Tmw Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: TMW BOOK 3.txt
Chapter 82 of 86
Sai washegari da bai fita aiki ba baya jin dadi zazzabi ya kwana da shi.
Sai nace ya kwanta a gida ya huta sai dai ya kira can wajen aikin su ya gayamusu.
Dani da shi ranar a daki muka yini, muna shan soyayyarmu da Hiran mu.
Muna kwance ya bani wayarsa ina kallon Hotona sai naa ga Ummi an Dauketa ta yi kiba kamar ba ita ba.
Sai na juya ina kallonsa ya na kwance ya Rufe ido ammh ba barci ya ke yi ba.
Tab'osa na yi kafin nace"Na manta ban tambayeka ba ya su sultana da Ummi?
Fata suna lafiya?
Assadiq ya yi shuru kafin can ya mike zaune da sauri yana dariya.
Cikin mamaki nace"Miya faru?
Cikin gyad'a kai yace"Sultana na can na kuka wai na yi sonkai na kara yi miki ciki ita ban yi mata ba."
Ido na zaro ina kallonsa shi kuma sai ya yi dariya kafin ya cigaba da fad'in"Wlh rigimar da naje tarar ta na yi kenan, tace ba na mata adalci ina Fitita ki a kanta, da farko cikin yan Biyu na yi miki ita kuma da ba na kaunarta d'aya na yi mata shine yanzu da son kai da rashin Adalci na yi miki Ciki ita ban yi mata ba to wlh itama bata yarda ba in ina son na zama mai adalci itama na yi mata ciki."
A tare da ni da shi muka Fashe da dariya cikin Dariya nace"Assadiq to kai baka yi adalci ba, me yasa ka dawo ba ka yi mata cikin ba?
Mirmishi ya yi kafin ya koma ya kwanta ya yi filo da hannayensa.
Cikin Tattausan lazafi ya kira sunana"Hasiya."
Na amsa masa sai ya mika Hannun ni kuma na kama ya jawoni jikinsa ya Rumgumeni na yi matashin kaina a saman kirjinsa.
Cikin Sanyin murya yace"Ina so na fad'a miki wata magana."
Cikin ba shi hankalina nace"Ina jinka. Sai ka fad'a"
Kai Tsaye yace"Kin san meyasa na gayamiki wani abu daya danganci sultana game da ni yanzu?
Sai na girgiza masa kai, yana shafa kaina yace"Saboda na nuna miki Sultana bazata taba sauyawa ba. Halinta ne haka zafin kishi zargi da kuma rashin son zaman lafiya, a baya na damu da Fitinarta ammh daga baya da na zauna ma Fahimci halinta har ga Allah lamarinta ya Daina damuna, can u just imaging ta tasani gaba ta na min kuka wai sai na yi mata ciki in ina so na yi adalci.?
Ina yar dariya nace"To sai ka ce mata mene?
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace"Me zan ce mata? Tun ta na bani mamaki sai ta dawo bani dariya da Tausayi, yanzu dai na lallasheta nace ta bari itama zan yi mata ciki tunda shi ta ke so"
Mirmishi na yi ban yi mgana ba shi kuma ya Cigaba da fad'in"Shiyasa na ke son na gayamiki ki yi hakuri da ita don Allah kin ji ko? Tunda mun san halinta mu zauna da ita a yadda ta ke"
Ina jinsa sai na gyad'a masa kai ina fad'in"Baka da matsala dani in sha Allahu"
Da bakinsa ya ke fad'amin wasu daga cikin Rigigiman su, wasu na yi ta Dariya sultana yar bala'i ce wlh.
Yace yanzu duk ta b'ata da su Sadiya aammh yasa ta ba su Hakuri.
Yace Har Umma fa in abunta ya tashi sai ta yi mata yaji tace an yi mata gori ko Umma ma nuna son kai.
Yanzu ma zuwan su Asim sai da tace Umma ta yi sonkai.
To itama Ummi zata kawo mata, Umma tace sai ta bari ta yayeta.
Ammh sultana bata ji ba sai ga shi ta had'o kayan Ummi ta kawo ta wajen Umma.
Ina Dariya nace"Kai to wannan jaririyar aka rabata da uwarta ai sai a dauki hakki."
Assadiq yace"Umma tace Shegantakan Sultana ya isheta wlh, sai da Abba ya shiga mganar yana ta lallashi yanzu dai tace itama ta na yayeta Umma zata riketa Tunda ta rike ya'yan kishiyarta."
Yana bani Labarin ina auna wasu abubuwan.
Nan take na kara tabbatar ma da kaina Sultana bazata tab'a sona ba.
Sannan ko kwanta mata na ke yi bazata bar kishi da ni da gasa dani ba.
Na fahimci duk wani abu da zata ganni da shi sai ta yi kokarin mallakan wanda ya fishi a Tunaninta ta fini, sannan ta na ganin Assadiq ya fi sona shiyasa ya ke nuna mata rashin adalci.
Alhalin adalci daidai gwargwado yana yi mata kishinta da Zarginta da Rashin mutumcinta yasa ta kasa gane komai.
Tundaga Lokacin na fahimci ita Rayuwa ba ta cika 100% bisa dari in kaji dad'i a wani bangaren Dole ta wani bangaren asamu akasin haka.
Sai ka yi hakuri da yadda taka Rayuwar ta zo, haka kila kafi wasu wasu ma sun fika.
Cikin ikon Allah na Cigaba da Renon cikina Amna wajen wata uku ta yi min sannan ta koma gida tunda za ta shiga makaranta.
Saboda nuna godiya da ni da Assadiq muka maidata har gida tare da shatara na arzikin da Assadiq ya yi mata.
Mun yi mata sabbin d'inkuna kayan kwalliya littafan makaranta da jaka da takalma Assadiq har karaman Ipad ya siya mata saboda karatu.
Adda Rukayya na ta godiya da Mijinta Adamu dai kamar ba shi ba.
Ya zauna da Mijina suna ta Hira har yana kallona yace"Ikon Allah Hasiya ki yi hakuri da abubuwan da na rika aikata miki a baya, wlh sai daga baya na kara gane cewa duk zencen mutane ne, sannan naji wani wa'azin kwanaki da akace rashin yarda da Allah nw in wani ya samu bawa yana nuna mutum bai yarda da musulunci da ya ke ciki ba kenan."
Assadiq yace"Kwarai ma da gaske, ai acikin shikan shikan musulunci akwai yarda da kaddara mummuna ko kyakyawa."
Sai ga shi zamu tafi Amna na hawaye nima wlh na saba da yarinya mai kwazo ga hankali.
Assadiq yace ta bar kuka duk sanda ta samu hutu zai rika zuwa yana Daukanta.
A gidan mu na zariya muka sauka da ya sha kura, Allh sarki maman suhailat sun tashi d anta ya gina gida sun koma can wajen kabama.
Ummi ma sun tashi gidan duk bakin Fuskoki ne.
Dakin ma Assadiq yace zai sake shi, sai dai in ya samu kudi ko karamin gida ne ya gina mana in da zamu rika sauka in mun zo garin.
Wannan zuwan da muka yi Amma ta matsamin sai na ne gidan Baba Tanko tare da Assadiq muka je har gidan Baba Saminu.
Sannan na kaisa gidan Goggon kona itama suka gaisa sai kuma jin kunya, suna ta kame kame a raina nace ku kuka sani ta bakin Amma tace mu mun riga mun sauke hakkin zumumcin da ke kanmu.
Kuma Assadiq ya yi musu alheri suna ta Tambayan yan biyu nace suna Gusau.
Hatta wasu daga cikin yayansu masu zagina da mugun baki na gansu, sai kunya da sunne kai.
Mugun abun da suka Rika jefani da shi ya koma musu.
Tunda cikin ya'yan Baba Tanko akwai sakakkiya auranta uku baya zama ta na gida, nidai nace alhakina ne ya kamasa da ya rikamin mugun baki in ma na yi aure bazan zauna ba Tunda na zama bakar Annoba gobara daga kogi mganinta sai Allah ba.
Daga zariya ne muka je Gusau nan muka yi jima Tunda Lokacin hutun karshen shekara ne.
Su Asim sun zama yan gusau ina wuri ma kamar ba na nan Umma da Mama ne iyayensu yanzu.
Muna garin Siyama ta haihu har aka yi shagalin suna.
A sunan ne su Anty Sakeena ta yi ma Sajida tsiya lokacin da bazawarinta ya kirata a waya.
Sai a lokacin naji ashe wani Tsohon saurayinta da ya nemeta tun tana Budurwa ne ya Dawo kuma abun mamaki bai yi aure ba shi har yanzu.
Saleema ta zo sunan itama da Cikinta Tunda sau biyu ta na samun b'ari.
Ita kuma asibiti ta ke zuwa Tunda in dai ta samu ciki sai ya zube.
Duk ta rame ta zub'e ba wannan gayun sai a hankali.
Shahida ke bada labari a wajen suna irin yadda Baba Jibril ya rika nuna ko Salimar ne ke da wani Laluran a jikinta? Kamar ya na nuna shi fa matsalan daga wajen salima ne ya manta Allah ke kashewa da Rayawa.
To ina Baba Jibril yasan Allah shi ban da neman duniya ai bai saka ma komai gaba ba.
Don ma Saboda Abba ne yana karuwa ta bangarensa da Tuni salima ta wulakanta kuma domin mijinta na sonta.
Ammh in akace Salima ta yi b'ari suna asibiti ji ya ke yi kamar kud'insa ne za su yi kuka ya yi ta mganganun rashin Takwalli.
Ni tausayi ta bani, ina auna irin yadda Rayuwar mata ke fuskata a wannan zamanin Allah dai yasa mu dace
Ya kuma cika zuciyoyin mu da Takwalli da yakana.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.