Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 15 of 86

Surayya da Sajida a kan hanyarsu ta komawa Gusai, Direba na gidan gaba ya na Tuki su kuma suna gidan Baya, Surayya ko mijinta bata gayama gaskiya ba,  Sai cewa ta yi Umma ce ta aiketa Sajida kuma zata rakata.
Kowannensu ya yi Shuru zuciyarsu na saka musu tunani iri iri.
Surayya tunaninta ya zurfafa sannan ba irin na kowa ba ne, Damuwarta daya ne yadda su Umma za su Karb'i mganar uwa uba kuma Innani tasan akwai babban kalubale, ballatana su san Labarin Hasiya, sannan ta ga alamun za su kyamaceta jin ita bazawara ce, sannan ga Sultana bata san ta ina zasu Karb'i mganar ba.
Ba ta jin Abba shi ya na da Saukin kai, Umma ce abun ji saboda ba lalle ta yarda da abunda zataji ko zata gani ba.
Sadiq ya yi kuskure kuma ya zama Dole a nuna masa rashin kyautawarsa, sai a yanzu abubuwa ke dawowa kanta daki daki ta tuna yadda aka sha fama da shi kan auran Sultana tun a wanchan lokaci ashe ashe ya na dalilinsa, daman ita fa ta yi wannan Hasashen na cewa akwai wani abu a zariyan nan da ya ke Dauke ma Assadiq Hankali, ta kira Tahir ta tambayeshi ya yi mata karya shima, ta na mamakin Wayau Sadiq har ya iya yin aure a boye ya kama ma matar haya suna zaune tare, har tsawon wannan Lokacin ba wanda ya sani abun a jinjina masa ne.

A gefe daya kuma na zuciyarta tausayin Hasiya ya darsun mata, Ba laifinta ba ne ammh sai ga shi ta na Shiga gagarin rayuwa saboda hakan, sannan har itama Sadiq ya yaudareta Don ma zuciyar macece da Rauni Sannan Tsskanin mata da miji sai Allah, ammh ai ko ta barayin hanata Haihuwa yaci Amanarta, ammh ko ma menene Allah ya nuna isharansa shi ya Kulla auran su, kuma shi ya nuna cewa akwai zuru'a a tsakaninsu.
Tunanin ta ya na tafiya ne kan yadda zata iya gayama Umma da Abba wannan Labarin.
Ba Sadiq zata taimaka ba, Hasiya ce wacce taji matukar Tausayinta ta na cikin wani Halin da ta ke Bukatar taimako, Sadiq kuma chan ya karata Shi da ya kira ruwa shi ruwa zai Cinye, zata dai Tsaya tsayin daka ta ga an yi ma Hasiya adalci ko domin cikin Sadiq da ke jikinta.

Ammh tabbas sai ya karb'i Hukuncin abunda ya aikata, sai ya gane ba shi da wayau bazata yarda ta karesa ba, Gwara ya gane kuskurensa nan gaba bazai kara gigin aikata haka ba.
Sajida ko acikin ranta ta gama kissima, irin yadda zata zuga Umma da Innani, in sha Allahu wannan bakar Annobar bazata zauna acikin zuru'arau ba.
Sadiq kuma ta zageshi a ranta bata san iyakata ba, Shege bata san Uban me ya gani a jikin wannan yarinyar ba farinta kamar na ma su cuta, ta gama tsara har Sultana sai taji mganar nan kuma zata zugata tace bazata zauna da Sadiq ba sai ya saki wannan Annobar.
Surayya kamar tasan Tunanin Sajida ta kalleta ta na fadin"Sajida kada naji mganar zuwan mu zariya a bakin kowa, Saddiqa kawai zata ji itama Saboda tasan mganar ne, ammh ban da Labarin Rayuwar Hasiya na baya Sajida ko a gida bazan fad'a ma su Umma canfin karyan nan da mutane ke yi a kanta ba, domin ni kaina ban yarda ba, sai dai ba laifin in sun ji cewa a bazawara ya aureta."

Sajida ta kalleta Sheke sheke kafin tace"Meyasa ba za su san abunda Sadiq ya kawo mana cikin zuru'a ba?
Big sis ki yi hakuri duka sai na karanta ma yan'uwa da su Umma gwara su san abunda ke Faruwa, kina fa ji da bakinta tace duk wanda ta aura ko rasa dukiya ko rasa lafiya, Sadiq kadai ne garemu namiji in wani abu ya same shi ba? kuma mun sani muka Boye wlh Allah bazai barmu ba, ni dai ba Ruwana bazan iya Boye wannan mganar ba ki yi hakuri."
Sai Surayya ta kasa mgana ta na kallon Sajida jin ta kara cewa"Kuma banda Sadiq ya yi asara me zai ci da auran bazawara? Bazawaran ma wacce ta yi aure Har biyu, abun takaicin ma  kuma yasan komai a kanta ammh kuma ya aureta a haka ba da sanin iyayensa  ba Dan Burauba ai ya yi asara wlh, ina sultana zata had'u da wannnan matar? Fatar jikinta kamar na mayu, har ga Allah ban ga abun so a jikinta ba sai wauta irin ta Sadiq."
Ran Surayya ya baci da Sauri tace"Ya isa Sajida, kar ki Rufa asirin kin Dad'e baki Tona ba, ammh ki saani wanda ya Rufa ma wani asiri shima Allah zai Rufa masa asiri ranar gobe kiyama, kuma da ki ke mganar bazawara kina Zagin dan'uwan ki, kin san adadin ladan da ya samu akan haka? Ba zaman bariki ya ke yi da ita ba Matar aurensa ce da shaidu suka shaida auran su, kinga kuwa ko wannan kadai ya isa ki yi salama ki kuma jinjina hikimar Ubangiji"
Sajida ta kyabe baki kafin tace"Daman Tun a dazun na Fuskanci zaki goyama Sadiq da yarinyar nan baya kamar yadda kika saba tsaya masa, ammh ina so ki sani ko Umma bazata taba karb'an wannan yarinyar da abunda ke Cikinta ba."

Surayya tace"Ni ba su zan tsayama ba, Ina bayan gaskiya ne, domin ita ba namu ba ne hakan baya nufin bazamu yi mata adalci ba, itama in zamu kalli abunda ta Fuskar adalci ya yaudareta kamar yadda mu ma ya yaudaremu, maganar Annoba da kike fad'i ki bari Allah ne ya Halliceta tare da kaddaranta ki daina Dariyann rayuwarta ke kuma kina alfahari da naki Rayuwar, mganar bazawara kuma kada ki zama Jahila Sajida, da ilimin ki da komai, ki ke so ki kawo wani karatu na banza wani nafsin ne yace ita bazawara ba Mutum ba ne? Ko kuma akace Saurayi ba zai iya auran bazawara ba? Kin manta da Labarin Annabi ne da Nana khadija? Ashe ko in da shi mu ke ko yi, mu al'ummarsa bamu isa mu kyamaci bazawara ba."
Sai ta yi shuru ta dakata, ta na lura da Sajida da ta koma ba ma yaronta Nono, kanta na gefe kamar maganar na Surayya ta na shiga ne ta na fita.

Ganin haka yasa Surayya ta Had'e rai kafin ta cigaba da fadin"kuma da ki ke mganar Umma bazata amince ba, daman bukatar shi ne a bi kadin auran a tabbatar da auran na gaskiya ne, bayan wannan ruwan kowa ne ya karb'i Asiya ko kada ya karb'eta ammh baku isa ku sauya wannan mganar na cewa itace Matar Sadiq ta farko, sannan har Abada ita din iyalinsa kinga shaida ma, tunda ga ciki kin gani a jikinta,ni bazan kara miki magiyan ki kama bakin ki ba, ammh ina so ki sani, ita Rayuwa ta na da Fad'i, kila watarana Asiya zata iya miki wani amfani ta fanni da baki zata ba, ko da ki ke ganin kin rainata."
Daga haka ta kama bakinta, ta koma ta na kallon tagar gefenta ta na ganin Dajukam da suke wucewa.
Sajida kuma ko a ranta ba ta ji zata iya Rufe wannan mganar ba, kuma har acikin ranta bata hango Sadiq ya cigaba da zama da wannan yarinyar ba.
Ta na jin Surayya na magana da Saddiqa ta na kara bata tabbacin da gaske ne Hasiya matar Sadiq ne ita ya fara aura a boye kafin ya auri Sultana, Dagachan Bangaren Saddiqa ta na ta salati, Sai dai surayya tace ta bari su koma gida za su tattauna yadda za su tari su Abba da mganar, ammh ko ita tace kada sauran su ji tukunna dai.
Wajen la'asar suka isa Gusai, har gida Surayya suka kai Sajida sannan Suka wuce gidanta.
Daren ranar ta kwana Tunanim mafitan yadda zata kai mganar nan gida ta kasa, wazhegari da Safe sai ga kiran Sadiq bayan ta Dauka sun gaisa bata nuna masa komai ba.
Sai yace zai shigo wannan Satin in ta na Free akwai mganar da za su yi.
Sai Surayya ta zargi ko daman shine maganar da ya kasa fad'a mata?
Sai ya ba ta Tausayi, da Sauri tace"Ina nan Sadiq, wannan wani irin mganace tun yaushe ka ke cewa zamu yita, ka kasa kuma fad'amin? Ina fatan dai lafiya ko?
Dagachan Bangaren Sadiq ya yi shuru kafin yace"Sai dai na zo big sis, ina fatan zaki fahimceni kamar yadda kika saba Fahimtata a baya."
Sai kawai Surayya taji kwalla ta cika Idanuwamta, sai tace ta na tsumayinsa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.