Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 16 of 86

Shi kuma a satin Zariya ya kamata yaje, ammh ya riga ya yi kudurin Fad'ama surayya komai a kan Hasiya, sai ya kirata yace ta yi masa Hakuri yaje Gusai kan mganarta.
Ni kaina ya na gayamin ina share kwallah, bazan iya gayamasa ya yi jinkiri ba, ballatana na sanar da shi abunda ya ke so yaje ya fad'a sun san da shi kafin shi ya Furta musu.
Alkwarin da na yi ma Surayya na bazan fad'a masa komai ba yasa na kasa gayamasa komai.
Sai dai ina ta addu'an Allah yasa koma me zai Faru ya zo da sauki.
Sadiq yaje gusai, ammh kana ganinsa wani sukusuku, Sultana duk yadda ta Shiryamasa Tarba ya kasa sakin jiki, kuma har ita kanta bai wani yi mata rawan jiki da ya kan yi in ya zo ba.
A daran jumma'an duk yadda ta so su kad'aice bai biye mata ba, sai yace mata baya jin dadi, washegari kuma da Safe yaje gaida su Umma.
Ita kanta Ta Fahimci ya rage walwala ta tambayesa ko lafiya? Sai yace gajiyan aiki ne.
Abba ma sai da yace ko ya yi ciwo ne?Sai yace a'a, Abba kai Tsaye yace yaga ya rame ne, kuma ya rage walwala.
Sai ya kasa mgana, Daga Shashen Innani gidan Surayya yaje, sai dai duk kokarinsa da mganganun da ya gama Tsarawa ya kasa fad'a ma Surayya su  kuma bayan ita ba shi da wani Sauran Hope.
Zaune kawai ya yi tsuru a gabanta, ya kasa magana ya rasa ta ina ma zai fara, duk abunda ya shirya ganinsa gaban Surayya sai yaji komai kamar an shafe masa daga kwakwalwarsa.
Surayya ta kallesa shuru ta na nazarinsa, kafin tace"Sadiq me ke faruwa ne? Tun dazu ka yi shuru ka kasa mgana?
Sadiq ya runtse ido sannan ya Bude ya kasa had'a ido da ita, cikin jin nauyi da kunya yace"Big sis na rasa ta ina zan fara ne"
Da sauri tace"Ka fara ko ta ina Sadiq, zan fahimce ka."
Ta fad'a ta na fatan ya fad'a mata da bakinsa.
Ammh Sadiq ya kasa, ce mata kawai ya ke yi"Big sis na yi muku Laifi, a lokacin wlh zuciyata ba ta ganin komai sai na taimako, ku yafe min."
Surayya ta kallesa kafin tace"Me ya faru? Ka gayamin don Allah"
A gefe daya kuma daga shi har Hasiya suka bata Tausayi domin ta hango Tsaka mai wuyar da za su shiga.
Ammh abun Takaici Sadiq tafiya ya yi, batare da iya gayama Surayya komai ba, ya dai ce kawai yaci amanarsu su yafe masa.
Kasa fad'a mata ya yi, yace zai dawo gobe ya na tafiya sai ga  wayar Saddiqa, Surayya ta karanta mata yadda suka yi da Sadiq.
Saddiq tace"Wayyo Sadiq ya shiga Tsaka mai wuya, ni kaina ina fatan su Umma su Fahimcesa."
Surayya ta so ta kara Turke Sadiq in ya gayamata sai ta gayamasa komai ta kuma nuna masa kuskurensa ta yi masa adalci bisa gayamata da ya yi.
Ammh sai me? Ta yi ta kiran wayarsa bata samu sai ta kira Sultana, ita ke gayamata ya tafi zariya yau da safe dagachan zai wuce Abuja.
Surayya ta sauke numfashi, Sadiq me yasa ya ke haka ne?
Wannan fa gudun nasa ba mafita ba ne.
A ranar ta gama yanke shawaran abunda zata yi, ya kamata zuwa yanzu su Umma su san abunda ke faruwa.
Ba sai na nesa sun zo ba, ko da iya na kusa ne sun wadatar, Saddiq ta kira suka yi mgana, ta tabbatar mata da zuwa Jibi zata zo sai su taru su sanar da ma su Umma komai cikin Rukuni. Ba ta yi ta kan Sajida ba
ta lura so ta ke yi ta b'ata al'amarin to gwara tun kafin ta bata lamarin ita ta warware komai.
Sun rabu da Saddiqa akan Surayya zata Tura ma Hasiya Direba gobe ko jibin ya kawota gidanta ta kwana ranar Laraba da zasu taru sai ta taho da ita hakan zai fi sauki.

Bata kirani a ranar ba sai Ranar Litini da safe, lokacin ina makaranta Assadiq ya saukeni ya wuce Abuja.
A yadda ya zo min na yarda cewa yan'uwansa ba su fasa mganar ba.
Ammh mun rabu bayan ya tabbatar min da cikin Satin nan zai fad'ama Ahalinsa komai game da ni.
Bayan mun gaisa kai Tsaye surayya tace"Sadiq ya tafi ko ya na nan?
Cikin jin nauyi nace"Dazu da safe ya wuce."
Sai tace"Ki shirya zuwa gobe zan aiko Direba zai taho da ke wajena, ki shirya kayanki kamar kala uuku haka"
Cikin wani yanayi nace"Ba matsala ko Anty Surayya?
Da sauri tace"In sha Allahu, zan kira ki in zai taho."
Daga haka muka rabu, a cikin raina sai nake jin wani Tsoro.
Tsoron abunda zan je na tarar, abu biyu ne ko su aminta dani ma zauna cikin Tozarci ko kuma su rab'a ni da Assadiq sun yi min koran wulakanci.
In hakan ko ya faru na lalace domim bansan kuma wani mafita zan kama ba.

*Janafty*
*TMWBK3005*

*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*

https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk

Ku zo ku yi sayayya tare da Yar Gidan Imam cikin aminci da kwanciyar hankali komai akwai harda kayan gyaran jiki hamshakan mata na supliments kala kala wanda ba su da illa, akwai kuma gagarumin haÉ—in mu na Arabian sabaya powder wanda babu kamarsa wannan ba irin sabayar da ki ka saba gani bace, kayan kicin dogayen riguna kuwa ba'a magana ke dai ki yi sauri ki shigo domin kwasar roman wadannan kayan.

Washegarin Talata Saddiqa ta baro Kebbi zuwa Gusau, kuma ita kad'ai tazo ba tare da yara ba tace saboda makaranta sai ta barsu a gida tare da Babansu.
Zuwan bazata tayi, tunda ko Umma sai dai ta ganta kwatsam gashi motar haya ta shigo ta sha wuya, ammh abun mamaki ta na isowa sallolin da suka Subuce mata ta fara rankawa kafin ta ci abinci.
Ta na gama cin abincin sallar mangariba tayi, tace ma Umma zata je gidan Surayyah abun sai ya ba ma Umma mamaki, ganin ko hutawa ba tayi ba, kuma tace zata fita.
Taga kuma ko shashen Mama bata je ba, ta dai Leka shashen innani sun gaisa gashi ma Abba bai dawo ba.

Umma ta kalli Saddiqa na waya da megidanta, tana nazarinta sai taga kamar zuwan nata ya sha bambam da zuwan da ta saba yi, daga gani tafiyar tazo ne babu shiri.
Jin kuma tace zata je wajen Surayya da Daren nan, sai gabanta ya fad'i ta fara Tunanin ko wani matsala ne ya faru da Surayyan ba su sani?
Tunda ta kwana Biyu bata leko su ba, Umman ce ma ta kirata shekaranjiya sai taji muryanta wani iri, da ta yi mata mgana sai tace bata jin dadi ne.
Saddiqa ce ta katse ma Umma Tunani da cewa"Umma bari naje, kada na yi dare na rasa abun hawa."
Umma ta sauke ajiyar zuciya kafin tace"Saddiqa Surayyan ta na lafiya kuwa?  naga daga zuwan ki, baki huta ba kuma kin ce zaki tafi gidan Surayya"
Da sauri Saddiqa tace"Lafiya kalau fa, kawai ina so naje akwai mganar da zamu yi ne, kuma ba dadewa zan yi ba kila jibi zan koma."
Kamar Umma zata kara mgana sai kuma ta fasa, sai kawai ta ce "Allah ya kiyaye hanya, ki kwana achan kawai in dare ya yi."
Saddiqa na daukan wayanta da Jakarta na Hannu tace"Zan dawo Umma ai Bamu gaisa da Abba ba."
Ba'a son ran Umma Saddiqa ta tafi ba  ta na fita Haraban suka had'u da Mama zata zo shashen Umma suka gaisa itama da tace mata zata je gidan Surayya sai da ta kalleta kafin tace"Da daddaren nan Saddiqa? Allah yasa lafiya"
Saddiqa tace"lafiya lau Mama, bari dai naje ba dad'ewa zan yi ba."
Daga haka suka rabu, adaidaita ta samu zuwa gidan Surayya, Daman sun yi waya dazu da rana lokacin suna hanya ba ta riga ta iso ba.
Surayya na falonta zaune ita da yaranta suna homework sai ga Saddiqa cikin mamaki ta mike ta na fad'in"Saddiqa"
Cikin irin nayi mamakin ganinki a yanzu.
Saddiqa ta samu kujera ta zauna yaran Surraya suna gaisheta, karamar ta dauka saman jikinta Lokaci d'aya ta na fad'in"Ban dad'e da isowa ba, nace sai nazo ina so mu yi mgana, big sis ta na zamu fara kamo bakin zaren wannan maganar nan?
Surayya ta kalli yaranta lokaci d'aya ta na fad'in"ku shiga ciki khalil."
Sai da suka shiga cikin sannan ta mike ta na fad'in"Bari na kawo miki lemu da ruwa."
Saddiqa tace"Bar ruwan nan Big sis, ki zo mu zauna mu yi mgana."
Ba musu surayya ta dawo gefen Saddiqa ta zauna ta na fad'in"Ina jinki Saddiqa, ta ina ki ke ganin zamu fara?
Saddiqa na fuskantar ta lokaci d'aya ta na fad'in"big sis ni a shawarata ta inda aka hau ta nan za'a sauka."
Surayya tace"Kamar ya?
Saddiqa ta gyara zama ta na fad'in" Nufina anan shine Sadiq ne ya jawo komai saboda haka shi sai ya zo ya sanar ma su Umma da bakinsa, in muka Shiga fad'an da babu ruwan mu  fa? Kuma abun haushin ma ba da bakinsa ya fad'a mana ba, shi har yanzu bai samu lokacin sanin bai kyauta gamw da abunda ya aikata ba."
Surayya ta yi shuru kafin tace"Ban ki ta mganarki ba, ammh ni a shawarata tunda kin zo, ni da ke zamu tara su Umma mu sanar da su abunda ke faruwa."
Saddiqa ta zaro ido kafin tace"Mu kuma?saboda mene?
Surayya ta gyara zama lokaci d'aya ta na fad'in"Saboda Sadiq kanin mu ne."
Saddiqa ta katsesta da fad'in"Kina so ki nuna min zamu kare Sadiq a wajen su Umma? Zamu karesa big sis ki ke nufi duk a irin abunda ya aikata? Tabdijan wlh in muka yi haka ma gobe sai ya kara  ya ma raina mutane wlh"
Saddiqa ta karishe fad'a ta na Nuna bacin ranta kafin ta cigaba da fad'in"kuma suma su Umman ai su gani, tsabar soyayyar da suka nuna ma yaron nan da Abba da Innani, suna Fifita mganar Sadiq a saman ta su, ba dole ya je ya aikata abu mai girma haka bada sanin kowa ba, ya na Tunanin babu abunda zai faru ne shiyasa kika ga ya yi shurunsa ko ajikinsa fa."
Surayya ta yi mirmishi ba ta yi mgana ba, Saboda ta na Tunanin ba lalle in ta yi mgana kowa ya fahimceta ba.
Sanin tsakaninta da Sadiq yanzu sai ace shi ta ke goyama baya.
Tana cikin wannan Tunanin taji Saddiqa na kara fad'in"Nasan dai tsakanin ku da Sadiq akwai kauna, kin fi shakuwa da shi duk da yana namiji, ammh bai kamata ki goyamasa baya ba, tunda duk yadda ku ke bai iya samun ki ya fad'a miki ba."
Surayya ta kara yin mirmishi kafin ta muskuta ta na fad'in"Ke ma kina Tunanin ina Goyon bayan abunda Sadiq ya aikata ne?
Saddiqa tace"Haka ne mana, tunda kina so ya na chan kwance mu mu yi masa yakin a nan."
Surayya tace"Ba shi zamu yi ma yaki ba, Adalci zamu nema ma Hasiya."
Saddiqa ta yi karamin Tsaki kafin tace"Wacece wata Hasiya kuma? Chan ita ta sani, me ya kaita auran wanda bata sani ba?
Surayya tace"Kada ki manta itama ya yi mata karya, in zamu kalli abun ta fuskar adalci itama bai kyauta mata ba. Kuma ni wlh tallahi bazan kare Sadiq ko na minti d'aya a gaban su Umma ba, Hasiya da na yi ma alkwarin komai zai yi daidai ita zan nema ma adalci.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.