Tmw Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: TMW BOOK 3.txt
Chapter 51 of 86
Ranar litini da Sadiq zai je ganin Likita dagacan ya Biya Zariya Tahir ya taho jiya da yammah zai Tukashi su tafi tare, Umma bar bakin mota ta bisu tana kara jaddada masa ya gaishe mata da Twins.
Kamar tace zataje sai kuma ta fasa kada a Fahimci yanayinta.
Ammh da yaran nan ta ke kwana acikin Ramta, ta na son su dawo kusa da ita ta riga ganinsu a koda yaushe.
Sai da suka fara Zuwa asibitin sannan daganan suka dawo ta Zariya.
Likita ya tabbatar da warkewa tare da Samun nasaran gyaran karaya, sannan yace masa zai iya cigaba da Tukinsa ba bu wata matsala.
Sai dai Fatan Allah ya tsare kuma Nasara ma sosai aka samu ganin ko Dingishi Sadiq ba ya yi kafarsa da Hannunsa sambal suka warke.
Sai dai tabbai in da ya samu Rauni ne mutum zai kallah ya Fahimci ya taba samun had'ari.
Ko da suka iso wajena kamar ba Jego na ke yi ba mun cakare ni da su Asim, muka tarbi Babansu cikin Fara'a da Farinciki Tahir kuma shi ta su Asim kawai ya ke yi
Har ya kalleni yana fadin"Kai girmansu ya bani mamaki fa."
Ina dariya ban ce komai ba Assadiq ke fada masa suna shan har da madaran yara kuma basa wasa da Nono.
Bayan sun gaisa da Inna talatu ta ba su waje ta koma dakin Maman suhailat ban da Innani da ta zauna ta rika musu Hira..
Karshenta dai nan muka barsu Tahir da yaran da ita muka Shiga ciki.
Muna shiga ya Rumgumeni ya kamkameni yana shakan kamshin Jikina, mun jima a rike da juna Sannan ya sakeni ya koma ya na kallon Fuskata cikin Fara'a yace"Jegon nan ya yi miki kyau My siya."
Mirmishi na yi kafin nace"Kai ne dalilin haka Abban Asim"
Dariya ya saka yana fadin"Ehye wato na tashi daga Assadiq na koma Abban asim?
Sai naji kunya na koma ina sunne kaina saman kirjinsa, shi kuma yana Biye min tare da Tsokana ta.
Saboda za su tafi shiyasa bamu yi mgana sosai ba, na dai yi masa mganar zan je makaranta da ke kusa damu wata private zan kai musu Tp letter dina kafin su yi hutu tunda an kusa Fara jarabawa.
Sannan mun yi mgana ko bayan na yi arba'in Habiba zata zauna dani har su Asim su fara wayau saboda ni kadai bazan iya ba, sai nace ya kira Adda Fati su yi mgana yace min zai kirata.
Mun shagala aciki mun manta da kowa da komai.
Assadiq ya Rud'e ya na ta kamani ni kuma ina kwace jikina Tunda jego na ke yi ga mikin aikin bai gama warkewa ba.
Sai da Tahir ya rika kiransa a waya sannan ya sakeni ya fito ni kuma sai da na sako uban Hijabi Saboda kunya.
Tahir dubu goma ya ba ni yace a siyama su Asim kayan wasa.
Shi kuma Assadiq yace zai Turamin Sako ta waya da haka muka yi sallama.
Cikin ikon Allah Innani tace zata bisu da na ce har kin gaji damu?
Sai tace"Ina fa, kawai dai naga kamar ban kyauta ba ne, sulaimanu ma na da Hakki a kaina. Kada ransa ya baci yaga nazo nan na tare, gwara dai na koma shima ya ganni hankalinsa ya kwanta kada kuma na yi rashin Adalci."
Ni kaina sai da na yi Dariya Assadiq ne kawai ya Murmusa.
Tahir kuma har yana rike ciki, Inna talatu ta yi cewa zata yi kewar Innani, sai ga Innani na kuka ta na fadin"Ni kaina ba'a son raina zan tafi ba, sulaimanu na ke tausayi."
Sai kuma ta koma kallonsu Asim ganinsu ya sa ta kara kecewa da kuka ta na fadin"Yaran nan abun Tausayi uwarsu kadai ke wahala da su, Ubansu bai san wahalan ya'ya ba."
Assadiq ya kalleta kafin yace"Sai ke kika san wahalan na su ko?
Innani ta ballamasa harara kafin tace"Kwarai nan yara nan ke tsala kukan dare haka muke hana idanuwan mu barci muna wahalan reno, ammh daga karshe baka Gode ba."
Karamin Tsaki kawai ya yi ya fice daga dakin ya bar Tahir na Dariya.
Innani ta kwabe baki kafin tace"Masifaffe duk ya zama wani mafad'aci yo ni ko ubansa Sulaimanu lallabani ya ke yi Ehe."
Naji dadin zamana da innani a wajena na bata atamfa da sabulan wanka da omo har da Turare ta yi ta min godiya ta a sakamin albarka.
tace kuma kada na damu zata dawo daman domin tana jin Tausayin sulaimanu in ba haka ba inda zataje nan zata zauna tare da yara nan ta na tayani renon su.
Har Habiba sai da tace gidan ba Dadi da Innani ta tafi, innani ai akwai hiran ban dariya.
Farida sai dai ta koma bangaran Umma, Shiyasa da Innani ta dawo ta yi ta Murna, innani tace shaf ta manta da Amana a hannunta to gaba kafarta kafar Farida bazata barta anan ba, ba mai Tausayin da zai kula da ita.
Ba wanda yace mata a'a sanin halinta kada ayi mgana ta tada kukanta na Fama sai aka bita da yadda take so.
********
Bayan wata d'aya."
Kwana uku da yin Arba'in din su Asim Safiya ta zo ta goyamin Asif ni kuma na goya Asim mukaje private school d'in da ke kusa damu na kai musu T.p letter a lokacin ma suna Wassanin yara ne sun gama Jarabawa hutu za su ba da.
Na gaya musu tsaikon da na samu aiki aka yi na haihu ganin yaran yasa suka karbeni suka bani accpted letter wanda zan kai makaranta suka ce bayan an dawo hutu sai na fara zuwa..
Jin dadina da Safiya tace ba'a fara zuwa Dubawa ba, makaranta ne na sha Fad'a a Tp office sai da suka ga su Asim sannan suka yarda da uzurina.
Tunda na yi arba'in Inna Talatu kwana daya kawai ta kara ta koma gida, na bata atamfofi guda Biyu Assadiq ma ya siya mata har da waya tunda a gidana na hannunta ta lalace sannan ya bata kudi, muka rabu tana min godiya mu ma muna yi mata.
Habiba ce ke wajena Tunda Assadiq ya yi mgana da Add Fati ta amince daganan na ke bata kudin mota ta na tafiya makaranta.
Assadiq ya koma Abuja wajen aikinsa sannan kuma Abba ya gwangwajesa da Sabuwar Mota Camry mai ruwan madara ta yi kyau motar tunda har nan yazo min da ita mun shiga ni da su Asim mun je yawo.
Yawon arba'in na fara nan cikin gari tunda yace min har wajen Amma zai kaini mu kai mata su Asim in ya dawo sannan zamu je gusau mu yi kwanaki Umma ta matsa yaushe zan kai mata su Asim?
Umma ce ta bani mamaki har waya muna yi da ita, in yau bata kirani ba gobe zata kirani ta ji ya ya lafiyar su Asim har wasanninsu ina kara mata tana ji.
Ni yanzu Hankalina duk ya kwanta, in da nake hangen matsala Cikin ikon Allah komai ya zo ya zama kamar bai Faru ba.
Naje gidan Adda Fati na kwana daya, Gidan Ramatu ma na kwana ita kwana muka yi mganar kayan gyaran jiki nace mata Adda Rukayya tace akwai wata marubuciyar littafan Hausa kayanta na da kyau da inganci.
Ramatu tace in na samu na gayamata itama zata siya ammh sai ta Haihu Tunda Tsohon ciki gareta.
Gidan Adda Rukkaya ne da naje ban kwana ba saboda mijinta na dai yini da ita kuma ta kiramin mai saida kayan gyaran Gudiyo kaya masu inganci daga Chadi.
Surayya Dee marubuciyar Littafin Halinyau, sabo da kaza da kuma bakar Ta'ada, ashe Adda Rukayya tana karanta littafanta ta nan suka saba yanzu kuma suna cinikayar kayan gyara da ita.
Ta kirata a gabana ta fad'a mata na haihu kuma duk da aiki aka yi min ina so na yi gyara nan take tace zata had'amin komai da komai cikin Farashi mai Sauki zata sauko a mota zuwa Jibi
Nima ban yi kasa a gwiwaba na tura ma Adda Rukayya kudin na kuma karbi Lambarta Tunda nace mata Ramatu ma tana so zata siya.
+234 803 277 3332
Washegari Samaru Habiba ta rakani har Gidan da muka zauna na kai musu su Asim su maman Boy dai ana nan jiya i yau ba wani Cigaban Rayuwa.
Na jima a gidan suna ina suka sakani sai da muka yi la'asar muka fito.
A hanya na had'u da wata kanwar Salisu ta na ta kallona ganin haka yasa na gaisheta.
Ta amsa ganina da goyo tare da Habiba yasa tace ko na haihu ne? Habiba ce ta ce mata Eh,Har kuma yaran na Bude mata ta gani ta yi musu addu'a har muka kule tana waigen mu.
A ranar naje Dirimi gidan Baba Tanko da Baba Saminu, na gaishe su tare da kai musu su Asim.
Baba Tanko har Daukansu ya yi sannan ya kalleni yana fadin"kwanaki naji an ce dangin mijin naki sun miki koran kare?
Ban yi mamakin jin ya samu Labari ba, na san kuma daga bakin Baba Jibril yaji kila shima Salima ta fitar da mganar waje.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.