Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 11 of 86

"Big sis Sadiq ko? Ko ba shi ba ne?

"In da naga Hoton, tace wai mata da miji ne?
Sadiq na da wata mata ne bayan Sultana?

"Kin yi shuru?

'"ni macen Hoton ne na ke ganin kamar na santa."

Sakon Saddiqa na karshe yasa Surayya ta kara Duba Hoton macen da kyau, Tabbas tasan wannan Fuskar, kuma kamar a gidansu ta taba ganinta, zama ta yi ta na kallon Hoton ta na so ta tuna inda ta taba ganinta Momorig lokacin na Shiga kanta.
Kamar an Tuna mata sai taji ta tuna a da inda ta tab'a ganinta kawar Saliha da ta zo bikin Sultana.

Da Sauri ta kira Saliha tace ta Hau chart zata Tura mata wani Hoto.
Gudun abunda zai je ya dawo sai ta yanke Hoton Sadiq ta Tura mata na Hasiya sai da ta tabbatar ta gani sannan ta  kara kiranta
Ta na Dauka Surayya tace"Saliha kamar kawar nan ta ki ko?
Saliha tace"Kwarai HASIYA ce. Ba ta zo min bikin Sadiq ba? Kin manta wacce na ce muku a kaduna muka had'u yar'uwan mijin Salima ce fa."
Surayya sai jinjina kai ta ke yi cikin Tsananin mamaki kafin tace"Na tuna ta wata tfara haka  har ma kika bani wayarki na yi muku Hoto ko?
Saliha tace"Kwarai ashe baki manta ba, bari na tura miki hoton ki kara gani, anan ta yi kiban fuska ne kila Saboda cikin jikinta ne, ni ban ma san ta na da ciki ba, kwanaki dai da muka yi waya tace min ta yi ta fama da Zazzabi."
Surayya sai ta kasa mgana ji ta yi zufa na keto mata ta saman goshinta, duk da AC Din da ke falon.
Cikin wani yanayi Surayya tace"Da bikin sun had'u da Sadiq ne?
Saliha ta yi shuru kafin tace"Gaskiya bazan iya tunawa ba? Hala me ya faru?
Da Surayya tace"A'a bakomai, wata kawatace naga ta  saka a status sai na ke tunanin inda na taba ganinta."
Da haka ta shanshantar da mganar Saboda kada Saliha ta fahimci wani abu.

Sai gashi kafin ma ta tambayeta Saliha ta fara gayamata Hasiya ta ja baya da ita, ba kamar farkon fara kawancen su ba.
Surayya ta koma ta zauna Dafe da kai bayan sun gama mgana da Saliha a waya.
Jikinta gabadaya ya saki bata so ma ta yi wani Tunani sai kawai ta fara maimaita"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un" a cikin zuciyarta.
Wacece wannan yarinyar Tare da Sadiq? Me ye alaqarsu da za su yi Hoto rike da juna haka?
A ina zata samu amsar Tambayoyinta?
Kiran Saddiqa ya katse mata Tunani da Sauri ta daga kiran ta na fadin"Saddiqa Sadiq ne a wannan Hoton."
Saddiqa tace"Innalillahi Sadiq ne?
Surayya tace"Ba tabbaci gareni ba, yakini ne da cewa shi ne Saddiqa"
Saddiqa ta share zufa kafin tace"To in dai shine to miye alakarsa da wannan yarinyar?
Surayya tace"Sunanta Hasiya, kuma yar'uwar mijin Salima ce, itace kawar da Saliha ta yi a kaduna, ta kuma zo bikin su Sultana Shiyasa ki ke Tunanin kin santa"

Saddiqa ta saki baki kafin tace"Tabbas an yi haka sai da kika fad'a na gane? Wacce Saliha tace ta tafi ba ta yi mata sallama ba?
Surayya tace"Saddiqa ki bar mganar nan a tsakanin ni da ke, zan yi yadda zan yi na binciko komai  ammh kema ta bangaranki ina so ki samo min address din in da yarinyar ke zaune."
Saddiqa tace"Big sis Khairiya tace min fa matar aure ce kuma a yadda abun ya ke, Sadiq shine mijinta wai"
Surayya tace"Duk da haka muna so mu san inda ta ke, ki kace a zariya ko?
Saddiqa tace"Eh haka tace"
Kawai sai Surayya ta yi wani Dariya takaici kafin tace"No wonder"
Daga haka ta katse wayarta, ta fara safa da marwa a tsakar falonta.
Ta na sake maimaita sunan Hasiya da Zariya.
Sai kawai ta fara Tunano yadda Sadiq ya nace ma karatu a zariya, ya gama yace bautar kasa, ya gama yace aiki zai yi achan sai ya fake da karatu, ta tuna ya na yawan ambaton wata ASIYA da sunan abokiyar aikinsa, kenan in ta hasaso daidai su Sadiq ya maida kananun yara ya ke wasa da Hankalinsu?
Koma wacece wannan yarinyar akwai alaqar da ta yi karfi a tsakaninsu wacce ba su sani ba, ita ko kadan bata bari Tunaninta ya bata wani mugun abu Sadiq ya ke yi ba, Tunanin ya fi karkarta kan abunda Sauran ba su hasaso ba.
Wayarta ta sake Dauka da Sauri ta Kira Salima ta na tambayanta ko ta na ina? Sai tace mata ta na makaranta.
Kai Tsaye Surayya tace"Salima me kika sani kan wannan yar'uwan mijin naki kawar Saliha?
Salima tace"Wacce Big sis? Ban ganeta ba?
Surayya tace"Wacce suka had"u lokacin bikin ki, ta kuma zo bikin su sultana.".
Salima da ke tare da Zahra'u a makaranta domin ta fara karatu a kasu, kaduna State University.
Tace"Oh na tuna me ya faru da ita?
Surayya tace"Kinsan ta sosai ne?
Salima tace"a'a ni ban kara ganinta ba, hala me ya faru?
Surayya tace"Taimako na zaki yi, ina son sanin labarinta ne, ko shi Mubark din ki tambayeshi mana."
Salima tace"Ok!
Sai Surayya tace zata Tura mata Hoton ta, Tunda ta lura kamar Saliman ba ta maida kai kan mganar da ta ke yi mata ba.
Da Sauri ta Bude data sai ga Hotunan Saliha ta Turo mata harda wanda ta yi mata ita kad'ai Tabbas wannan yarinyar ce.

Da Sauri ta Dauka ta Turama Salima, ta kuma kara kiranta tace ta bincika mata da Sauri don Allah.
Jin haka yasa Salima cikin Tunanin to lafiya? Ta dai san me ya had'a Big sis da neman Labarin wata!?
Sai dai sanin kawar Anty Saliha ce sai bata damu ba nan ta ke ta Bude datan ta, ta shiga ta ga Hoton da Big sis ta Turamata sai a lokacin ta kara gane Matar da ake mgana a kanta.
Zahra'u ce ta leka ta na ganin Hoton sai taga Hasiya da Sauri tace"Hala wannan ai Hasiya ce"
Salima sai ta kalleta kafin tace"Eh itace kinsan ta ne sosai?
Sai zahra'u ta girgiza kai kafin tace"Gasiiya ba sosai ba, ni ma da Bikin ku ne na santa, da ya ke Baba bai cika barin mu, muna zuwa zariya ba, sai dai su zo"
Sai salima tace"To ki tambayan min ko Baba ne kin ji ko?
Sai Zahra'u tace to shikenan zata tambayan mata, ammh sai da tambayeta me yasa ta ke son sanin Labarin Hasiya? Sai tace kawar yayarta ne ita ke son karin sani akanta.
Sai zahra'un ta gamsu da maganar Salimar kamar yadda, itama Salima ta gamsu da cewa dalilin da ya sa Big sis din ke son ta sani kenan.

Ita kuma ta bangaren Surayya, sai da ta gama Tunaninta gabadaya sannan ta daga waya ta kira Sajida tace anjuma tazo gidanta ta na nemanta.
Sajida kuma daman uwar son jin mgana ne da zence, ba jimawa sai ga ta tazo, itama Hoton Surayya ta nuna mata tace ko ta gane waye?
Da sauri ta Mike ta na kwalalo ido Lokaci daya ta na fadin"Mun shiga uku, kamar Sadiq?
Surayya tace"ai ba kama bace shine."
Sajida ta dafe kirji da karfi kafin tace"Shi ne? To ita wannan macen da ke tare da shi fa! Wacece?
Surayya tace"Shi na ke son sani yanzu, ki kara kallonta dakyau zaki ganeta, kin taba ganinta kawar Saliha da ta zo bikin sultana wacce tace yar'uwan mijin salima ce."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.