Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 14 of 86

Ta kasa dago Hasiya, kamar wani shashe a ranta ya Tausayama Hasiya, sai kuma yanzu ta kara yarda da Dalilin Da yasa Sadiq ya aureta Tausayi ne da Taimako daga karshe kuma Allah ya rubuta da akwai Rabo da zama mai Tsawo a tsakaninsu.
Sajida kuma ido kawai ta ke zarewa cikin Firgici ta ijiye yarinyarta a gefe ta mike ta na fad'in"Ki ka ce auran ki na Biyu Sadiq ne na uku? Mun shiga uku mun Lalace Taurin kan yaron nan ya sa ya jawo mana Mugun iri acikin zuru'a? ammh uwarki dai itace batulu duk alherin da ya yi mata sai ta saka masa da Sharrin Bin Rayuwarsa? Ai tasan ke Annoba ce meyasa ta nace sai ya aure ki? Wannan wlh zalumci ne, in wani abu ya samu dan'uwan mu na rantse da Allah sai Abba ya karar da duka Ahalin ku, matsiyatan banza kawai da Wofi."

Ta fad'a cikin bacin rai, Surayya da ta daka mata tsawa cikin Fushi ta kira sunanta" Sajida."
Sajida cikin fusata tace"Big sis ke baki hango abunda na hango ba ne? Sadiq kadai garemu yanzu in wani abu ya sameshi ya zamu yi?

Kai Tsaye Surayya tace"Ba bu abunda zai same shi face abunda Allah ya tsara masa, da zai samesa da ya samesa Tuntuni, tunda ba yau suke tare ba, ki koma ki zauna ki kuma Rufemin bakin ki anan wajen"
Sajida ta koma ta zauna ta na fad'in"Bazawara! Bazawara Kai ina wannan Had'in kwata kwata bai yi ba, da sake wlh"
Ta fad'a ta na jin kamar ta Rufe Hasiya da duka, tsanar ta taji ta kara shiga ranta, daman tun jiya ta ke tsine mata tun kafim ma tasan abunda ke Tsakaninsu.
Ina duke gaban Surayya ina kuka bani da tacewa domin nasan irin wannan Ranar ta na zuwa.
Surayya ce ta saka Hannu ta Dagoni ta kuma mikar dani Tsaye ta zaunar dani saman kujera ta na fadin"Ki rage wannan kukan kin ga Halin da ki ke ciki ko?
Fuskata Hawaye shabe shabe da hawaye da majina na kalleta ina fadin"Bazaku rabani da Assadiq ba ko?
Sai kawai ta yi min mirmishi kafin tace"Bamu isa mu rabaki da mijin ki ba, tunda ai bamu muka had'a ku ba Allah ne, ki kwantar da Hankali in sha Allahu Alherinne zai Biyo baya."
Ban san Surayya Sosai ba  ammh kuma sai naji na aminta da mganarta.
Da tace na daina kuka sai na Daina na koma saka bayan Hannuna ina share hawaye.
Sai da na natsu sannan Surayya tace"Duk da ina Babba  bani da ikon yanke komai a rayuwar Sadiq ya na da magabatansa, zamu koma gida zan sanar ma iyayensa, so na ke Sadiq ya Fahimci Babban Kuskuren da ya yi, na yi aure ba da sanin iyayensa ba."
Sai ta d'an dakata ta na Kallona kafin tacigaba da fad'in"Hasiya ki kwantar da Hankalin ki, kema ba laifin ki ba ne ya zauna da ke da karya kamar yadda muma ya lullubemu cikin karya, ki yi min alfarma Rufe zuwan mu a matsayin sirri bazaki taba bari Sadiq ya sani ba kin ji ko?
Sai na gyad'a mata kafin nace"Bazan gaya masa ba, daman kuma ina ta ce masa ya sanar da ku game dani, sai yace yana jiran Lokaci ne, abunda na ke tsoro kenan ko da yaushe ina cikin Fargaba, ina tsoron kada daga baya ku zo ku sani ku ki karb'a na ni da Abunda ke Cikina."

" Ai ba zamu taba karb'an ki ba, Daga ke har shegen cikin jikin ki, da kike kokararin Dangantamu da shi, mu Sultana Kad'ai muka sani matar Dan'uwan mu, in dai ba ita bace ta haihu bazamu iya karb'an Datti acikin Zuru'armu ba."

Sajida ta fad'i haka cikin Tsanar Hasiya har ya na bayyana a saman fuskarta, sai na kasa kallonta Saboda yadda naji kuka ya tasomin sai kawai nace"Ku yi hakuri don Allah, kada abunda ke cikina ya fuskanci hukuncin da ba laifin sa ba ne."
Surayya ta balla ma Sajida Harara kafin tace"Wlh da na san abunda zaki yi kenan da ban zo da ke ba."
Jin haka yasa Sajida ta yi shuru, ammh ta na ta kunkuni ita kad'ai.
Surayya ta yi banza da ita, ta koma ta na kallona cikin sanyin murya tace"Kada ki damu Hasiya kin ji ko! Tunda har kun yi aure komai zai zo da sauki, ki rufe wannan mganar in muka koma gusai zan sanar da su Abba, kila akwai bukatar ki zo Gusai Domin tabbacin, zan baki lambar wayata in bukatar hakan yaa ta so Direban da ya kawomu zai zo ya Dauke ki kin ji ko?
Cikin Tsoro na kalleta kafin nace"Assadiq fa?
Surayya tace"Zai san komai Daga baya, kada ki damu ki yarda dani."
Sai na kasa musa mata, wayarta ta Dauka ta yi danne danne.
Sannan ta Dago ta na kallona kafin tace"Na kira ki da lambata, ki adanata zan kira ki in sha Allahu."
Sai na bi ta da kallon mamaki ina ta samu lambata?

Kamar ta sani sai ta fara min bayanin ta inda suga hoton da komai.
Surayya ta ce"bamu sha wani wahalan gane gidan ba, tunda baya cikin lungu, sai dai mun shiga wani gida achan baya matar gidan ne tace mu zo nan ta na Tunanin ke ce'"
Sai na kasa mgana ina kara jin Tsoron Rayuwa zaton abunda ba ka yi zato ba.
Ko ni bansan Safiya ta Tura wannan Hoton ba, sannan bani da masaniyar yayarta khairiya na mu'amala da Daya daga cikin yan'uwan Assadiq.
Surayya ce kad'ai ta sha ruwa  har na samu karfin halin cewa zan musu girki tace za su tafi ne ba wanda yasan sun yi wannan tafiyar.
Har ga Allah sai naji Surayya ta Burgeni baki ta ke ta bani ta na lallashina akan na daina kuka ko Damuwa ta na da tabbacin Komai zai zo da sauki na kwantar da Hankalina Sajida ko da mun had'a ido sai ta harareni da kallon Tsana, daman nasan ba kowa ne zai karbi mganata ba, zan Fuskanci tarin kalubale.
Tun ballatana da za su tafi, surayya ta rike hannayena ta na kallon cikin Idanuwana tace"Ki kwantar da Hankalinki Asiya, ba bu abunda zai Faru Sadiq kanina ne kuma Favorite d'ina, ya na ji dani, nima kuma ina ji da shi, kaf gidanmu ba shi da abokiyar shawara kamata, na yi mamakin da bai iya sanar da ni labarin ki ba, na yi masa uzurin Halinsa ne na Taimakon wanda ke neman taimako sai dai bazan taba masa uzurin boye mana wannan gagrumin abun ba, Tunda abu ne da ya shafi aure da Rayuwa gabadaya,so ki kwantar da Hankali komai zai wuce in sha Allahu."
Sai naji hawaye sun cikamin kwarmin Idanuwana, na fara yi mata godiya tace min bakomai.
Sannan ta yi ta jadaddamin na cire damuwa har ta na zolayata akan ina Dauke da Bbyn su, kada na yi musu asara sai ga shi ina Dariya.
Sajida ko ta fita mota, saboda ta kasa zama gani ta ke yi kamar kunnuwan Surayya Hala sun toshene da ta tsaya tana Saurarena kuma har ta na Neman Goyen bayana.
Suna tafiya na koma falo na zauna kan kujera, na saki kuka  ta wani bangaren in na duba Surayya sai naji kamar na samu salama, ta wani Fannin kuma in na Tuna ire iren su Sajida sai naji na Raunana, na Shiga uku ina zan saka kaina in har Assadiq ya rabu da ni? Na tabbata Rayuwata sai ta fi baya kuntata matukar haka ya faru.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.