Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 45 of 86

******

Nayi matukar Farinciki ganin Anty Surayya, acikin raina nasan ya'yana a kallah suna da masu son su daga dangin mahaifinsu.
Innani kamar ta lashe yaran nan ta yi kuka kafin su tafi bata san iyaka ba sai ta kallesu sai ta koma ta na jan majina tana fad'in"Allahu akbar Ashe ina da Rabon ganin tsatson magajin gida ban mutu?
Mangaganu dai an sha su kamar ba Gobe sun yi ta tsiya da Siyama wacce tace Innani ta hanata ganin ya'ya.
Innani ta balla mata Harara kafin tace"Kaji min rashin kunya, to an hanaki ganin su d'in, in kin ji Haushi sai ki yi aure ki haifi naki."
Siyama sai hawaye Adda Fati ce ke faman bata Hakuri innani ko sai ta fara masifa Surayya na gefe bata ce komai ba ballatana Mama da in ta Tofa tasan nata sai yafi zafi.

Ba su wani dade sosai ba sallar azahar kad'ai suka yi da Adda Fati ta yi tayi suje gidanta su huta su ci abinci Anty Surayya tace za su tafi ne kada su yi dare.
Ita dai Surayya ta yi karan cewa Umma na yi min barka na amsa ba wai domin na yarda ba, Abba dai da tace na aminta tunda kafin Tafiyar Assadiq ya had'ani da shi a waya ya yi min sannu ta wayar Tahir.
Siyama ce ta bani mamaki itama da ko maganar arziki bata tab'a had'amu ba sai ranar.
Kuma ta yi ta daukan yan biyu Hoto a waya sai da tagaji, Surayya ta kawomin kayan da ta taho da shi Inna talatu ne ke ta yi musu godiya Tunda ko a jiyan ita ta kwana dani a madadin Amma.

Wajajen Biyu da wani suka juya sai dai an sha daga da Innani Domin tace ita bazata tafi ba jego tazo yi min.
Dakyar ta yarda suka koma da ita dacewa ta bari in taje ta gama Had'o kayanta gabadaya sai ta dawo.
Anty Surayya ta bani kudi 10k tace na rike a Hannuna kafin ta Dawo yadda bata min maganar abunda ya faru ba nima ban yi mata ba duk da dai nasan tasan abunda ya faru d'in.
Sai bayan tafiyarsu ne su Adda Fati ke hirar Rigimar Innani, ina dariya nace musu haka fa take, Assadiq na bani Labarinta Akwai aikin Tsufa a tare da ita.
Sai kuma suka koma mganar Mama da Anty surayya ce, sukace ta na da kirki duk da ba su san abunda ya faru ba ammh sun san cewa Dangin Assadiq ba su karb'eni ba.
Ni dai nayi shuru ban yi mgana mganar ma tawa ta karfin Hali ce tunda ruwa kawai na fara sha, likita yace sai da safe zan fara cin wani abu mai nauyi haka.
Bani da waya a hannuna shiyasa ban yi waya da Assadiq ba, ammh mun yi mgana da Anty Surayya tunda ta karb'i lambar Adda Fati ita ta kira da Daddare muka yi mgana na yi musu bangajiya.

Assadiq kuma sai washegari can da rana ya kirani da layinsa, ashe ya siya wata wayar ce sai ya saka layinsa, tunda wayarsa tasa da Atms dinsa da I.D card dinsa da aka gani wajen da Had'arin ya faru ya na Hannun Abba sanda ya koma ajiyan a daran tun kafin ya yi mgana Abba ya Dauko masa ya bashi shine da Safe ya siya sabuwar waya ya saka layinsa a ciki.
Haka na cigaba da zama a asibiti karkashin kulawar likotici, tare da yan'uwana Amma dai bata zo ba tace ga Inna talatu nan tare dani.
Sai dai matar Hamma Isuhu da Sauran matan kannensa sun zo sun dubani sun yi min barka suka koma.
Sannan matan Baba Tanko ma sunzo tare da wasu daga cikin ya'yansa.
Na yi mamakin inda suka samu Labari sai gashi suna fadin a bakin Baba Tanko su ka ji, shima yace Alhaji Jibril ya gayamasa na haihu kuma yan biyu ni kuma nasan a cikin gidansa yaji Tunda surukarsa kanwar Assadiq ce.
Su ba su yi wata mgana ba sai da Adda Fati ta kira Goggon kona ta fad'a mata ranar da na ke da kwana Biyar a asibiti sai gata tazo da yammah,.
A bakinta na ke jin yan'uwana Suka san yan'uwan Assadiq ni suka d'orama Alhakin Hatsarin da ya same shi.
Na yi ta jin Tsoro kada ta fad'i wata mgamar da zai saka su Fahimci abunda ya faru sai kuma bata fad'a ba.
Illah Adda Rukayya da ta yi Tsaki kafin tace"wannan ba bakon abu ne goggo. Abu ya sha faruwa a d'orama Hasiya alhakin abunda bata ji ba, kuma bata gani ba."
Goggo ta tabe baki kafin tace"To mutane fa suna amfani da abunda suke gani yana faruwa ne."
In da Allah ya taimakeni ba ta dad'e ba ta tafi da mgana ta fasu, kuma sai har bayan tafiyarta ba wacce a cikin su ta d'aga maganar tunda daman na fad'amusu abunda ya faru zuwana Gusau a karo na Biyu.
Sai washegari ne da Adda Fati tazo kamar daga sama ta jefamin Tambayar a ina Sadiq din ya samu hatsarin da ake kokarin d'oramin laifi?
Kai tsaye nace achan inda yaje aiki ne, bansan karyan da zan yi a gaba ba shiyasa na yi shuru da bakina, Sannan game da key din dakina karya na yi musu nace ya bace bansan inda ya ke ba, kuma na tabbatar musu ko Assadiq ba shi da wani key a hannunsa. Duk da akwai kayana da yawa acan sai Adda Fati ba ta maida kai ba, ganin har alokacin ina asibiti sannan ga Assadiq ya bar mata kudi kuma na kara mata kudin da Anty Surayya ta bani a Hannuna.
Kuma koda yaushe tana kirana tana jin Lafiyata ni da Twins ita da Assadiq.
Safiya ma kusan kullum sai tazo ganina sai a lokacin naga Khairiyya yayarta tare da Mamansu zuka zo dubani tare da ganin yan Biyu.
Ana gobe za'a sallameni Assadiq ya zo shi da Abba da kuma Baba Sammani sai Mallam Shitu da Auwalu da Ranar da Assadiq ya koma Gusau shima ya koma gida.
Ba ni kad'ai naji dadin Zuwan su ba harda su Adda Fati, duk da ba su dad'e  ba domin iyakarsu awa daya suka juya Assadiq ya sake siyamin kayan Tea da madaran yara da likita yace Saboda ruwan Nonon ya yi musu kad'an dole za'a rika had'a musu da Madara.
Bamu yi wata mgana ba illah Tambayarsa da Adda Fati ta yi in da zasu kaini bayan an sallameni yace a kaini gidanta bayan suna in an samu wacce zata zauna dani sai na koma Dakina na cigaba da Jego na.
Kudi haka su Abba suka bani masu yawa ni da yan Biyu ballatana da Assadiq yace tun ranar da aka haifesu ya saka musu suna Sulaiman da Muhammad.
Wato sunan Babana da sunan Abba, sai ga bakin mu ya ki Rufuwa ni da Adda, Abba ma ya yi ta saka albarka har a fuskarsa ya nuna jin dadinsa su mallam shitu ma suna ta saka albarka tare da fatan lafiya mai Dorewa dani da yaran gabadaya.

Washegari likita ya sallameni bayan ya bani dokoki saboda mikin dake jikina, kenan kwana shida na yi a asibitin gidan Adda Fati kuma aka wuce dani Direct dakin da Habiba ke kwana aka saukeni ni da yarana a ramar kuma Inna talatu ta saka Ruwan masu zafi ta yi ma yaran nan wanka suka yi ta tsala ihu nima kuma ta iza keyata zuwa bayi ta gasamin jiki na sosai ina wash wash ta na fadin kwana nawa na yi a asibiti da d'anyen jiki ba gashi ballatana wanka sai dai gogemin jiki kawai suke yi acan.
Bani da zannuwa Atamfa Adda Fati ta siyamin guda d'aya ta farkamin zannuwa uku ina sakawa, su kuma jarirai Adda Fati ta shiga kasuwa ta kara siyo musu wasu, kuma daman dayan akwatina duka kayan haihuwan da Anty Surayya ta siya ne aciki, Anty surayya washegarin ranar da aka sallamomi ta dawo ita da Anty Sa'ima ta zo min da Ferfesun kayan ciki mai yawa tare da Kayan jarirai sannan kuma ta ce ta zab'o ma ya'yanta sunayen yan gayu, Asif da Asim tace zamu rika kiransu Saboda Sakayawa.
Da ita ma mun yi mganar taron suna tace Sadiq yace sai sati ya zagayo za'a yi taron suna, bayan kuma ita cikin yan'uwan Assadiq ba wacce ta kirani sai Anty Saddiqa daga kebbi sai kuma Saliha da ita ba sau daya ta kirani ba sai Anty Sa'ima ta kirani Lokacin muna asibiti ina jin Anty Surayya ke ba su Lambar Adda ta nan suke mgana da ni.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.