai wani mummunan abu ya faru da Assadiq ne? Kuma ni sun kwace wayata ballatana na samu lambar Anty Surayya na kirata naji wani Hali yake ciki, a koda yaushe ba na iya barci balle ma Tunda cikina ya tsufa ban cika samun  barci ballatana ni da na ke cikin Damuwa da halin kakani k'ani.
Ko alama ban yarda na bari Amma ta Fahimci wani abu ba, ina son uwata shiyasa ba na fatan ni nayi sanadiyar gayamata abunda zai kara Ruguzata shiyasa na yi shuru da bakina sai dai ina ta addu'an a duk inda Assadiq ya ke Allah ya bashi lafiya ya tada kafad'unsa ni ma kuma Allah ya sauke ni lafiya cikin ikonsa da kudurarsa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.