Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 54 of 86

Saboda jin Hauahinsa a d'ayan bedroom d'inta ta kwana, da Safe kuma ta yi kwanciyar ba ta yi abun karyawa ba Sadiq ko bai ko Tsaya ba ballatana ya wulakanta
Da kansa ya shiga kitchen ya Dafa Ruwan zafi sannan ya soya kawai yazo ya had'a Tea ya sha da Kwai tare da Buredi.
Yaso ya kai gobe da Safe ammh ganin iskancin Sultana yasa ya yi shirin komawa Abuja a ranar.
Bayan ya gama karyawa ya koma daki ya kira Siya suka yi ta waya suna shan Soyayyarsu sai sha Biyu ya tashi ya yi wanka ya shirya ya Dauki Mota ya fita daga masallaci ya shiga gida ya gaida su Umma, Ko alokacin sai da Umma ta kara tambayarsa Yaushe su Asim za su zo? Yace sati mai zuwa.
Sai ga Umma cikin Fara'a ta na fad'in"Ma sha Allah, ammh za su kwana Biyu ko?
Kai Tsaye yace"Eh sati nace za su yi, ko ba na nan sai direban Abba ya maidata gida tunda ga yara."
Umma tace"Eh hakane kam,"
Suka yi shuru na wani lokaci shi yana Duba wayarsa ne.
Tahir ne ya ga kwana Biyun nan gabadaya in dai ba abun siyasa ba gabadaya post dinsa na Soyayya ne, to ya fara zargin wannan karon Tahir ya fara soyayya gaskiya ya daina yaudaran ya'yan mutane.
Hankalinsa na kan wayarsa yaji Umma na tambayarsa can gidan Siya zata sauka in ta zo kenan?
Sai ya maida wayarsa aljihu Lokaci daya ya na kallonta kafin yace"Eh haka nace Umma, tunda ina da gida bai kamata ta rika sauka gidan big sis ba."
Umma ta jinjina kai a zuciyarta kamar tace to ta sauka a waje na  mana Saboda su Asim ammh sai ta kasa mgana shi kuma ganin haka yasa ya kara kallonta yana fad'in"Ko hakan bai yi ba Umma?
Da Sauri tace"Ah ya yi sosai ma, Allah ya kawo su dai lafiya."
Ya amsa da Ameen Ameen daganan yace mata yau zai tafi, bata masa mganar Sultana ba sai da taji yau zai koma cikin mamaki tace"Yau kuma? Sultanan bata dawo ba ne?
A dakune yace"Ta dawo mana, ina da ayyuka a office ne gobe da Safe."
Nan dai ta yi masa Fatan alheri ya sallameta daganan ya shiga bangaren Mama ya kara yi mata gaisuwa duk da har gidan gaisuwan yaje.
Daganan da ya fito sai ya shiga bangaren Innani ya iske ta tare da Farida da Siyama suka gaisheshi.
Innani na ganinsa ta washe baki ta na yi masa kirarin baban yan Biyu.
Bai jima a wajenta ba ya yi mata sallama ta shiga kwarara masa addu'a tun ballatana ma da ya bata kudi.
Yana jinta yan Biyu da mamansu sun sha addu'o'i.

Abba baya nan sai dai ya kirasa ta waya, Umma ce ta kirasa tace in bai tafi ba ya dawo tana son ganinsa.
Da sauri ya koma bangarenta ta na zaune inda ya barta.
Shima sai ya koma ya zauna inda ya taahi Lokaci d'aya yana fad'in"Umma lafiya kuwa?
Kai Tsaye Umma tace"Daman saboda na yi maka mgana ne, kana ganin bai kamata matarka ta can zariya ta dawo nan da zama ba? Gani na yi kai ma ya kamata ka Huta zirga zirgan zai yi maka yawa kaje can kazo nan."
Sadiq ya yi shuru kafin yace"Zata dawo Umma, ammh ba yanzu ba."
Cikin mamakinsa Umma tace"Bangane ba? To meyasa?
Kai Tsaye yace"Saboda ta na karatu, ammh ta kusa gamawa, nima ina Tunanin in tagama ta dawo nan da zama ko can inda na ke aiki."
Umma da sauri tace"A'a ba can ba, nan din dai, in can ka ke so sai dai ka tafi da sultana."
Kallon Umma ya yi, sai dai bai yi mgana ba kad'a kai kawai ya yi kafin yace"to Umma shikenan."
Ita kuma tace hakane saboda bata son su Asim din su yi nesa da ita.
In suka koma Abuja ai sai ta Dade bata gansu ba, kuma yanzu yadda take kaunar yaran nan bata jin ko iyayensu suna da iko a kansu yadda take jin tana da shi.

Daganan Shima gida ya koma sai dai yana ta auna mganar Umma, ya Fahimceta Saboda su Asim ne, shima kuma yana Tunanin haka Siya ta fara zama Gusau in ya samu Ma'aikatansu sun saka hannu a takardan ba su Loan gida da Mota shi sai ya karb'i na gida duk wata za'a rika cirewa a albashinsa.
Gwara dai ya fara natsuwa waje daya shi kanshi ya gaji da duk bayan sati yana Hanyar Zariya ko hanyar Gusau.
Ya kamata ya natsu waje daya ko shima ya samu cikakiyar natsuwar da ya ke fata.
Har daki ya bi Sultana ya yi mata sallama ta na kwance, ko dago kai batayi ba ta amsa masa kamar bata son ta yi mgana.
Shi kuma bai damu kansa ba ya ijiye mata kud'i saman Side drower d'in gadon da ta ke kwance ya ficewarsa lokaci daya yana girgiza kansa, shi a tarihin zamansa da Siya ba tab'a masa irin wannan ba, shi fa a zamantewarsa da Siya sai dai shi ya ji kunya in ya yi mata laifi ammh ita bata taba yi masa laifin da yaji ta bata masa rai ba.
Sai dai abunda ba'a rasa ba, na zamantakewar yau da gobe.
Share Tunaninta ya yi saboda Tuki zai yi kada taje Tunanin ya yi masa ya kara samun matsala.
Kafin ya tashi sai da ya kira Siya ya gayamata zai kama hanyar Abuja cikin yanayin mganarta tace"Assadiq yau da rana kuma zaka tafi?
Kai Tsaye yace"Zan shiga Office da wuri ne Siyata."
Bata damu sai ta kara jin wani Dalili ba, ta shiga yi masa addu'an fatan isa lafiya har ta na kara masa gwarancin su Asim.
Kafin su yi sallama haka ya Dauki hanya cikin Farinciki tuni ya shafe Tunanin Sultana ballatana Sakarcinta.
Sai bayan mangriba ya isa Abuja Abba ya yi ta kiransa yana hanya sai da bayan ya natsa ya yi sallah yaci abinci sannan ya kira shi suka yi mgana.
Bayan nan ya kira Siya ya gayamata ya isa, itama ta na ta kiranshi yace bai Sauka ba.
Umma kuma daman tana tare da Abba domin yaji muryanta Lokacin da suke waya.
Sultana ma ya kirata Saboda ya fita hakkinta kira Biyu sai ana uku ta Dauka tana wani cin mgana shi dai bai Tsaya nuna ya gane fushi ta ke yi ba yace mata ya isa lafiya.
Kawai Ok tace ta kashe wayarta sai ya yi Sororo a fili ya Furta"Yarinyar nan ta yi nisa."
Danne bacin ransa kawai ya yi saboda hakane ma sai kawai ya Kira Tahir ai sai yaji Tahir na amfani da wayar. sabodq yakuresa yasa ya yi ta kara kiransa wajen sau biyar duk bai gama wayar ba, wajen awa daya sannan sai gashi ya Biyo kiran Sadiq din yana Dauka yace"Wai lafiya ka ke ta min kira ba daga kafa?
Sadiq yace"Allah ya baka Hakuri ai bansan ka fara Serious Soyayya ba ne."
Sai Tahir ya yi shuru bai yi mgana ba, Sadiq ya sha Mur kafin yace"Ina taya ka Murna, sannan barka iyayen yara za su huta da tsabar yaudaran musu ya'ya da ka dinga yi a baya."
Tahir ya yi dariya kafin yace"To nagode, kasan komai Time ne nima ina ji a jikina Lokacin da zan yi aure ya kusa in sha Allahu."
Sadiq na dariya yace"Eh lalle to Ameen."
Daganan suka cigaba da Tattaunawa kan lamarin na wani Lokaci kafin su yi sallama.
A ran Sadiq yana jinjinama wannan yarinyar da ta iya sace zuciyar Tahir farat daya haka akanta ne kawai yaji Tahir ya nuna cewa lokacin da zai yi aure ya kusa.
Tunda ya koma kullum da Safe in ya Kira Siya itama Sultana zai kirata yaji Lafiyanta.
Ko da bazata amsa dakyau ba, shi dai daman Saboda ya Fita hakkinta ne.
Ranar alhamis da ya kirata da daddare bayan sun gaisa ya ke kara mata Tunin inda Siya zata sauka.
Kai Tsaye Sultana tace"Ni fa na gayamaka bani da masaukinta a gidana, kuma duka kayan da ke cikin gida nawa ne naga ba Dakin da bakomai a ciki ballatana kace na Sauketa aciki."
Mamakinta ya kara kamashi Saboda Haushi sai kawai yace mata"Sulatana ki yi duk abunda ki ke so, lokacin ki ne."
Daga haka ya katse wayarsa, Sai ya kira Big sis ya so ya fad'a mata abunda ya Faru tsakaninsa da Sultana ne sai kuma ya fasa a ransa yace ai shi Namiji ne shi zai Dauki matakin da ya Dace.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.