Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 49 of 86

Ba abunda yafi bakanta mata rai sai ganin yadda Sadiq ke faman rawan kafa akan yarinyar nan da ya'yan da ta Haifa bashi kadai ba hadda Abban Siyama, sannan uwa uba ga Innani can ta je ta tare a gidan su yarinyar, shiyasa ta yanke shawaran gwara Sultana ta dawo da ita zata yi amfani ta fitar da yarinyar nan har Abada daga Rayuwar Sadiq tunda a baya ta kokarta bata samu nasara ba
Sannan itama Sultanan ta samu ciki ta Haihu shime yanzu babban Burinta.
Tana cikin wannan Tunanin har Sadiq ya Biyo bayan kiran Sultana muryan nasa a cunkushe kamar an yi masa Dole, yace wayar na silent ne bai ga kiranta ba sai daga baya.
Itama cikin Dage baki ta gayamasa wai Umma tace ya siyo Cefane.
Umma kamar ta maketa haka taji da Sauri ta karb'i wayar suka gaisa shi daman Abba ya fad'a masa Umma yau tace masa zata maida Sultana gidanta duk wannan Murnan da ya ke ji a baya na kasancewa da sultana ya kasa jinsa a wannan Lokacin.

Shifa tunda ya Fahimci yarinyar bata da kunya ya gane ta su bazata taba zuwa d'aya ba kawai ta na cin Darajan masu daraja ne shiyasa
Cikin Sauya mgana Umma tace"Kyale Sultana da Sakarci cewa tayi ta na so ta yi maka girki kuma ba Cefane sai nace to ta kiraka ta fad'a maka mana."
Yana kwance ne yasa ya gyara kwanciyarsa yana fad'in"Shikenan Umma dame dame ake bukata sai na je a siyo?
Cikin jin dadi Umma tace"Komai fa babu na Cefane, kuma kai da baka gama Jinya ba?
Mirmishi kawai ya yi kafin yace"Na warke Umma, na ma kusa komawa aikina in sha Allahu."
Jin haka yasa Umma ta fara yi masa addu'an tsarewa tare da Fatan nasara sun rabu tace anjuma yazo tana so ta yi mgana da shi tare da Sultana gabadaya yace mata toh.
Kasala ce ta Rufesa a lokacin domin ba su jima da gama waya da Siya ba itama Gobe zata koma gidanta tare da Inna Talatu da zata Zauna da ita.
Ya na Tunanin ya Tura mata itama kudin da za su yi Cefane duk da tace masa aikwai kayan abinci za su isa har yazo garin.
Hakanan ya mike ya sauya kaya, yasan in bai je da kansa ba sai Umma ta rike sa a ransa.

Saboda kafarsa da bata gama dawowa daidai ba, bai yo siyayyar da yawa ba kayan miya ya siya sai nama da kifi sai kayan lambu da Ruwa tare da lemu, kuma ba shi yaje ya kai ba Mallam tajudeen ya roka shi yaje ya kai ma su Umma sakon ya dawo.
Umma da kanta ta taya Sultana girki mai rai da lafiya.
Farar shinkafa da miyar naman Rago sai cowslow da suka had'a bayan sun gama ta saka Sultana ta tsala wanka da kwalliya ta na tashin kamshi.
Umma ta yi ta kuranta da cewa ta yi kyau ita kuma Fuskar Sultana ba Fara'a.
Dalilin da yasa Umma ta jata suka zauna bakin gado lokaci d'aya tana fadin"ko ke fa? Kin ganki kuwa?
Sultana ta wani kara bata rai, sai Umma ta yi mirmishi kafin ta gyara zama tana fadin"Na lura in ban yi miki bayani ba, zaki iya bani matsala gashi ni kuma a yanzu ke ce Makamina."
Cikin mamaki sultana tace"Bangane ba Umma?
Umma ta gyara zama ta na kara Fuskantar Sultana Lokaci d'aya ta na fadin"Saboda Matar nan ta Sadiq bakar Annoba Mahaifina ke neman yi min baki, sun  kasa Fahimtar abunda na ke so su Fahimta a dole sai na saka ma auransa da wannan Shegiyar yarinya albarka ni kuma na Tsaneta kasancewarta ita da d'ana a waje daya matsala ne, Shiyasa na nuna musu na Hakura komai ya wuce, yanzu haka nace Sadiq ma zamu je Zariyan na yi barka naga yaran saboda su kara aminta dani. Ke kuma daga bangarenki ki yi amfani da kissa da kissina ki na y'a mace ki san yadda zaki yi ki hana ta jin Dadinsa har daga karshe ma ki Raba su, sannan kema ki yi kokarin ki samu Ciki ki haihu sai naga zuciyar wa zata kama saboda Ta haifi yan Biyu."
Sultana ta yi shuru kafin tace"Kamar kin sani Umma, ni kaina yanzu bani da wani buri sai na ganin nima na Haihu kuma nima yan Biyu na ke son na Haifa Umma."
Ta karishe kamar zata yi kuka, Umma tace"Da ikon Allah ke yan uku zaki Haifamana ita din banza, shiyasa na ke so ki kwantar da Hankalinki zamu rika waya ina tsara miki wasu abubuwan, ni yanzu in nace zan kara yin wani abu ido na kaina sai mgana ta kara zuwa kunnen mallam kuma ya yi min gargadi a ka sake kawo masa karana wlh sai ya bace ni fiye da Tunanina, ni kuma na samu Dakyar na kira shi na bashi Hakuri shiyasa ke na ke son ki natsu ki bar mganar zafin kishin nan ki Tsaya ki kwace shi daga wajenta."
Sultana tace" anya Umma zan iyaa? Kina ganin yadda Yaya Sadiq baya ji kuma baya gani a kan matar nan fa."
Idanuwamta suka tara kwallah ta Cigaba da fadin"Ita ya ke so, ni ai matar chuse ce ba ni da Daraja a wajensa."
Umma tace"In ji waye? Yana sonki mana in da baya sonki da bai amince da auranki bayan ya aureta ba."
Sultana ta kalli Umma cikin wani yanayi tace"Umma ni fa ina jin haushin ace itace gaba dani, Mayar kwacen miji kowa ai yasan Yaya Sadiq nawa ne ni kad'ai."
Sai hawaye Umma na faman share mata ta na fadin"Kada wannan ya dameki ni a wajena bayan ke ba wata mata a gidan Sadiq, ki kwantar da Hankali da sannu zata fahimci karatun kurma."
Da wad'anan kalaman Umma ta yi ta lallashin Sultana har ta samu ta yi shuru kuma ta yarda da Shawaran Umma.

Sallar isha'i suka tashi suka yi, Abba ma ya yi mamakin da ya dawo gida ya iske bata dawo ba tana tare da Sultana har alokacin
Da ya kirata cikin Dariya tace Sadiq ta ke jira yazo ta had'a su ta yi musu nasiha sannan sai ta taho.
Shi har acikin ransa ya ke ganin Sauyawar Umma, tunda yasanta ko a baya da Tunani tare da hangen nesa kuma bai taba kamata da laifi irin wannan ba, shiyasa ta yi ta abubuwa shi kuma yana yi mata uzuri.
Umma ta gaji da jiran Sadiq har wajen tara kuma tana so ta koma gida sai ta saka Sultana ta kara kiranshi sai yace yana kan hanya.
Sanda ya shigo falon kallo d'aya ya yi ma Sultana ya kauda kansa ya maida wajen Umma.
Ita kuma Umma ta hau take mata kafa Shiyasa ta mike ta isa gabansa tana yi masa sannu da zuwa.
Ya kalleta sama sama sannan ya amsa yana karisawa kusa da Umma.
Cikin Ladabi ya gaisheta, ta amsa cikin Fara'a ta na kara tambayansa kafarsa yace ta kusa warkewa gabadaya Tunda yanzu ya daina yawo da taimakon Sanda.
Shine ma yake gayamata zai koma asibiti litini mai zuwa yaga likita.
Umma tace yakamata yaje a kara ganinsa.
Suna mganar nan Sultana taje ta kawo masa Ruwa Umma na ta faman mirmishi ta na fadin"ina ruwan Sultana."
Shi dai kanzil bai ce ba ya dai Dauki Ruwan da ta zuba masa ya sha Saboda kada ya kwabe kokarinta a gaban Umma.
Ganin Sultana zata shige Ciki kamar gaske Umma ta kirata ta dawo gabanta ta zauna.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.