Tmw Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: TMW BOOK 3.txt
Chapter 76 of 86
Nima na rakasa da sai da Safe.
Ina ga shi yace ma Naja ta shigo mu kwanta sai gata ta shigo nace taje ta yi fitsari tazo mu kwanta.
Ni kan na dad'e ban yi barci ba akwai wani Tunani da ke yawo a raina Shi na ke ta nazari ba na so na fara yin wani abu batare da sanin Assadiq ba.
Mun yi chart da Surayya ta ke tambayata ya bakuwa na ce lafiya.
Bata gayamin komai ba sai dai ta kara tambayata ko Sajida ta kirani?
Nace mata bata kirani ba.
Daganan sai na kara Fahintar wani abu ya faru, wanda yasa sultana tazo kuma daman Umma tace an yi yar hatsaniya.
Da asuba Assadiq ya tasheni sallar asuba shi kuma ya tafi masallaci.
Saboda yana fita aiki in na yi sallah ba na komawa na ke fad'awa kitchen na sama masa abunda zai ci.
8am ya ke fita kafin lokacin kuma ya karya ya shirya, har kuma ya bar gidan Sultana bata fito ba abun karyawanta ma Naja na ce ta bita da shi Tunda ta zama Hakima.
Ni bazan yi mata abunda tayi min ba, Ummi ma na goye bayan Naja tun safe, ko wanka ba'a yi mata ba ni na karbeta na yi mata tare da Asim.
Ai ko da naja ta kaita a saka mata kaya ina falo ina jin Ta na yi mata fad'an Uban wa yace ta ba ni yarta?
Salon aje a goga mata wani bala'in ko kashin tsiya.
Da karfi ta rika yi saboda naji, ni kuma sai na yi kamar ban ji ba ta kuma tayi ma Naja kashedin kada ta kara bani yarta in ta kara sai ta yi mata Duka tsiyan
A raina nace abun bai kai nan ba, rike yarki ai nima na Haifa.
Assadiq ya kirani yaji ko ba ma Bukatar wani abu? Nace ba ma abukatar komai.
Ni kadai na ke Budirina acikin gidana sai Naja da yau ta hanata ma zaman Falo tare da su Asim.
Komai na Dafa daki nake aikama Sultana taci kuma ta bar shi aciki sai zan yi wanke wanke na ke saka Naja ta shiga ta Daukomin.
Haka na ke tafiyar da ita, tun kuma ina saka ran yau zai ce min zata tafi har naga ta kwarari sati ta na Hutu ina yi mata Bauta.
Sannan ni da tazo gidana ne nice in ta fito na ke gaisheta ta amsa kamar ba ta so wani Lokacin sai in a gabansa ne ta ke amsani.
Ranar da ta cika sati muna cin abinci da Daddare kai Tsaye ya kalleta yace"Yau dakin Siya zan kwana, ki tafi da Naja dakin ki."
Dagowa na yi ina kallonsa sai naga ya had'e rai, kuma daman na lura tunda sultana tazo ba wani jutuwa tsakaninta da Assadiq.
Shekaranjiya ina jin tashin muryansa kamar ya na mata fad'a ne.
Kafin na yi mgana ita ta rigani da cewa'"Banga ne ba?
Kai tsaye yace"Da hausa na yi mgaana ko baki jin Hausa ne?
Baki ta tura kafin tace"Tabdijam wlh ba'a isa ba, ni da na zo kwanan nan ita ai anan take koda yaushe tare dakai in adalci zakayi min a dakina zaka zauna har sai na gama zama na tafi."
Shima kai Tsayen yace"Shine na yi miki na fitan hakkin bakunta, sai ku raba kwana Bibbiyu, tunda naga kin wuce bakuwa yanzu kin zama yar gida."
Ta kallesa ranta na suya ta gane take takensa so ya ke ta koma gusau kuma wlh ita taga waje bazata koma ba.
Kuma ta fad'a masa kada ma ya Dauka wasa ne.
Shi kuma ransa ne ke bace yarinyar nan ta mugun rainasa ya na mgana tana maida masa martani.
Ya ji kunya da yaji wai Dambe ta yi da Sajida Surayya ta gayamssa Tun ranar da Sultanan ta zo.
Kuma ya Tsareta ya tambayeta ta na kuka tace Sajida ce ta fara zagin Ubanta.
Ya yi ma sultana fad'an baya son reni kada ta kara gigin fad'a da yan'uwansa in bata ci darajan suna yayyensa ai su ci Daraja suna yayyenta ita.
Kuma ya yi hakame saboda kada ta kara kwatatanwa a gaba ammh a ransa yaji dadin haka.
Yanzu sai Sajida ta kara gane bata da wayau, Tunda abokiyar shawaran nata yanzu itace abokiyar Fad'anta.
Yace in ta yi sati ta koma Gusau ta saka masa kuka abunda yasa ya kyaleta ya bari sati na sama in zai tafi ko taki ko taso sai ya tafi da ita baxata zauna a gidansa ta hanashi zaman lafiyan da ya samu ba.
Ni kuma gudun Fitinar Sultana yasa nace na bar mata kwanan nawa gabadaya har ta tafi.
Shi kuma sai yaji Haushi ya fara min Fad'an meyasa na fara abunda ba Halina ba?
Gaddama zan fara yi masa?
Ina jin haka sai na yi shuru na koma ina bashi Hskuri.
A fusace yace"Nan gidana ne, ku kuma dukkan ku mata na ne, kuma hukuncin da na yanke da shi za'a yi amfani na gama mgana."
Sultana ko na jin haka ta mike ta rike Kugu ta girgiza jiki kafin tace"Tab wlh baku isa ba, in a can kun saba Tauyemin hakki anan ko ba wanda ya isa."
Dagani har shi ita muke kallo, sai naga kuma hankalin Naja ya koma kanta sai na yi saurin cewa ta tafi da su Asim dakina su cigaba da wasan su acan ta na goye da Ummi ta rike hannayen su Asm suka tafi dakina Tunda sun gama cin abinci.
Sai da suka shige sannan na kalli Sultana ta na wani cika ta na batsewa kafin nace"Ki yi hakuri, dakin ki zai rika kwana har ki tafi in sha Allahu."
Cikin Fusata Assadiq ya kira sunana"Hasiya.."
Na kallesa da Sauri ina fadin"Assadiq menene aciki? Ai ni muna tare dakai ko da yaushe ita kuma zuwa ta yi zata tafi nan da Lokaci kad'an"
Kamar sultana na jirana sai ta harzukomin ta na fadin"Malama yi min shuru ba na son munafunci, har kina wani cewa zan tafi to ba inda zani nan gidam mijina ne ina da iko da shi kamar yadda kema ki ke da iko da shi."
Ina jin haka sai na yi shuru, shine ya kalleta cikin bacin rai yana fadin"Na gaya miki zan sake fad'a miki kuma nan ba gidan ki ba ne, gidan Siya ne gidan ki na Gusau kin barosa."
Sultana tace"Wlh bazan yarda ba ai gidan ka ne ba nata ba,nima ina da Iko da abunda ka mallaka Ehe."
Cikin gatsali yace"ok tunda hakane kina son kwana da miji sai Siya ta baki girki shikenan'
Siya daga gobe ta fara yin girki, ta bar kara miki walaha kin ji na gaya miki."
Sultana ta Fashe da kukan kissa kafin tace"Wlh ni bazan yi girki ba, dame zan ji da Girki ko da Reno. Ni bazan iya ba"
Kai Tsaye yace"Fine sai ki tattara ki koma gidanki, ki bar mata nata gidan."
Cikin Dara kafa tace"Saboda me ka ke korana? Baka san na zo kusa da kai?
Assadiq yace" saboda ba alheri ya kawo ki ba, in da zaki zauna lafiya da matata kibi Umarnina ko shekara zaki yi bazan damu ba."
Sultana ta shiga mganganun cewa yace mata shed'an ita wani rashin Alheri ta kawo kaza kaza sai yi ta ke yi bai tanka ta ba.
Ni kuma na kwashe abunda muka bata na kai kitchen na koma daki na basu waje suna cashewa yana mgana ta na maida masa martani kamar bata san Darajansa ba.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.