Tmw Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: TMW BOOK 3.txt
Chapter 73 of 86
Umma Mama na shashen Innani Naja taje ta kirasu Allah yasa bakin sun tafi a haraban gidan suka ci karo da Siyama ta dawo rakasu.
Suka dumguma bangaren Umma suka iske Sajida ta haye ruwan cikin Sultana ta na jibga.
Ga Ummi na kwace kan kujera kamar ta sani ta na tsala ihu.
Dakyar su Umma suka rabasu.
Sultana fuska ta kumbura baki da Hanci ya fashe ita kuma Sajida duk sultana ta cijeta ta yakushe mata jiki ta kuma yagamata riga.
Sannan ta riga jan gashin kanta har tana Cire mata tsinke kitson ta gashinta guda d'aya.
Umma cikin bacin rai ta kallesu kafin tace"Me zan gani haka? Sajida abun kunya da kanwarki kike dambe?
Sajida na haki tace"Na rantse sai naci Uban yarinyar nan".
Sultana na hawaye tace"Ba dai Ubana ba."
Siyama na gefe tace"Sultana baki da gaskiya miye haka?
Mama na gefe tace"To kana karami ma ina kai ina rashin kunya?..
Inaga tun mganar dazu ne ke sultana baki kyauta ba kamar tozartata kika yi."
Umma dai takaici ya hanata mgana ta koma daki ta zauna ta yi Tagumi.
Sultana kuma ta saka kuka tace an had'e mata kai saboda an ga ba gidan Ubanta ba ne.
Ta tattara kayanta da yarta ta tara Naja suka tafi.
Ita kuma Sajida na yi ta mata Fad'an ba girmanta ba ne ta tsaya ta na biye ma Sultana har ta kai su ga Dambe.
Siyama ma tace abun ba tsari.
Kuma daman Sultana ta zama mara kunya yanzu.
Sajida na kuka ta na gayama Mama da Siama irin tozarcin da Sultana ta dad'e ta na yi mata.
Su kansu sai da suka ga bakin Sultana suna mamakinta Aure ne ko iskancinta ne ba su san abunda ya sauya ta ba.
Umma ta kasa ko yi ma Sajida mgana saboda Haushi.
Sai da Sajidar ta sameta ta bata hakuri sannan ta gayamata duk abunda ya faru.
Umma tace"Uhm sultana sai shirin Allah, bai kamata ki zagi babanta ba tunda uba bai fi uba ba, bacin rai da kika Biye mata kina gaba da mijinta bama ita ba, ba girman ki ba ne ki zauna kina fad'a da ita."
Sajida tace in sha Allahu bazata kara ba.
Mama dai kusanta da rariyan baki ita takwashe labari ta gayama ya'yanta.
Surayya kuma Sajida ta je har gidanta ta na kuka tana gayamata abunda ya Faru.
Surayya ta yi ta ma Sajida fad'an wani irin raina kanta ta yi da Sultana zata yi dambe da ita?
Surayya tace"Ba ga shi nan ba, ina gaya muku gaskiya ke da Sadiya kuna gamin ina kare ma Sadiq ba, ai gashi nan ta nuna muku halinta, daman ina amfamin Babba ya rika shigema yaro da sunan ba shi shawara?
Wlh daman nasan haka zai faru."
Sajida na kuka tana fadin"Wlh naga abunda kike fad'amin a baya, don Allah ki kara bama Sadiq hakuri, Hasiya ma ki bani lambarta zan kirata na bata hakuri."
Da Farko Surayya taso ta Fattaketa ne sai daga karshe taji Tausayinta sosai..
Tace ta zauna gidanta ta kwana Biyu ta huta.
Sadiya ma da taji sai jikinta ya yi sanyi tace Lalle Sultana ta zama yar iska mara Mutumci.
Ta kirata a waya tanaa mata fad'an abunda ta yi bata kyauta ba sultana ta kashe mata waya.
Wato ba ta da Lokacinta Sadiya da zuciya ta shirya ta bita har gida ta mata Tas tace taji kunya.
Taje ta nemi wasu dangin tunda kuma ta raina gidan ubansu kada ta kara ganin kafarta a gidansu.
Sultana ta rika kuka tace sun ci mata Mutumci kawai sai ta shirya kayanta Bata so taje shinkafi Tunda ba mai yarda da ita acan.
Kai Tsaye batare da sanin kowa ba Washegarin Alhamis ta je tasha ta hau mota ita da Naja da Ummi sai garin Abuja.
Suna sauka ta daga waya ta Kira Sadiq tace gata a Abuja yazo ya Dauketa.
Yana Office ne zaune ammh sai da ya mike cikin mamaki yace"Abuja kuma?to ke da waye?
Kai Tsaye tace"Ni da Ummi da Naja."
Saboda tsabar mamaki sai da yavce"lafiya kuwa? Kin manta na fad'a miki gobe ina hanya tafe?
Cikin gatsali tace"Ina sane, wulakanci aka yi min acan shiyasa na taho wajenka in kuma kaima zaka wulakantani ne shikenan sai na san inda zani."
Bai Tsaya wani Tunani ba yace su tsaya a inda suka sauka gashi nan zuwa yanzu.
Har ya dauki mota ya fita yana tafe yana mamaki da Tunanin me Sultana ta zo yi a Abuja?
Yana hanya ya kira Umma yana gayamata ga sultana tazo Abuja ita kad'ai me ya faru?
Umma kai tsaye tace"To ina zan sani ni tunda ba ta daukeni uwarta ta gayamin gata zuwa ba? Sai ka je ka sameta in ka tambayeta sai ta gayamaka abunda ya kawota."
Daga haka ta kashe waya daganan yasan ba lafiya.
Shi tunaninsa yana zaman lafiyansa da iyalansa zuwan Sultana zai iya lalata masa yar natsuwarsa.
*Janafty*
*TMWB3K019*
*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*
‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/IhAz8h8nRy250ZnGGXwM65
A Jabi suka sauka na cikin Abuja shiyasa ya d'an dauki Lokaci kafin ya karisa, Sultana kuwa sai kiransa ta ke yi yana ce mata gashi nan bisa hanya.
Ya yi mamakin ganin Sultana yarkace yarkace kamar wata yar gudun Hijira daga ita har yar Rakiyan nata daga gani sun sha wuya.
Ummi ma sai rigima ta ke yi, Sultana uwar banza ce son jiki ya yi mata yawa wai Naja ta mika ma Jaririya ita ta na tsaye kamar wata sakara.
Shine ma ya yi saurin karb'an Ummin a hannun Naja ya kuma karb'i kayansu ya saka a bayan mota.
Da Mamakin Akwatin da yaga Sultana ta kwaso ya bude mata gidan gaba ta shiga ta zauna Naja kuma ta zauna a gidan baya.
Sun fara tafiya ya mika mata Ummi yace ta bata nono ta na kuka, ta karb'eta ta na tura baki. sai alokacin ya lura da kumburin fuskarta na Fad'an da suka yi da Sajida.
Cikin mamaki ya kalleta kafin yace"Me ya same ki a fuska kuma?
Kallonsa ta yi kafin tace"Bakomai.."
Ta fad'a lokaci d'aya ta na kauda kai can garin kalle kallenta Nono ya shake Ummi ta fara tari.
Sadiq ya fara yi mata fad'an meyasa ita ba ta kula ne?
Cikin gatsali tace"to ba ita ta shake da kanta ba."
Cikin Hararanta yace"Da ta shake ke kuma uwa mara kula ko?
Haka ake ba yara Nono? Kin sakar mata shi yaushe ta saba ballatana ta iya rike kanta, duka duka yaushe aka haifeta? Ya kamata ki rika lura Sultana kin girma tunda ki ka zama uwa yanzu."
Tura baki kawai ta yi bata yi mgana ba, sai shi nw ya nuna mata yadda zata saka Ummi a saman kafad'anta ta jijjiga ta na Buga bayanta tare da Hura mata kanta zuwa wuyanta.
Tana yi kuma ta na tura baki a Fili ya Furta"Allah ya sauwake miki, da kike son ki haifi yan biyu in da Allah ya baki na tabbata wlh bazaki iya renon su ba tunda ga shi guda d'aya ce ammh ta gagareki."
Da Sauri Sultana tace"Ai ko zan iya."
Kallonta ya yi ta kasan ido a rene kafin ya maida hankalinsa kan Tukinsa.
Batare da ya kara kallonta ba yace"Me ya faru ne a can gusau kika taho ba wanda ya sani.?
Kallonsa ta yi kafin tace"Umma ta sani mana."
Kai tsaye yace"Bazaki daina min karya ba ko Sultana?
To na yi magana da Umma kafin na zo nan kuma ta tabbatar min bata san kin zo ba."
Sai ta kifta ido kamar wata barauniya sannan ta wani tura baki kafin tace"Gidan mijina ne sai na nemi izini zan taho.?
Kai tsaye yace"Gidan ki na can gusau nan gidan Siya ne, kinsani kuma."
Hararansa ta so ta yi sai taga yana kallonta sai kuma ta fasa ta koma ta na sunne kanta kasa kamar wata munafuka.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.