Tmw Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: TMW BOOK 3.txt
Chapter 2 of 86
Har wajen la'asar ina zaune ban samu mafita ba shed'an ne da kuma kishin Assadiq suka Ingizani na kira Saliha nace ta turomim adireshin gani nan zuwa, nan ta ke ko ta turomin ta na mai Farinciki batare da sanin mijina ko yan'uwana ba na shirya tafiya Gusai a gidan mu Maman suhailat kawai na yi ma sallama itama ban ce mata tafiya mai nisa zani ba, sai ita kuma ta yi Tunanin wajen Amma zani har ta na min fad'an na yi yamma, ballatana yadda Rayuwarnan ta lalace na rashin Tsaro.
Sai da na je tasha na hau Motar gusai har mun dau hanya sannan na fara nadama naji kamar na Dawo ammh kuma zuciyata na ingizani zuwa ganin abunda na ke so na gani ko kuma nace na kara samun Tabbaci.
Abunda ya faru dani, yau shine abunda Amma ke ta min gudunsa ta fad'amin kada na matsa da sanin abunda ba'a so na sani ba, in na matsa to zan zo na san abunda zai zama tashin hankali a gareni.
Shiyasa akace abunda Babba ya Hango yaro ko ya hau kan Rimi bazai hango shi ba.
Bansan Lokacin da na fashe da kuka ba, ina tuna Kasadar da na yi sai wajen goma saura na Dare muka iso mota ta lalace mana a funtua sai da aka dad'e sannan aka gyara.
Saliha na ta kirana nace mata muna Hanya, sanda muka shigo gusai na kirata na gayamata sai tace na tsaya a tashan tunda dare ya yi zata zo ta Daukeni.
Sun zo tare da wata itama yayar Assadiq ne tunda suna da yawa naji dai ta na ambatan sunanta da Yaya Saddiqa, sannan kuma inaga ta riga ta fad'a musu ni yar'uwar mijin Salima ne shiyasa suka saukeni Shashen Mama cikin kyakyawan Tarba.
Sai a lokacin naga Salima muka gaisa, yadda ta nuna bata sanni ba, ammh dai ta san Dangin Uban mijinta yan zariya ne.
Saliha ke tafe fad'in ta na da kawa yar'uwan mijin Salima, a kaduna muka had'u ga shi har na zo mata Biki, daga dare zuwa wayewar gari na kara yardan ma kaina Rayuwar Assadiq a zariya karya ce wannan itace Zahirinsa, naga ahalinsa gabadaya na kuma kara tabbatar ma kaina cewa shi d'in dan gata ne kuma ya ci sunansa Magajin gida.
Naga Umma da Abba, na kuma kara yardan ma kaina da zuciyata Assadiq ya yi nisa da Rayuwata kaddara ce ta had'a zaman mu waje D'aya.
Kukan da na ke yi yasa har sai da mai adaidaitan da na ke ciki ya juyo ya na kallona, ni kuma ganin haka yasa na yi Saurin shanye kukana, na koma ina faman goge Hawayena.
Ina Tunanin soyayyar da naga ana nun ma Sultana matar Assadiq, ina da yakinin yadda Suke sonta in Labarina ya bayyana a garesu ba za su taba karb'a na ba har Abada.
Mun zo ta sha ana kiran sallar mangariba ammh ban damu ba gwara komai zai Faru dani ya faru da ni a hanya, da na bari ya faru da ni a gidan su Assadiq.
Allah ya taimakeni na samu motar da ta taso daga Sokoto ta sauke wasu mutane a gusai, shi ne ma samu na shiga muka tashi da wuri, muna tafe ina bayan mota na Rufe rabin Fuskata da mayafi ina ta kuka ni kad'ai kamar raina zai fita ba kuma kukan kome na ke yi ba sai na Soyayyar Assadiq da Tunanin yadda Rayuwata zata kare in dan babu Assadiq a cikinta.
Wayata ta dawo dani hayyacina, ina Dubawa naga Saliha ke kirana Sai na kasa Dauka saboda bansan me zan gayamata ba.
Sai da ta yanke sannan na samu Damar Tura mata sakon ta yi hakuri mijina ya kirani yace bai amince na kara kwana ba, shiyasa na tafi ban mata sallama ba ammh ta yi hakuri.
Ina Tura mata sakon sai na yi kokarin kashe wayar gabadaya.
Sai ga kiran ASSADIQ ba kakkautawa, da ta katse kafin na kashe wayar sai wani kiran ya shigo, sai kawai na maida wayar jaka na Tusa kaina a Tsakanin Cinyoyina ina kuka.
Har muka isa zariya ina jin karan wayata a jaka tana virabtion daman Tun jiya na sakata a silent.
Motar ta yi gudu gaskiya wajen tara da wani abu muna zariya.
Daga tasha na samu mashin sai gida, kowa ya kwanta anguwan ma tsit kamar ba Mutane.
Na lalubo key din dakina a jaka na Bude kofa na shiga, nan falo na watsar da komai na kwanta a kasan Tayels ina kuka kamar wata karamar yarinya.
Halin da ni ke yasa na manta da cikina, sai chan da naji yunwa na mukurkusana na mike na saka Ruwan zafi na sha tea, sannan na Diba na yi wanka na Dauro alwala na Rama Sallar mangariba da Isha'in da suka Kubcemin.
A daran na kwana kuka da neman mafita daga karshe na bi shawaran Tahir na yin nesa da Rayuwar Assadiq a wannan Lokacin.
Na yi tunanin naje gidan Adda Fati sai kuma na fasa ta inda aka hau ta nan ya kamata a sauka.
Tun safe na tashi na fara had'a kayana acikin akwatuna, ina kallon kayan Assadiq ina kuka, ina kallon dakin ina Tuna Momemt din da muka yi tare cikin Farinciki.
Wata zuciyar tace karatun ki fa? Sai ma kara gayama kaina Tunda na Rabu da wanda ya yi min sanadin karatun to miye amfanin karatun a wajena? Babu ya zama Dole na tafi tun kafin abubuwa su zo su faru ba daidai ba.
Sai da na gama had'a kaya na duka, na yi tunanin zan tafi da su na bar wasu, sanda na Dauko wayata Assadiq ya kirani yafi sau arba'in sannan ga sakon sa nan na magiyan na Daga wayarsa na kuma Sauraresa.
Ban bi ta kansa ba Sakon Saliha kawai na Bude ta nuna bata ji dadin na tafi ban yi mata sallama ba.
Sai kuma kiran Safiya Ahmad kila mganar makaranta ne, itama ban bi bayanta ba na kashe wayar gabadaya na turata a cikin jaka.
Ban so na kara kwana a garin zariya ba, a niyyata sai a wajen Amma naje na gayamata garejin da ta yi ko nace kuskuren da Soyayyar da ta ke min yau ga abunda hakan ya janyomin.
Sai dai me? Ciwon kai ya matsamin daman Tunda na tashi da shi na tashi sai ban bi ta kai ba tunda daman na kwana kuka daman na yi Tunanin haka zai faru.
Ina ta karfin hali had'a kayana da kauda wasu, sai kuma zazzabi ya Rufeni, na had'a tea domin na sha Tunda ba ni da kuzarin dafa abinci sai amai komai da naci tundaga jiya sai da na Amayar da shi ba komai acikina sai Kakarim Aman na ke yi ba abunda ke fita acikin cikina.
Wasa wasa kafin Dare zazzabi da kasala da Ciwon kai ya kwantar da ni, sai taruwan miyau a bakina, jikina har ya saki ko sallah sai dai na yi a zaune, haka na kwana na yini cikin wannan Halin su Maman suhailat kuma ba su san dawowata ba, balle su lekani su gani kuma tunda na Dawo ban fita ba, sannan kofata na kulle.
Ba na iya cin komai sai Ruwa shima da naci zan yi amansa, ranar talata da naga zan mutu ne na had'a tea da Ruwan sanyi na sha a falo na yi amansa ban iya tashi naje Tiolet ba.
Jikina gabadaya ya saki duk na Rame sai Idanuwana da baki da Hanci daman gashi komai nawa karami ne ballatana ya had'e da cuta.
Ranar Laraba ina falo kwance saman Tayels kamar ruwa ina maida Numfaashi naji muryan Safiya suna mgana da Ummi.
Ta na ce mata kamar ba na nan fa, na yi tafiya, Safiyan na fadin ta yi ta kiran wayata a kashe.
Gani na yi in na bari Safiya ta bar gidan nan zan mutu acikin Daki ba wanda ya sani.
Da Rarrafe na Rarrafo har kofar daki na Bude lokacin har Safiya ta juya zata tafi, ita kuma Ummi daman da ta fito shanya ta koma Dakinta.
Sai dai Safiya taji ina kiran sunanta cikin Dakushewar murya.
Cikin mamaki da juyo ganina kwance a bakin kofar dakina ina maida numfashi yasa ta nufeni hankalinta tashe ta na kiran sunana.
Cikin firgici tace"Hasiya me ya faru? Ba ki da lafiya ne?
Ta na mgana ta na tab'a jikina da taji kamar wuta.
Miyau na bin gefen bakina nace"Safiya ba ni da lafiya, komai baya zama a cikina sai na yi amansa kamar zan mutu."
Safiya na jin haka ta taikamin na mike muka koma cikin Daki, ita ta Daukomim wata Riga na sauya duk da taga kayana a had'e bata damu ba tunda ance na yi tafiyqa kila na dawo kenan na fara rashin lafiya.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.