Tmw Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: TMW BOOK 3.txt
Chapter 58 of 86
Kuma duk Sajida ce ta saka mata wannan Tunanin na cewa hasken Fata kawai Hasiya zata nuna mata ammh jikin mata ta fita komai da ilimi da komai ita Hasiya Jahilar banza ce.
Sai daga baya take jin Hasiya da iliminta Tunda har Karatun Nce take yi a yanzu shima sai da ta tada masa Rigiman itama makaranta zata koma.
Shi ko yaso ya tafi da ita Abuja Tunda mganar Loan din gidan da za'a basu ya tabbata.
Tunaninsa sai taje can ta cigaba da karatunta ita kuma Hasiya sai ya dawo da ita nan Gusau, ammh Zargi da kishi suka rufe ma Sultana ido ta kafa masa kahon zugan Tunda Hasiya na karatu itama karatu zata koma shi kuma ba tashin hankali yace Allah ya bada sa'a, in an fara saida Jamb ta yi masa mgana ya siya mata sai ta Rubuta shi ba shi da matsala.
Duk irin abubuwan da ta ke yi masa bai taba daga baki ya kai karanta gaban Umma ba, gwara ma wani Lokacin ya na yin mganar da Big Sis, ita kuma sai ta rika Tausan shi da yarinta ke damun Sultana ya yi mata Uzuri, shi kuma abubuwa da dama ya ke dubawa ciki harda in yace zai Dauki mataki a kanta Umma ya ke ji, sannan mutane za su ce saboda Siya ne ya yi haka kenan zai goga ma Siya abunda bata san faruwarsa ba.
Ita kuma Surayya ta san harda Zuga ke dawainiya da Sultana kuma tasan masu zugata bata so ta gayama Sadiq ne tunda akwai yar matsa tsakaninsa da su Sajida har gobe bayan gaisuwa wata hira da ke shiga tsakaninsu a baya yanzu ta kare..shi ya riga ya tsame su gefe suma kuma suna ganin suna gaba da shi, shi ya kamata ya bi su. shi kuma ta bakin shi yace ba su Haifeshi ba sannan su suka Tsallake Hurumin da ba na su ba.
Kuma su dai suna iya bakin kokarin su wajen gayamata gaskiyan ta kwantar da Hankalinta ta zauna lafiya da mijinta watarana sai labari, ammh sai take ganin kamar ba gaskiya suke fad'a mata ba. Ba gidajen su har wajen Umma ta Dauke kafa ta Daina zuwa ita kuma Umma ta yi fushi tace a kyaleta Tunda Sultana ta nuna ta na da wacce ta fita, ta koma ta kama yan'uwanta na Shinkafi tare da matannin Ubanta shikenan.
Ita Umma Taurin zuciyar Sultana da Sakarcinta yasa ta fita sha'aninta, da abunda ta ke nunawa na Tsanar ya'yan Sadiq kiri kiri a gaban mutane ita bata damu in ta tsani Hasiya wannan Dabam, ammh yaran fa? Ko ta manta ba jinin Hasiya ne kad'ai ne a jikin yaran ba har da jinin Sadiq, kuma in da alkwari ai Ruwa bazai yi gangancin Dafa kifi Sadiq dan'uwanta da duk inda taga jininsa abun karramawarta ne, ballatana yanzu da ya ke matsayin mijinta.
Tasan da Farko har da ita wajen saka ma Sultana Tunanin Banza ammh Daga baya ta maidata gidan mijinta ta bata Shawaran ta zauna ta yi masa Biyayya da kissan nan na mata ammh Sultana bata ji mganarta ba, ita kuma yanzu Tsakani ga Allah yadda ta ke son yara nan duk wanda yace baya son su itama bata kaunarsa.
Sannan Tunda Mallam yace in da ace Sadiq bai auri Hasiya wannan Rabon ya'yan da ke Tsakaninsu ko da aure ko ba aure sai sun zo duniya.
Acikin zuciyarta taji ta saki komai, ta kuma san inda a lokacin Sadiq yazo da mganaar auran nan tana cikin yan gaba gaban hana lamarin, da Faruwar haka kuma daga baya azo a haifi d'a mara ido ai sai tace gwara da ya yi auran Boye duk daga baya gashi an samu mafita.
Kuma ta fara saki da kiyayyar Hasiya tunda bata taba kamata da wani hali na banza ba, balle ma zuwanta taga kunyarta da Hankalinta da Biyayyarta illarta Daya wannan bakin Canfin da ke tare da ita shi ke kara sanyayamata da Gwiwa, bata kaunar wani abu ya samu magajin gida da gaske ne d'aya Tamkar da Dubu ne.
Ita ce silar had'a auran Sadiq da Sultana tafi kowa son ganinsu tare, kuma ta na son ganin jikokinta ta Tsatson su, Sultana ita ta Rikete tun tana karama Sadiq kuma ita ta Haifeshi tana son su matuka, Soyayyar da ta ke yi musu ne ma yasa ta so kasancewarsu matsayin ma'aurata sannan zata fi kowa Murna in Sultana ta Haifa mata Jikoki.
Sai dai Rashin kunyar da Sultana ta yi mata sannan ta Dauke kafa da wajemta bayan taje ta na yawo da ita wai ta yi mata Gorin Haihuwa yasa Umma ta fita Batunta bata kuma kara bi ta kanta ba.
Kuma hakan da Sultana ta aikata ba wai wani jin dadi ya kara mata ba, kullum tana cikin kunci duk ta rame ta lalace sai kace ta na cikin Wahala.
Abun takaici shine kishin da Zargi sun kasa barinta ta samu sukunun zuciya.
Sadiq har fargaban zuwa Gusau ya ke yi yafi Murna da jin Dadi in yaje Zariyq Saboda yasan har ya gama kwanakinsa ya koma Faranta masa kawai siya zata yi, duk hanyar da zai Shiga Damuwa ta na nisanta kanta da shi.
Ita kuwa Sultana hanyar da zata bata masa ta ke nema, kuma komai zai yi mata sai tace bai yi mata adalci ba ga Zargin bala'i, satin karshe da ya sauka a Gusaubsai da ya yi mata kaca kaca haka suka Rabu zukata ba dad'i.
Bai san waya zaunar da ita ya karanta mata Ranar jumma'a ya ke zuwa zariya ba sannan kuma wai baya tafiya sai Ranar litini.
Kuma ita sai yazo mata Ranar asabar ya yi kwana daya ya koma ranar Lahadi, har ds cewa ita bata yarda ba in ma ana zaluntarta ne bata yafe ba.
Ya dad'e yana kallonta bakinsa a bude yana Tunanin wani irin sake ne ya yi ma sultana haka da ta rainasa?
Tsabar ransa ya baci ko bayani bai tsaya yi mata ba ya balbaleta da Masifa daga karshe yace an zalunceta ta jima bata yi Allah ya isar ba.
Ita bata ga yafi zuwa wajenta sosai saboda su Umma ba, Siya sai ya yi sati biyu har uku bai je ganinta ba.
Da Sun yi waya ya bata hakuri zata ce bakomai ita Kwanciyar hankalinta tajisa Cikin koshin lafiya.
Gusau kuma ya rantse da Allah in ya Dad'e ne ya yi sati Biyu bai zo ba ammh duk da haka bata gani ba har tana kiransa da azzalumi.
Ya fahimci wani abu ta na Dauka wani Rayuwa Siya ta ke yi mai kyau din da ta fi wanda take ciki, ita bata godema Ni'imar Allah da ta ke cikin Gidansa Ba na Haya ba, Allah ya jikan Siya da gidan Haya ta ke zaune kuma bata taba yi masa korafi ba ta zauma da shi Tun bata san cewa shi wani ne ba.
Shiyasa har Gobe Siya ta kwashe matsayi mai girma acikin Zuciyarsa, ita kuma Sultana abunda ta ke yi bata san a sannu sannu take sire masa ba.
Shiyasa wannan karon ya yi tafiyarsa Zariya wajen Siya da su Asim da suka kara wayau suna da wajen wata Hudu da kwanaki, kuma Satin Gusau ya kamata ya je da kuma ya koma Abuja. Ya share kafa ya yi zamansa sai dai ya kira su Umma a waya.
Da an tambayesa shuru bai zo ba sai yace aiki suka yi masa yawa.
Sai da ya yi wajen sati hud'u bai zo gusau ba kanwar naki sultana ta kama kiransa yaki ko amsa kiranta.
Har Tasasai take turamasa na mangaganu ya yi kamar bai gani ba.
Da kuma ya tashi zuwa ranar asabar ya shiga garin kuma da yammah Saboda ya kara nuna ma Sultana kuskurenta Gida ya sauka sai can dare ya isa gidansa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.