Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 18 of 86

Jin maganar Mutuwa da kuma yanayin Rudewarsu yasa Da Sauri Saddiqa tace"Ba fa maganar Mutuwa ba ce ko wani abu, Lafiyan Sadiq kalau babu abunda ya same shi."
A tare Umma da Abba suka Sauke Numfashi  mama ko sai da tayi hamdala.
Innani ne ta tsaya da kukanta ta na kallon su Surayya ta cikin gilashinta na wani lokaci kafin a fusace tace"To karya ku ke yi, in ba wani abu ya sameshi ba uban me yasa baku fad'i abunda ya faru ba tun dazu? Kun tsaya kuna ta raina mana wayau.'
Ta karishe fad'a cikin masifa, Abba dai jikinsa gabadaya ya yi sanyin da ya kasa mgana.
Umma kuma zuciyarta ne taji ya na gudu sosai kamar dai wacce wani abu ya sameta.
Cikin karfin hali tace"Zaku fad'a mana ne, ko kuwa sai mun mutu da zullumi.?
Da Sauri Saddiqa tace"Sadiq ne ya yi aure Umma."
Gabadaya sai falon ya yi shuru kowa na auna mganar Saddiqa.
Innani ce ta yi tsaki kafin tace"Ji wani shashanci daman ai kowa yasan magajin gida ya yi aure, daman dalilin dayasa ku ka taramu anan kenan? Kai sulaimanu yi tafiyarka sabgoginka yara nan wasa za su yi da Tunanimmu."

Surayya ta sauke ajiyar zuciya kafin tace"Innani ba wannan auren ba, kafin.. kafin ya auri Sultana to daman ya auri wata achan zariya."
Sai falon ya kara Daukan Shuru Surayya kawai a ke kallo.
Umma ta sandare a zaune, Innani kuma har gilashinta ta cire ta kara maidawa ta kara gyara kunnuwanta kafin ta kalli Abba ta na fad'in"Sulaimanu ko dai kunnuwana sun samu matsala ne?
Me nake ji Ana fad'a na wai?
Abba ya yi shuru bai ce komai ba, Mama ce ta kalli su Surayya cikin rawan baki tace"Ku yi mana karin bayani, bangane ba wani irin aure kuma?
Surayya kanta na kasa tace"Aure ya yi a garin Zariya tun Lokacin ya na bautar kasa, shekaru uku da suka wuce."
Mama ta Bud'e baki cikim mamaki kafin tace"Da gaske ku ke yi? Wani irin aure kuma ni Saratu?

Saddiqa ta gyara zama ta fara ba su labarin yadda akayi suka ga hoton Sadiq da Hasiya da yadda suka Bincika suka gano gaskiya da zuwan Surayya zariya ita da Sajida. Da kuma karin tabbaci daga bakin Hasiya tare da Shaidar ma cikin jikinta.
Mama ta koma ta yi zaman dirshan a inda ta ke  maimaitawa ikon Allah kawai ta ke yi.
Umma kuma kanta na kasa bata Dago ba, ammh a cikin kasan ranta mamaki ne da al'ajabi Abba kuma ba wanda zai iya cewa ga yanayin da ya shiga.

Innani kuma shuru tayi kamar bata ma afalon Inaga tsabar Mamaki ne ya hanata mgana wannan karon.
Abba ne ya yi gyaran murya kafin yace"Shi Sadiq din baisan kun san labarin ya yi Auran ba?
Surayya tace"Eh Abba, ya yi kokarin ya fad'amin ammh kuma ya kasa, daman tunda abun har ya fallasa naga ya kamata ku fara sani."
Abba ya jinjina kai kafin yace"Ita matar tace Tahir ya san da mganar auran?
Surayya tace"Tabbas haka ta ce ya sani"
Kafin Abba ya yi wata magana Umma ta d'ago ta na kallon Surayya cikin wani yanayi kafin tace"Shi Sadiq din da kansa ya yi aure batare da sanin mu ba?
Tsakanin Surayya da Saddiqa sai aka rasa me bama Umma amsa.
Mama ce ta rike hab'a kafin tace"Ni kaina ina ta mamaki, Sadiq fa? Me yasa Sadiq da hankalinsa da Tunaninsa da iliminsa sai ya aikata haka? Aure fa kuka ce? Kuma kun ce an dade ma tunda su Surayya sun je sun ganta har da ciki"

Kafin kowa ya samu zarafin mgana sai sai ihu da kurruwan innani suka ji, har ta na wani tuma da kafafunta kamar karamar yarinya.
Cikin kuka ta ke fad'in"Wai daman da gaske kuke yi Magajin gida ya auri wata matar kafin sulsana? Yanzu Amana ta zai ci ya yi ma Jikata kishiya? Magajin gida ina ganinsa mai Hankali ashe maci amana ne, mara Mutumci to billahillazi bai isa ba, ya yi kad'an jikata ta zauna da kishiya ni da Magajin gida baram baram ko ya saki wacce ya aura ya zauna da jikata ita kada'i ko kuma ya sakar min jikata, sannan ya yi ta kansa nima na yi ta kaina.".
Sai kuma ta kara fasa kuka, har da majina ta na kara fadin"Tsakaninmu da wannan yaron sai Allah ya isa."
Lalle lamarin ya lalace tunda innani ke auna ma Sadiq Allah ya isa.
Umma ta yi kokarin danne abunda ke ranta kai tsaye ta kalli Surayya kafin tace"meyasa tunda bai so mu sani ba ku ke sanar damu yanzu? Na dauka Tunda ya yi auransa a boye baya so mu sani ne, sai mu bar shi a haka tunda shi a wajensa haka ya zab'a."
Surayya tace"Umma saboda matar ne, itama ya yi musu karyan ba shi da kowa  iyayensa duk sun rasu."
Mama tace"Shi Sadiq din?
Saddiqa tace"Shi fa, ai Sadiq ya bani mamaki ban taba Tunanin haka daga bangarensa ba."
Mama tace"Ni kaina, ina ta mamakin wannan lamarin, abu kamar almara."
Umma ta had'iye abunda ke ranta kafin tace"Ni banzan ce komai ba, ramar da yaso mu sani zai zo ya fad'a mana da bakinsa"
Daga haka ta mike zata fita, Da Sauri Surayya tace"Umma kunsan matar fa."
Da sauri Umma ta Juyo cikin mamaki kafin tace"Mun santa?
Ta fad'a ta na kallon Mama, itama ta na kallonta.
Cikin karin mamaki Mama tace"To wacece?
Kafin Surayya ta yi mgana Saddiqa tace"Ina kawar saliha da tazo mata Biki daga zariya? Wace tace sun hadu da bikin salima a kaduna yar'uwan mijin salima wata Fara haka.".

Umma da Mama suka yi shuru suna Tunani, nan da nan suka ganeta Tunda ai sun ganta.
Saliha har falon Umma ta kaita suka gaisa, mama kuma a shashenta ta kwana ta gane, kuma kammninta ba shi da bacewa a fuska.
ita Umma ma har a kaduna ta tuna ganin da ta yi mata Lokacin da ta fito neman Innani.
Cikin mamaki Umma ta kalli Surayya kafin tace"Kuma kikace itama ya yi mata karyan ba shi da kowa? A ina ta san nan gidan?
Surayya ta kalli Umma kafin tace"Umma koma ki zauna na yi miki wani karin bayani."

Ba musu ta koma ta zauna, Innani ma ta daina kuka ta na saurara Abba dai ko a fuska bai nuna wani abu ba.
Surayya ta warware ma Umma komai game da zuwanta Zariya..abu daya ta Boye na canfin da ke bibiyar Rayuwar Hasiya.
Sai kuma na auranta Biyu, ta dai ce bazawara ce, Sadiq ya kama mata haya tana zaune a zariya ya na zuwa ya ganta in ya samu Lokaci.
Sannan ta karishe da fadin"Umma ba wai ina so na kare Sadiq ba ne, A'a ina so ku fahimci namu ne mai laifi, itama ya yi mata karya ne ita da yan'uwanta, sannan dalilinsa na auranta wannan sai shi in yazo ya yi bayani, sannan mganar tasan nan gidan tamin Rantsuwa bata sani ba sai daga baya had'uwarta da Saliha a kaduna da kuma Hoton mu da tagani, tace sai da tazo nan ne taga komai, a yadda ta fad'amin ta na ma sadiq mganar ya kamata ya sanar da mu komai ammh sai yace ta bashi Lokaci yana so ya sanar daku ya na da wata matar kafin Sultana."
Mama ta bude baki kafin tace"Bazawara? Shi Sadiq kamar wanda bakin uwa ke binsa?

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.