Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 71 of 86

A gidan Sultana ita da Farida sun ci aiki Tunda gidan ya ji ma kulle duk ya yi kura.
Suna cikin aikin Sadiya ta kirata tace gata nan tazo gida Umma tace ta na gidan Sultana suna gyara.
Sajida tace"Sadiya kinga yadda Rayuwa ta yi dani ko? Na zama yar aikin Sultana ina yayar mijinta na koma kamar kanwar mijinta."
Sadiya tace"Tabdijam, Allah ya kyauta."
Da Sajidan tace Sadiyan ta zo nan gidan su had'u sai ma ta tayasu sai tace megidanta ya yi tafiya daga kasuwa ta biyo gidan Umma gida zata koma zata yi masa girkin Tarba.
Kiri kiri Sadiya ta wucewarta gida kuma Umma ma da ta yi mata mgana haka tace mata.
Sultana kuma Saloon taje bayan ta dawo ta biya gidan kawarta ita ta rakata gidan kumshi aka yi mata.
Sai Yamma Sajida ta dawo sun gaji ita da Farida.
Suna dawowa ba dad'ewa Sultana ta Dawo Umma na ta fad'an ta yi dare ga jaririya a bayanta.
Kai Tsaye tace"Umma kunshi fa naje, haka zan koma jiki fari."
Umma ba ta yi mgana ba Sajida ma da idar da sallah bata tanka mata ba.
Umma taso ta tusa ma Ummi sai taga ta tashi tace zata shiga wajen Innani daganan ta wuce shashen Abba.
Mama bata nan suna kano bikin diyar kanwarta bangarenta kulle ya ke ba kowa.
Kawai sai ta isa gaban Sajida ta mika mata ta na fad'in"Anty Sajida ga yarki, ban yi sallar azahar ba ballatana mangariba."
Ko kallonta Sajida bata yi ta mike lokaci daya ta na fad'in"Salla zan yi, kin ji an fara kiran sallar isha'i."
Daga haka ta kabbarta salla tabar Sultana tsaye rike da yarta.

Ai ko ta gane bata da wayau domin Sajida na gama sallah ta mike ta shige ciki gashi taki yin shuru sai kuka ta ke yi damam kuma sultana bata saba ba, ta saba Umma ke mata reno ko Sajida yau kuma ba ko d'aya.
Duk ta yi wani yarkace yarkace da ita, A fusace ta shiga dakin ta iske Sajida kwance ta na Buga game a wayarta.
Kusa da ita ta tsaya ta na fadin"Gaskiya Anty Sajida baki da imani, kina jin yarinyar nan na kuka ammh kin kasa zuwa amsheta ki lallasheta sallah fa nace miki zan yi gashi har an yi isha'i."
Sajida ta dago cikin mamaki ta na kallon Sultana kafin tace"Ke ni sa'ar ki ce? Ko don kinga ina rage miki wahala shine zaki maidani kamar wata baiwarki? Yau din ma aikin Uban wa naje na yi ba naki ba?
Gabadaya jikina ciwo ya ke yi gidan nan naki bayan kura harda tsohon dattin kazantar da kika saba, nagaji ba daukarta da zan yi gwara tun wuri ki goya yarki ki kama Hidimarki kin ji ma na gayamiki."
Ta fad'a na juya mata baya Sultana ta kalleta rai bace kafin taja tsaki ta wuce.
Sajida ta mike ta na fad"in"Kan bu, Sultana ni ki ke ma tsaki?.
Sultana ta fice daga dakin tana fad'in"To haka kurun me kike yi? Daga nace ki taimake ni ki rikemin yarinya sai ki fara zagina, ni nace a sake ki da zaki wani Huce a kaina."
Sajida mamaki ya sandar da ita a zaune ta ciji yatsa sannan ta girgiza kaj lalle yarinyar nan bata santa ba ne sai ko ta gyara mata zama.
Kanwar dai naki dole Sultana ta goya yarta ta yi sallolin da ke kanta.
Sajida barcinta tayi bata san shigowar Sultana ba cikin dare Ummi na ta tsala kuka tana jin Sultanan na kiran sunanta ta yi mata  banza
Acikin ranta tace shegiyar yarinya mara Mutumci.
Washegari tun safe Umma tace Sultana ta shirya ta maida ta gidanta Anty Surayya ta zo, Sajida kamar an matsi bakinta ta kwashe rashin kunyar da Sultana ta yi mata ta gayamata.
Surayya ta kama baki kafin tace"Ita sultanan?
Sajida tace"Wlh ita fa Big sis ai bata da kunya shegiya da kauye ta girma da naga karyan tsiya ni ce zata rika sakawa aiki kamar ta samu wata jaka?
Surayya ta yi dariya bata ce komai ba sai dai ta bama Sajida Hakuri tace ta kama girmanta zata yi ma Sultanan fad'a.
Koda suka tashi tafiya Sajida kin zuwa ta yi, zamanta ta yi a gida daman kuma Yusuf ta ke yi ma nacin don Allah yazo su hadu ita ta bashi Hakuri ya maidata dakinta kafin ta gama Idda tagaji da wannan bala'in yarinya karama ta fara raina mata wayau.
Ta tuna kwanaki har sata ta kulla mata wai an sace mata 1k acikin jaka to waya sace ita ko? Tunda su biyu ne acikin dakin.

Abba shi ya  ba da kudi aka yi ma Sultana duk cefanem da ta ke Bukata, Umma da Anty Surayya ba su dade ba suka barota Bayan Surayya ta ce ta tashi ta yi girki domin tarban mijinta Tunda ya taso yace yana Hanya.
Suna fita ta koma ta kwanta ta na bama yarta Nono ta na kuma Chart.
Ita fa bazata iya ba ta na zuwa shinkafi zata Dauki Naja kanwarta ta so ta rika taimakamata.
Sadiq kuma da yamma ya iso gida ya fara Sauka sai a lokacin suka had'u da Sajida.
Kallon kallon suka yi ma juna afalon Umma kowa ya dauke kai.
Sai shine ya kalleta kai tsaye kafin yace"Sannu Sajida ashe kuma abunda ya faru kenan? Allah sarki zawarci ba dad'i ga shi daman kin tsani bazawara."
Sajida ta kallesa ta san mgana ya gayamata, kuma ba laifinsa ba ne da kunya ma ta maida masa martani.
Kasa mgana ta yi kanta na kasa tana Tunanin zama bai ganta ba.
Umma ke tambayan su Hasiya da yara sai ya ke fad'a mata suna Zariya taje karbo Result dinta daganan zata je can garin da Mahaifiyarsu ta ke ta Dubata.
Umma na zaune tace"Allah sarki, kwana Biyu bamu yi waya ba, ba na samun zama sosai Ga Innani ga Kuma Mama bata nan sun je biki."
Sadiq yace"Umma jikin Innani na kara Rikicewa? Yanzu fa na shiga ta na dai kwance ammh ba wannan kuzarin da karfin jikin nata irin na baya?
Umma tace"Ai innani jikin girma ya kwanta Sadiq, yanzu fa komai fa sai an yi mata jikin ya riga ya gama saki gabadaya."
Sadiq yace"Umma zan yi mgana da Abba za'a siya mata keken da zata rika zama a kanta ammh kwanciyar nan ai bata da dad'i."
Umma ta yi na'am da shawaransa sosai shiyasa yace zai tafi gidansa da Daddare zai dawo su yi mgana da Abba.

Yana fita gidan ni ya kirani yana fad'amin ya sauka lafiya.
Ni kuma lokacin ina gidan Adda Fati kwanan mu Biyu da zuwa ni da su Asim.
Sai na gama cuku cikun karb'an Result sannan zan karisa wajen Amma.
Shi ya ke fad'amin Umma na Cigiyata sai naji kunya nima kwana Biyu ban nemeta ba.
Muna gama waya dashi na kirata muka gaisa har na bata su Asim da suka fara mgana Umma rad'am a bakinsu.
Bayan nan mun yi mganar jikin Innani da ita, Innani na ran Assadiq koda yaushe sai ya yi mganarta har ce min ya yi ba domin kada Abba yace ya Dauke masa uwa ba da ya kawomin Innani wajena saboda gani ya ke a gabansa za'a fi kula da ita sosai.
Sai na koma ina gayama Adda Fati yanayin jikin innani, tunda gidanta na sauka ban je gidana ba.
Cikin Tausayawa tace"Allah sarki Allah ya tashi kafadanta, ni ko ina ita abokiyar zaman taki ta yi arba'in ko?
Kai Tsaye nace"Eh sun gama wanka naji Assadiq na mganar."
Adda Fati tace"Har yanzu baku da daidaita a tsakanin ku?
Nace"Babu kam,"
Adda Fati tace"Ki kyaleta ki dai ki yi mata zaman da musulunci yace."
Cikin mirmishi nace"To ni miye nawa? Da ba waje daya muke zaune ba."
Adda tace"Shikenan ma kowa ya Huta."
Mun cigaba da Hirarmu ina ba ta Labarin yadda sultana ta min wulakanci sanda na kira na yi mata barka.
Ammh ban bata labarin abunda ya Faru sanda muka je gusau ba, ko bakomai akwai sirrin da zan Boye musu saboda bansan me gaba zata Haifar ba.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.