Tmw Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: TMW BOOK 3.txt
Chapter 77 of 86
Ko da na koma daki yara duk sun yi barci sai na gyara musu kwanciyar, nidai har na kwanta ina jin ta shin muryoyinsu a falo suna Rigima kai wannan yarinyar akwai rigiman tsiya.
Da safe kuma ya kara Jaddamin Sultana zata yi girki.
Ai bayan fitansa har 3pm na rana bata Fito ba maga zan yini da yunwa ni da yara na tashi na Dafa muka ci.
Ba kunya da yunwa ta Ciyota sai ga ta fito falo muna zaune muna kallo
Naja ta kallah kafin tace"Ke ina abincina?
Ni yarinyar ta kallah tunda taga yau ban bata ba ta kai mata kamar yadda na saba ba.
Naja ko tace ai ban bata nace ta kai mata ba, sai kawai ta Wuce kitchen ta na fadin"Ba wanda ya isa ya hanani cin abincin da mijina ya siyo ya kawo"
Na so nace mata da ya siyo ai ban yi mata iyaka ba, gwara taje ta dafa da kanta bazan hanata ba.
Ammh sai na Tuna da wani abu sai na yi kamar ban ganta ba.
Kuma har na Daren bata girka ba, ni na girka shi da Assadiq ya dawo yaga bata yi ba zai yi fad'a na ce masa don Allah ya yi hakuri ya kyaleta ba girmansa ba ne ya Biye mata suna sa'insa.
Da kamar bazai hakura ba sai kuma ya kyaleta, kuma na rokesa alfarman ya rika kwana a dakinta har ta tafi.
Cikin Takaici yace"ta ce miki ta na da Niyar tafiya?
Nima cikin mirmishi nace"Bakomai sai na bar maka kai, har sai ka Gundureta."
Karamin Tsaki yaja kafin yace"Ban taba sanin yarinyar nan Fitinanniya ba ce sai yanzu acan ta gama yi ma kowa rashin kunya har su Umma bata bari ba, nan kuma zata zo ta hanani zaman lafiya"
Ni dai sai na cigaba da bashi baki har yace zai saka mata ido.
Tundaga ranar na dai binta da abinci acikin daki, sai dai ta fito in taji yunwa ta dib'a a cikin Kitchen.
Kuma bata ganin girmana ballatana in samu arzikin ina girka mata taci.
Gaisheni ma batayi sai dai ta shiga daki ta kwana da miji ta fito ta na Chab'a ado ta na isa da gadara ita adole gidan mijinta ne.
Assadiq bai gayamin Abunda ya Faru Tsakanin Sultana da Sajida ba.
Siyama ta kirani ta bani Labari tas, sai naji Tausayin Sajida har ga Allah na san zafin sakin aure sai naji kamar alokacin ya faru dani.
Kuma na bama Sultana rashin gaskiya, komai lalacewar Sajida ta na da kimar da bazata iya maida mata mgana ba ballatana ta yi dambe da ita.
Ammh Saboda bata da Mutumcin har Anty Surayya ma a halin da sultana ke nunawa zata iya sa'insa da ita, Siyama ta yi ta son taji ya mu ke zaune da Sultana? Bakina kanin kafana nace muna zaune lafiya saboda mene ita fa Sultana ta su ce, ni ce bare na zak'e watarana zata iya barewa dani.
Sajida kuma bata kirani ba, ta kasa kirana Saboda kunya.
Sai ni da kaina na kirata Tunda ina da Lambarta ashe itama ta karb'i lambata.
Ina kira ta dauka muka gaisa ta na rawan baki.
Ta kasa yi min mgana, sai ni ce na yi mata jajen mutuwar auranta.
Cikin Sanyin murya tace"Hasiya ki yafemin, na gama dariyan taki kaddaran ga tawa ta fad'amin.".
Kai Tsaye nace"Bakomai ni ban taba rike ki a raina ba."
Batare da na tambayeta ba ta fara bani Labarin irin rashin mutumcin Da Sultana ta rika yi mata abun ba dadin ji.
Ta karishe da cewa"Sai yanzu na gane a wannan Rayuwar da muke ciki in kaga kaddaran wani kada ka yi dariya Saboda baka san yadda taka zata zo maka ba."
Nace kwarai da gaske,hakane Allah yasa mu fi karfin zukatanmu ya kuma zaunar damu lafiya.
Mun jima muna hira da ita, ta na gayamin Yadda Sultana ta ci mutumcin su ta gudo nan
Sajida tace"Wlh in ta yi miki wani iskanci ki ci ubanta."
Ni dai dariya kawai na yi ban iya gayamata komai ba sai ma na kare sultanan nace muna zaune lafiya.
Umma ma mun sake mgana itama na nuna mata muna zaune lafiya.
Abunda ya ke bani mamaki da sultana Mace ce Fitinanniyar mara son zaman lafiya.
Duk hanyar da zata nemi fitina shi ta ke yinsa domin na tanka tamin Wulakanci, sai kuma ni ba na biye mata Tunda naga ko wanda ya Ijiyeta bata raga masa ba, ballata ni kuma saboda Tsabar rigima suna can suna ta karatu a makaranta ammh ita ba karatun ke gabanta ba.
Neman Fitina dani da rashin son zaman lafiya.
Shima na nuna masa tunda yasan Halinta ya daina biye mata, kuma ya daina mata mganar tafiya gaskiyanta ne itama ta na da iko da abunda ya ke mallakinsa ne.
Kuma Assadiq na jin mganata in dai na bashi shawara ya na dauka kamar yadda nima na ke daukan na shi Shawaran
Sai ga Sultana ta yi sati uku tare damu ta gama neman fitinarta taga bata samu abokin tafiya ba, dagani har shi mun koma mun saka mata na mujiya.
Duk abunda tace shi ta ke so ayi zan Taushi Assadiq nace masa ya yi Hakuri don Allah mu rabu da ita lami lafiya.
Ni fa har wake waken Habaici ta sha yi min na mai Farar kafa da bakar Annoba kala kala sunaye ta ke kirana da su har da bazawara mai kwacen miji.
Ban taba daga kai ba, na sakata a layin marasa hankali da sanin Ciwon kansu wlh.
Sai gashi da kanta tace ma Assadiq zata koma zasu fara Test a makaranta ammh suna gama Jarabawa zata zo nan ta yi Hutu.
Ni kuma a raina nace Gusau zan je na yi hutu na in tagama Hutun ta dawo nima sai na dawo.
Har Allah ka yi nisa da wanda baya kaunar ko ganinka.
Saboda ita ya yi shirin tafiya Gusaubni kuma sai alokacin na gaya masa na yaye su Asim
Ya fara min fad'a meyasa ban gayamsa ba nace zai hana ni, bai yi fad'an sosai ba saboda bai ga suna Rigima ba, ni ko abinci da kunu da tea na ke dora musu.
Kuma suna girma suna kara Rage Rigimansu.
Yace shikenan na Had'a musu kayansu Umma da Mama suna da manyan baki.
Nima yaso na shirya muje nace masa a'a sai nan gaba gwara na zauna a gida na yi abunda na kudura a raina.
A daran da zasu tafi na yi masa maganar kudurin da ke raina akan ina so na Rubuta Labarin Rayuwata da Tsaka mai wuyar da na shiga Saboda matsaloli irin nawa suna kara yawa acikin al'umma.
Na dauko Sreenshoot din abubuwan da na Dauka saboda na nuna masa, na irin Labaran da suka yi kamaceceniya da nawa Labarin.
Assadiq ya kalleni ina zaune a falo a gefensa Sultana ta shiga ciki bayan mun gama cin abinci.
Cikin son karin bayani yace"Tunaninki tunani ne mai kyau My Siya, sai dai yanzu in kika ce zaki yi wannan Rubutun ta ina zaki fara? Ke fa ba marubuciya bace?
Cikin kwarin gwiwan da na saka ma kaina nace"Zan nemi marubuta na yi shawara da su, ai ina tare da su ina karanta wasu daga cikin Littafan su. Ga Surayya Dee da muke mutumci da ita sosai Sanadinta ma nasan marubuta da dama dukkansu nasan in naje musu da mganata zasu saurareni kuma su bani shawara sannan ga Anty Habiba iman ikra tare da Anty Sumayyah Abdulkadir Takori da kuma AuntySis tsoffin Marubutan bugawa ne tun Lokacin duniya na kwance, dukkansu ina da kyakyawan tabbacin in naje musu da kyakyawan niyyata zasu bani shawarwarin ta inda zan fara in sha Allahu."
Cikin gamsuwa yace"Dakyau kuma duk wad'anda kika Lissafo duk marubutan ne?
Cikin sauri nace"Eh Sosai ma, kuma suna yin Rubutu cikin ma'ana da Tsabtar alkalami."
Assadiq yace"Shikenan bazan hanaki niyar alherin ba, tunda zaki Rubuta wannan Labarin ne saboda Mutane su gane ba mai yi sai Allah kuma Ubangiji bai isa ya yi ma bawa abunda Allah bai yi masa ba, In har goyon baya kike nema na baki dukkan Goyan bayana Siya ta."
Cikin jin dadi nace"Nagode Mijin siya, ina kara nenan wata alfarma"
Da sauri yace"Ina jinki fad'eta, in dai bata karfina ba zan yi miki "
Da sauri nace"Ka min jagora ka zame min ido a kan wannan abunda zan yi."
Hannuna ya rike kafin yace"In sha Allahu Matar Assadiq."
Mun Cigaba da Tattaunawa ina bashi Labarai masu ban mamaki irin labaran da na ke samu a kan masu Fuskantar irin tozarcin da na Fuskanta a baya.
Ya tambayani a littafi zan Fara Rubutun? Nace sai na yi mgana da d'aya daga cikin marubutan da na gayamasa shawaran da suka bani da shi zan yi amfani.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.