Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 74 of 86

Suna tafe a mota ya tuna bai kira Siya ba, kuma bai kyautu sai dai taga baki kawai ba sanarwa ba.
Nan take ya rage gudun motarsa ya Dauki wayarsa ya kirani.
Lokacin ni kuma ina zaune a falo Tibi na aikinta da Mbc3 Cartoon saboda su Asim.
Waya ce a hannuna tunda yanzu saboda zaman kad'aici yasa na waye da sanin Kafafen sada zumunta.
Ina yin Faceebook har da Instagram, ina cikin Groups sosai na karuwa na ganin abunda ke faruwa a duniya.
Ina cikin Sirrin y'a mace a Facebook, sannan Ina cikin Arewa open diary, sannan a Intagram ina cikin Northenhabiscuss.
Ina ganin abubuwa sosai kuma ina karuwa na sha kuma cin karo da ma su irin abunda ya danganci Rayuwata.
Daganan na Fahimci yanzu mutane sun maida Canfi dabi'an su.
Sun kuma sakashi cikin Addini mun saki Allah mun kama mganganun jahilai da malaman tsubbu marasa tsoron Allah.
Ina Tsaka da dube duben Labarai na ban aljabi da Tausayi da mamaki da yanzu na kware wajen bibiya kiran Assadiq ya shigo.
Asim da Asif suna daga can gaba a kasan Cafet suna kallo rabi da rabi kuma suna wasa da Motarsu na roba irin na yara mai tafiya d'in nan.
Da zumud'i na Daga kiran nasa ina mai Fad'in"Mijin Siya."
Shima cikin Farinciki ya amsa min da cewa"Matar Assadiq."
Wanda fad'in haka da ya yi sai da Sultana ta kallesa wani kishi mai zafi ya Turniketa.
Wato matar Assadiq ita da kai Tsaye ya ke kiran sunanta ba Tausasawa a cikin kiran nasa  ammh kalli yadda ya ke mgana da Matarsa cikin girmamawa kamar ta na gabansa
Ya sha harara shi ko bai ko kalleta ba Rabin hankalinsa na wajen Siya rabi kuma na wajen Tuki.
Cikin yanayin maganarsa yace"Ya gida?
Da sauri yace''Gida lafiya lau, sai dai kewarka da mutanen gidan suka yi."
Cikin yar Dariya yace"Nima na yi kewarku, ina su Asim?
Na kallesu kafin nace"Ga su can suna kallo rabi kuma suna wasa kasan su.'
Jinjina kai ya yi kafin yace"ke kuma fa?
Ina dariya nace"Kasan ai abunda na ke yi ko?
Shima dariyan ya maidamin kafin yace"Nasani kina nan kan waya kina Shige shigen da yanzu kika saba da shi."
Mirmishi na yi ina kara fad'in"Kamar ka sani, ina can ina karanta wani Labari kamar irin nawa labarin, Mijin Siya na fara wani tunani fa"
Da sauri yace"Tunanin mene?
Ni kuma kamar nasan sultana na gefensa sai nace"sai dai ka dawo sai mu Tattauna mganar na Bukatar natsuwa gaskiya."
Gyaran muryan Sultana yaji da yasa ya tuna da ta na kusa da shi.

Shifa in ya na mgana da Siya ko yana kusa da ita ya kan manta da kowa da komai ne baya ganin kowa sai ita.
Shiyasa ya yi saurin cewa"Ga ni nan zuwa gidan ma yanzu da baki, ki gyara dakin nan da ke kusa da namu don Allah."
Cikin mamaki nace"Daga Gusau ne?
Kai tsaye yace"Eh! Kin dafa abinci?
Cikin zumud'i a zato ko cikin yan'uwansa ne yasa nace"yar sauran miyan jiya da ta rage dazu na Dafa Farar shinkafa naci, su Asim ma goldenmorn na had'a musu suka sha, bakin da yawa ne?
Cikin sauri yace"A'a mutun biyu haka."
Cikin Girmamawa nace"zai ishe su anjuma sai a kara dafa musu wani abun ko?
Shima sai yace min eh, Kamar yana ganina haka na mike ina fad'in"Dakin ma bashi da wani gyara sai dai saboda kura bari naje na share na goge.'
Ya amsa da"Allah ya yi miki albarka Siya, sai mun iso."
Daga haka muka yanke kiran, Ta bangarena ban taba kawo ma raina Sultana ce ta zo ba.
Tunda yace min suna hanya na Ijiye wayata na shiga dakin na fara gyarawa Gado ne kawai sai Wardrope sai cafet akwai Tiolet acikin dakinn.
Ba mu tab'a kwana aciki ba sai dai muna saukar da baki in suka zo mana.
Jiki na rawa na gama sharewa na saka Moper na goge ko'ina har Tiolet sai da na wanke na saka turaran Wuta a Burner mai kamshi.

Sannan na fito na iske su Asim sun min barin madara a falo tunda nan saman Tv sand na dora shi.
Sai na Musu fad'a na ce su hau kujera su natsu ina cikin goge cafet din ne naji Dirin motar Assadiq.
Su Asim sun yi wayau sanin Karan Motar Babansu da gudu suka fita na bisu da kallo shiyasa nace a karshen wannan watan zan kai ma Umms su, tunda na yayesu a Boye batare da Assadiq ya sani ba
Suna da wattanin sha tara kenan shekara Biyu, Assadiq ne ya hana in yaye su tun suna da wattani sha bakwai
Na gama gogewa kenan ina fesa Turaren ruwa na Cafet naji Sallamar Assadiq.
Na juya cikin Fara'a ina amsa sallamar nasa, sai dai bakina ya yi nauyi sanda na ga Sultana a bayansa sai wani mele baki ta ke yi Su Asim kuma Assadiq ya had'asu ya Dauke su, Yarinyar da ke bayanta ne dauke da Jaririyar nata.
Nan da nan na shanye mamakina, na Saki Fara'a ina yi musu maraba.
Na maida abun hannuna bayan Tv da ke falon na isa garesu ina yi musu maraba da zuwa.
Na wuce sultana na karisa gaban Naja na karb'i Ummi daga Hannunta.
Kuma na kalli Sultana ina yi mata maraba cikin Fara'ata nace"Sultana sannu da zuwa, maraba ku zauna mana."
Assadiq daman shi ya samu wajen zama yana bidiri da ya'yansa, Sultana tak bata ce min ba kallo ma ban isheta ba, kamar bata so haka taje ta zauna a kujeren da mijinta ya zauna lokaci d'aya ta na kare ma falon nawa kallo.
Tana wani tabe taben fuska kamar Taga kashi.
Ni na karbi akwatin da Naja ta jawo ina rike da Ummi na shigar musu da shi Cikin dakin da Assadiq yace na gyara.
Ina fitowa na isa gaban Sultana na mika mata Ummi da ta fara rigima ina Fad"in"Ki bata nono, Asim ba ku ga kanwarku bace?
Na fad'a ina nuna musu ita, Assadiq yace"Ku je ku ga kanwar ku mazajen Abbu"
Ya fad'a ya na nuna musu Ummi da ke hannun uwarta da ta had'e rai kamar taga wani abun ki.
Ni kuma kitchen na shiga Dauko musu Ruwa na had'o musu Lemun Maltina da Fanta sai Ruwan Faro mai sanyi na sako a wani babban Faranti na kawo musu nan Tsakiyar falon.
Naja center Table na tura gabansu a kai na sauke musu.

Kuma na durkusa ina zuba musu tunda na had'a da kofunan glass.
Naja na fara mikamawa sannan na mikama Assadiq ya karba yana min mirmishi ita kuma Sultana ganin ta ba ma yarta Nono sai na kyaleta da Niyar in ta gama sai ta zuba ta sha.
Na koma gefe na zauna ina kallonta ta na Ture hannun Asim da ke wasa da Hannun Ummi.
Asif kuma uban karambanin ya na neman haye jikin Sultana ya danne Ummi.
Ina shirin mgana naga ta Tureshi cikin Tsawa tace"Kai baka da Hankali ne?
Ban tashi ba ganin Assadiq ya kalleta cikin mamaki Asif jin an daka mai tsawa yasa ya tsorata shima Asim haka.
Kafin kace me sun fashe da kuka ba su nufi wajen Assadiq ba sai suka nufo ni suna kuka.
Na kama su na rike ina llallashin su ina fadin"baku san kanwarku ba ko? Ku yi mata wasa a hankali kun ji ko?
Suna ta kallo na tunda suna jin mgana, suma ai suna mgana sai dai bata nuna ba ne, ammh sun iya kira sunan Abbu da Mami su san Umma da Abba da Goggo Surayya.
Assadiq ne ke yi ma Sultana fad'a da cewa"Ina yaro kamar Asif yaga hankali sai ki yi masa a hankali Tunda yaro ne"
Baki ta tura bata yi mgana ba, ni kuma ganin su Asim sun yi shuru sai na kwaso musu kayan wasan su nace suje su yi wasa.
Lokaci d'aya ina kallon Assadiq kafin nace"Ko za su yi wanka ne kafin su ci abinci.?
Kai tsaye yace"Gata nan tana jin ki."
Ya fad'a lokaci daya yana mikewa agogon fatan da ke hanunsa ya kallah kafin yace"Zan koma Office akwai wani abun da kuke Bukata ne?
Girgizamasa kai na yi alamun babu.
Ita ya kallah yana jiran tace wani abu sai kawai ta kauda kai kafin tace"Ban ga dakin da zan sauka ba."
Kafin ya yi mgana na rigasa da sauri nace"Laa ga daki nan, har na kai kayan ku ciki ma."
Na fad'a ina nuna mata dakin da Hannuna ko kallona bata yi ba ta mike Dauke da ummi Lokaci d'aya ta na fadin"ta shi mu je Naja."
Muna tsaye ta wuce cikin dakin Naja na bin bayanta.
Shi dai kai kawai ya girgiza kafin ya wuce yana fad'in"Sai na dawo."
Na rakasa har kofar falo sannan na dawo cikin falo.
Na zauna na yi tagumi ina Tunanin yadda zaman mu zai kaya da sultana daga gani kuma ta zo ta jima ne, kuma Yadda ta ke nunawa har yanzu ba ta son zaman lafiya.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.