Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 19 of 86

Innani ta ja hanci kafin tace"Magajin gida yaci Amana, kuma Amana sai taci sa ja'irin mayaudari kawai yazo ya sakarmin jikata domin bazata zauna da tsohuwar kilaki ba."
Surayya da Sauri tace"Innani ba kilali ba ce fa."
Innani na Hararanta tace"To wacece kuma ta yi aure ta fito ai ta zama kilali yar duniya, ina jikata zata iya zaman kishi da ita? Arhin dinsa sai ya saketa kuma naga abunda da zai hanani ci ma Saddiqu mutumci shi da wannan Dogon abokin nasa mai wuya kamar kauren langa Langa."
Da Sauri Umma tace"Ba ruwan Tahir Innani, Abubakar ne bai Daukemu a bakin komai ba, nima ina goyon bayanki, yadda yaci Amanarmu shima sai Allah ya sa anci tasa, yata bazata zauna da shi ba, tunda wanchan ya zaba sai ya cigaba da zama da ita, Sadiq sai ya saki sultana tun kafin Mahaifinta yaji irin cin zarafin da ya yi ma yarinyar nan "

Kawai sai ta fashe da kuka ta mike ta na fadin"Na yarda dashi, ban taba Tunanin zai karya wannan yardan ba,  Wlh tallahi sai dai ya zaba, ammh har acikin raina ban aminta da wannan auren ba."
Ta na gama fad'in haka ta fice Abba na kiranta bata dawo ba, Innani ma ta tashi ta na dingisa sandarta ta shige dakinta itama ta na shan alwashin idonta idon magajin gida sai taci kwalarsa ya sakar mata jika bazata zauna da bazawarar kilakin matarsa ba.
Abba ne kawai da Mama afalon, shi ta kallah kafin tace"Abban Siyama baka ce komai ba?
Sai Abba ya dago kansa yana kallon Surayya kafin yace"Ki aika a dauko yarinyar nan shima Sadiq din ki gaya maasa yazo gida."
Da haka shima ya tashi ya fice, bai bi bayan Innani ba sanim halinta tunda ta Dauki zafi bazata Sauraresa ba.
Mama kuma sai ta gyara zama ta na kallonsu Surayya kafin tace"Ammh tsakami ga Allah Sadiq bai yi wayau ba, bazawara fa? Kodai farin fatarta ne yaja Ra'ayinsa?
Daga Saddiqa har Surayya ba wacce ta kulata ta gama mganganunta itama ta tashi ta fita.
Suma daga nab Shashen Umma suka koma ta shige dakinta ta Rufe, alamun bata son a dameta.
Sai suka zauna anan falon suka yi shuru kowa da abunda ya ke sakawa.
Saddiqa ta kalli surayya kafin tace"Sai ki kirasa ki fad'a masa ko?
Surayya tace"Zan kira sa, ita Hasiya ina tunanin kawai zan ce ta hau motar haya in tazo tasha sai naje na Daukota."
Saddiqa tace"Duk yadda dai ki ka yi, ni nafi son Sadiaq ya ci Ubansa hannun Umma da Abba saboda gaba"
Surayya dai ba ta ce komai ba, ta na wani Tunani Abba bai nuna wani abu ba, Umma ce ta Dauki zafi ita da Innani kuma a irin kalamansu ba su karbi Hasiya ba.
Kwata kwata su Surayya ba su dauka Mama zata gayama ya'yanta abunda ke faruwa ba, ashe ba haka ba ne ta na komawa daki ta fara kiransu a waya  daya bayan daya Sa'ima ta fara kira ta gayamata sannan Saliha da sauran.
Kuma kowa sai ta yi masa kwatancen Hasiya sannan ta kara da fad'in ance ma bazawra ce, kuma Surayya da Sajida sun je har zariyan sun ganta.
Dukkansu mamaki ya kamasu, Mama ko har da kalaman Umma da Innani sai da ta gayamusu sannan tace su zo gida ayi gabansu Tunda Abba yace a zo da yarinya sannan Sadiq ma yazo gida.
Saliha tafi jin mamaki ta jima tana nanata abun, sai alokacin ta Tuna kiran da Surayya ta yi mata, ashe daman dalilin kenan?
Salima ma Sa'ima ta ke gayamata, da kwatancen yar'uwansu mubarak yasa ta gane wacce Anty surayya ta Turo mata Hoton ta ne, ita ta manta da batun ammh jin haka yasa taji ta na son sanin komai.
Ballatana da Mama ta kirata ta na fad'amata tace an ce yar'uwan mijinta ne, sai ta fad'a mata yadda suka yi da Big sis kwanaki.
Nan ta ke Mama tace salima ta yi musu Binciken wacece Hasiya!
Salima kuma na jin haka a daran ta matsa ma Mubarak sai da suka je gidansu, ta samu zahara'u ta tuna mata, itakuma sai da aka had'u wajen cin abinci ta ke yi ma Abba kwatancen Hasiya.
Hajiya Murjanatu na wajen itace ma tace yar wajen marigayi dan'uwansa mamman ne.

Sai ya tuna, kamar ko yasan Salima na son labarin duka nan ta ke ya fara ba su labarin Hasiya da canfinta na mai farar kafa da tunanin da suke yi ita tayi sanadiyar talauta mahaifinta daga karshe ya rasu da aure aurenta da komai sai da ya fad'a ma yaran kuma agaban Salima.
Hajiya murjanatu na ta kifta masa ido ammh ya yi kamar bai gani ba.
Da ya gama yaga ta na yi masa wani kallo sai kawai ya karkace kai kafin yace"To ko karya na fada? Gaskiya dayace fa daga kinta sai bata Murjanatu"

Salima kuwa suma komawa gida ta kira Mama ta kwashe komai ta fad'a mata, ita kuma duk a daram ta kira yaranta ta fesa musu, suna ta faman Tattauna lamarin yan kusa sun ce gobe suna nan zuwa ayi komai a gabansu.
Ita kuma Hasiya Surayya ta kirata tace in da kudi a hannunta ta shirya ta hayo motar haya in zata iya.
Tace mata zata iya.
A ranar na baro zariya na zo gusai, gwara kawai nazo ayi wacce za'ayi, a tasha Surayya ta zo ta Daukeni zuwa gidanta ta bani daki kuma ta karraamani.
Ta kuma zaunar dani tamin bayanin komai da ya faru yau da safe, ammh bata fad'amin furucin Umma da Innani ba.
Tadai ce Abba yace na zo sannan Sadiq ma a kirashi.
Ta bar ni a dakin da ta saukeni ta fita falo da niyar kiran sadiq.
Sai taga ya kirata ma wajen sau Hudu. Ta na kokarin bin bayan kiran ne sai ga shi ya sake kira.
Sai da ta dauka suka gaisa, ta yi shuru shi kuma dagachan bangaran yace"Big sis mganar nan da na yi ta cewa ina so mu yi, shine yanzu na ke so in ba wani abu kike yi ba mu yi mganar"
Kawai sai tace"ka makara Sadiq na riga nasan  mganar"
Cikin firgici yace"Kin sani?
Mirmishi ta yi kafin tace"Ba na kayi aure a zariya ba? Sunan matar taka Hasiya kuma ma yanzu ta na da ciki ko?
Ai sai Sadiq yaji kamar a cikin kankara ya sandare a zaune.
Yana kwaso in'inan mgana Surayya ta katseshi da fad'in"Umma da Abba da Mama hadda Innani suma sun sani, Sadiq gobe kome ka ke yi ka barshi ka taho gida, in kuma ka ki zuwa ina mai tabbatar maka komai zai lalace."
Cikin rawan baki da na zuciya Sadiq yace"In sha Allahu zan taho da Sassafe.'
Daga haka ta katse wayarta, ta na Tunanin abunda zai iya faruwa a goben.

Abunda bata sani ba suna gama waya ya kira Hasiya, ta dauka kuma Daman Surraya tace kada na bari yasan ina Gusai.
Cikin tashin hankali ya ke gayamin yadda suka yi da surayya sai naji ya bani Tausayi, barin ma da ya ke cewa"Gobe zan tafi gusai siya, ki tayani da addu'a Umma da Abba su Fahimceni, ina son ki har abada ba na fatan Rabuwa da ke. Ki zama cikin shiri akwai yuyuwar ki taho gusai in bukatar hakan ya taso."
Ya yi ta kokarin ya nuna min kada na Damu in sha Allahu bakomai.
Shi tunaninsa daya ina suka san da wannan labarin? Duk da na sani ammh na kasa iya gayamasa yadda abun ya fara ba.
Muna waya ina sharan kwalla, na yi ma kaina alkwarin zan yi duk abunda Assadiq ya ke so, tunda wannan Halin Tsaka mai wuyar da ya ke ciki ba saboda kowa ya shiga ba sai saboda ni.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.